Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Ka Kusaci Jehovah

 BABI NA 20

“Da Hikima a Zuciya”—Amma Kuma Mai Tawali’u

“Da Hikima a Zuciya”—Amma Kuma Mai Tawali’u

1-3. Me ya sa za mu tabbata cewa Jehovah yana da tawali’u?

UBA YANA so ya koya wa dansa darasi mai muhimmanci. Yana dokin ya taba zuciyarsa. Yaya zai dumfari yanayin? Zai tsaya ne abin tsoro a kan yaron ya yi masa bakar magana? Ko kuma zai sunkuya ne zuwa tsayin yaron ya yi masa magana a hankali, a hanya mai kyau? Hakika uba mai hikima zai zabi hanyar nan na saukin kai.

2 Wane irin Uba ne Jehovah—mai fahariya ne ko mai tawali’u, mai tsanantawa ne ko kuma marar tsanantawa? Jehovah shi ne masanin kome, shi kadai ne mai dukan hikima. Amma ka lura cewa, sani da fahimi ba sa mai da mutane masu tawali’u? Yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, “ilimi kuwa ya kan sa kumbura.” (1 Korinthiyawa 3:19; 8:1) Amma Jehovah, wanda yake da “hikima a zuciya,” mai tawali’u ne. (Ayuba 9:4) Ka lura cewa wannan ba ya nufin cewa yana da karamin matsayi ko kuma ba shi da iko, amma fahariya ce ba shi da ita. Me ya kawo hakan?

3 Jehovah mai tsarki ne. Saboda haka fahariya, hali da yake kazantarwa, babu a gare shi. (Markus 7:20-22) Bugu da kari, ka lura da abin da annabi Irmiya ya ce wa Jehovah: “Babu shakka [Jehovah kansa] za ka tuna ka sunkuya a kaina.” * (Makoki 3:20; NW ) Ka ji wannan! Jehovah, Ubangiji Mamallakin Dukan halitta, yana shirye ya “sunkuya,”  ko kuma ya sauko zuwa matsayin Irmiya, domin ya mai da hankalinsa ga wannan mutumi ajizi. (Zabura 113:7) Hakika, Jehovah mai tawali’u ne. Amma menene tawali’u na ibada yake kunsa? Ta yaya yake da nasaba da hikima? Kuma me ya sa yake da muhimmanci a gare mu?

Yadda Jehovah Ya Kasance da Tawali’u

4, 5. (a) Menene tawali’u, kuma ta yaya yake bayyana, kuma me ya sa bai kamata a rikita shi da kumamanci ko rashin kwazo ba? (b) Ta yaya Jehovah ya nuna tawali’u a sha’aninsa da Dauda, kuma yaya muhimmanci tawali’un Jehovah yake a gare mu?

4 Tawali’u kaskantar zuciya ne, rashin taurin kai da fahariya. Hali ne na cikin zuciya, tawali’u yana bayyana a cikin halaye kamar su rashin tsanantawa, hakuri, da kuma sanin-ya-kamata. (Galatiyawa 5:22, 23) Amma, kada a dauki wannan hali na Allah rashin karfi ne ko kuma rashin gaba gadi. Suna jituwa da fushi na adalci na Jehovah ko kuma yin amfani da ikonsa na halakarwa. Akasarin haka, ta wajen tawali’unsa da kuma rashin tsanantawa, Jehovah yana nuna  karfinsa mai yawa, ikonsa ya kame kansa sarai. (Ishaya 42:14) Ta yaya tawali’u yake da nasaba da hikima? Wani littafin bidan bayani game da Littafi Mai Tsarki ya lura cewa: “A karshe an ba da ma’anar tawali’u . . . a kan sadaukar da kai kuma cibiya ce mai muhimmanci na dukan hikima.” Saboda haka, hikima ta gaske ba za ta kasance ba ba tare da tawali’u ba. Ta yaya tawali’un Jehovah yake mana amfani?

Uba mai hikima yana bi da ’ya’yansa cikin tawali’u da kuma rashin tsanantawa

5 Sarki Dauda ya rera wa Jehovah waka: ‘Kā ba ni garkuwar cetonka kuma: hannun damanka ya rike ni, [tawali’un]ka ya daukaka ni.’ (Zabura 18:35) Watau, Jehovah yana sunkuyawa ne domin ya yi sha’ani da wannan mutum ajizi, yana kiyaye shi kuma ya raya shi rana rana. Dauda ya fahimci cewa idan zai samu ceto—kuma idan a karshe zai samu daukaka a zaman sarki—zai kasance ne domin son rai na Jehovah ya sunkuya a wannan hanyar. Hakika, waye a tsakaninmu zai samu begen ceto idan da Jehovah ba mai tawali’u ba ne, wanda yake a shirye ya sunkuya domin ya yi sha’ani da mu na Uba marar tsanantawa mai kauna?

