A duniya ta yau rashin adalci ya yi yawa, kuma ana yawan ɗora wa Allah laifi yadda bai dace ba. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya koyar da gaskiya mai taɓa zuciya cewa “Ubangiji yana son shari’a.” (Zabura 37:28) A wannan sashen za mu koyi yadda ya tabbatar da gaskiyar waɗannan kalmomi, ya ba da bege ga ’yan Adam.