Ya Mai Karatu:

Kana jin ka kusaci Allah? Ga mutane da yawa, hakan ba zai taba yiwuwa ba. Wasu suna jin yana da nisa kwarai; wasu kuma suna jin ba su cancanta ba. Amma cikin kauna, Littafi Mai Tsarki ya aririce mu: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku.” (Yakub 4:8) Har ma ya ba da tabbaci ga masu bauta masa: “Ni Ubangiji Allahnka zan rike hannun damanka, in ce maka, Kada ka ji tsoro, ni taimake ka.”—Ishaya 41:13.

Ta yaya za mu yi kokari mu samu irin wannan dangantaka ta kusa da Allah? A kowacce dangantaka da muka kulla, madaurin ya dangana ne bisa yadda muka san mutumin, yadda muke sha’awar halayensa wadanda farda ne kuma muke daukansu da tamani. Halayen Allah da kuma hanyoyinsa, da aka bayyana su cikin Littafi Mai Tsarki, batutuwa ne da za a yi nazarinsu. Bimbini bisa hanyar da Jehovah yake nuna kowanne cikin halayensa, ganin yadda Yesu Kristi ya nuna su, da kuma fahimtar yadda mu ma za mu iya koyonsu za su sa mu kusaci Allah. Za mu ga cewa Jehovah shi ne Mamallaki da ya dace na dukan sararin samaniya. Bugu da kari, shi ne Uba da dukanmu muke bukata. Mai iko, mai shari’a, mai hikima, mai kauna, bai taba yasar da ’ya’yansa masu aminci ba.

Bari wannan littafi ya taimake ka ka kusaci Jehovah Allah, ka kafa dangantaka da shi da ba za ta taba lalacewa ba don ka rayu ka yaba masa har abada.

Masu Bugawa