6, 7. (a) Me ya sa Littafi Mai Tsarki bai taba cewa Jehovah yana da filako ba? (b) Mecece nasabar da take tsakanin rashin tsanantawa da hikima, kuma wa ya kafa misali mafi girma na wannan?

6 Yana da kyau a lura cewa da akwai bambanci tsakanin tawali’u da filako. Filako hali ne mai kyau da mutane masu aminci za su nema. A ce tawali’u, yana da nasaba da hikima. Alal misali, Misalai 11:2, (NW ), ta ce: “Hikima tana ga masu filako.” Amma, Littafi Mai Tsarki bai taba yin maganar Jehovah cewa yana da filako ba. Me ya sa? Filako, kamar yadda aka yi amfani da shi a cikin Littafi Mai Tsarki, yana nufin mutum ya sani daidai kasawarsa. Madaukaki Duka ba shi da iyaka sai dai wadanda ya kafa wa kansa domin mizanansa na adalci. (Markus 10:27; Titus 1:2) Bugu da kari, tun da shi ne Mafi Girma, ba ya karkashin kowa. Saboda haka, halin filako bai shafi Jehovah ba.

7 Duk da haka, Jehovah mai tawali’u ne kuma marar  tsanantawa. Ya koyar da bayinsa cewa rashin tsanantawa dole ne ga hikima ta gaskiya. Kalmarsa ta yi maganar “tawali’u na hikima.” * (Yakub 3:13) Ka yi la’akari da misalin Irmiya game da wannan.

Jehovah Yana Ba da Aiki Kuma Yana Sauraro Cikin Tawali’u

8-10. (a) Me ya sa abin mamaki ne cewa Jehovah ya nuna son rai wajen ba da aiki da kuma sauraro? (b) Ta yaya Madaukaki ya bi da mala’ikunsa da tawali’u?

8 Da akwai tabbacin tawali’un Jehovah a yadda yake ba da aiki ga wasu da son rai kuma ya saurara. Ganin yana haka ma abin mamaki ne; Jehovah ba ya bukatar taimako ko kuma shawara. (Ishaya 40:13, 14; Romawa 11:34, 35) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki a kai a kai ya nuna mana cewa Jehovah yana saukowa a hanyoyin nan.

9 Alal misali, ka yi la’akari da abu mai muhimmanci a rayuwar Ibrahim. Ibrahim ya yi baki guda uku ya kira daya cikinsu “Jehovah.” Bakin ainihi mala’iku ne, amma daya cikinsu ya zo cikin sunan Jehovah kuma yana aiki bisa Sunan. Sa’ad da mala’ikan ya yi magana kuma ya yi aiki, hakika, Jehovah ne yake magana kuma yake yin aiki. Ta wannan hanyar, Jehovah ya gaya wa Ibrahim cewa ya ji “karar Saduma da Gwamrata tana da girma.” Jehovah ya ce: “Ni sauka yanzu, in gani ko aikinsu ya kai gwargwadon karassa, wadda ta zo gareni; idan ba haka ba, na gane.” (Farawa 18:3, 20, 21) Hakika, sakon Jehovah ba ya nufin cewa shi Madaukaki Duka zai “sauka” da kansa. Maimakon haka, ya aiko mala’iku su wakilce shi. (Farawa 19:1) Me ya sa? Jehovah mai gani duka ba zai iya “gane” gaskiyar yanayin wannan yankin ba da kansa? Hakika. Amma maimakon haka, Jehovah cikin tawali’u ya bai wa mala’iku aikin bincika  wannan yanayi kuma su ziyarci Lutu da iyalinsa a Saduma.

10 Bugu da kari, Jehovah yana sauraro. Ya taba tambayar mala’ikunsa su ba da shawara game da hanyoyi da za a wulakanta mugun Sarki Ahab. Jehovah ba ya bukatar irin wannan taimakon. Duk da haka, ya yarda da shawarar wani mala’ika kuma ya umurce shi ya yi yadda ya ce. (1 Sarakuna 22:19-22) Wannan ba tawali’u ba ne?

11, 12. Ta yaya Ibrahim ya zo ga fahimtar tawali’un Jehovah?

11 Jehovah yana sauraron mutane ajizai wadanda suke so su nuna damuwarsu. Alal misali, sa’ad da Jehovah ya gaya wa Ibrahim nufinsa da farko cewa zai halaka Saduma da Gwamarata, wannan mutum mai aminci ya yi mamaki. “Ya yi nisa da kai ka yi irin wannan,” in ji Ibrahim, ya dada cewa: “Mai-shari’an dukan duniya ba za ya yi daidai ba?” Ya yi tambaya ko Jehovah zai kyale birnin idan da mutane masu adalci guda 150 a cikinsa. Jehovah ya tabbatar masa cewa Zai kyale shi. Amma Ibrahim ya sake tambaya, ya rage adadin zuwa 45, zuwa 40, da sauransu. Duk da tabbaci da Jehovah ya bayar, Ibrahim ya ci gaba har sai da ya rage adadin zuwa goma. Watakila Ibrahim bai fahimci sosai ba yadda Jehovah yake da jinkai. Ko da me ya sa, Jehovah ya yi hakuri da kuma tawali’u ya kyale abokinsa kuma bawansa Ibrahim ya furta damuwarsa a wannan hanyar.—Farawa 18:23-33.

12 Mutane masu fahimi guda nawa ne za su iya kasancewa da hakuri su saurari mutum wanda ba shi da fahimi kamarsu? * Irin wannan ne tawali’un Allahnmu. A lokacin wannan mahawara, Ibrahim ya ga cewa Jehovah yana da “jinkirin fushi.” (Fitowa 34:6) Watakila fahimtar cewa ba shi da ikon bincika abin da Madaukaki yake yi, Ibrahim sau biyu  ya yi roko: “Kada Ubangiji ya yi fushi.” (Farawa 18:30, 32) Hakika, Jehovah bai yi fushi ba. Da gaske yana da “tawali’u da ke na hikima.”

Jehovah Yana da La’akari

13. Menene ma’anar kalmar nan ‘la’akari’ kamar yadda aka yi amfani da ita a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma me ya sa wannan kalmar ta kwatanta Jehovah daidai?

13 Tawali’un Jehovah ya bayyana har ila cikin wani kyakkyawan hali—la’akari. Abin bakin ciki wannan halin babu shi a tsakanin mutane ajizai. Ba kawai Jehovah yana so ya saurari halittunsa masu basira ba amma kuma yana shirye ya yarda sa’ad da babu sabani da mizanai na adalci. Kamar yadda aka yi amfani da ita a Littafi Mai Tsarki, kalmar nan ‘la’akari’ a zahiri tana nufin “yarda.” Wannan hali ma alama ce ta hikimar Allah. Yakub 3:17 ta ce: “Hikima mai-fitowa daga bisa . . . mai-saukin hali” ce. A wace hanya ce Jehovah mai dukan hikima yake da la’akari? Abu daya shi ne, yana daidaita a kowane yanayi. Ka tuna cewa, sunansa ya koyar da mu cewa Jehovah yana sa kansa ya kasance dukan abin da ake bukata domin ya cika nufinsa. (Fitowa 3:14) Wannan bai nuna halin daidaitawa ba da kuma na la’akari?

14, 15. Wahayin Ezekiel na keken Jehovah ya koyar da mu menene game da kungiyar Jehovah ta samaniya, kuma ta yaya ta bambanta da kungiyoyin duniya?

14 Da akwai labari na Littafi Mai Tsarki da ya taimake mu muka fara fahimtar daidaita na Jehovah a kowane yanayi. An nuna wa annabi Ezekiel wahayin kungiyar Jehovah ta samaniya ta halittun ruhu. Ya ga keke mai girmar bala’i, “motar” Jehovah da take karkashin ikonsa kullum. Abin ban mamaki ma yadda take tafiya ne. Manyan kafafu hudu masu kama da zobe sun cika da idanu saboda haka suna iya ganin ko’ina kuma za su iya canja hanya a take, ba tare da sun tsaya ba ko kuma sun juya. Kuma wannan babban keken ba ya bukatar ya yi tafiya da nauyi kamar mota  mai nauyi da mutum ya kera. Yana iya tafiya kamar walkiya, kuma ya juya! (Ezekiel 1:1, 14-28) Hakika, kungiyar Jehovah, kamar madaukaki Mamallaki da ke rike da ita, tana daidaita a kowane yanayi kwarai, tana mai da hankali ga yanayi da yake canjawa da kuma bukatu.

15 Mutane sai dai su yi kokari su yi koyi da irin wannan kamiltacciyar daidaita. Ko da yake, sau da yawa mutane da kuma kungiyoyi sun fiye rashin daidaita a yanayi maimakon su daidaita, sun fiye rashin la’akari da yin la’akari. Alal misali: Babban jirgin ruwa ko kuma jirgin kasa za su iya kasancewa kyawawa wajen girma kuma da karfi. Amma za su iya canjawa kuwa idan yanayi ya canja farat daya? Idan wani abu ya fadi a kan hanyar jirgin kasa, ba a maganar juyawa. Juyawa a take ba ta yiwuwa da sauki. Babban jirgin kasa zai yi tafiyar mil guda kafin ya tsaya bayan an taka birki! Hakanan, babban jirgin ruwa zai yi tafiyar mil biyar bayan an kashe inji. Ko ma idan aka saka injin a ribas, jirgin zai ci gaba da tafiya ta mil biyu tukuna! Haka yake da kungiyoyi na mutane da ba sa iya canjawa kuma ba sa la’akari. Domin fahariya, mutane sau da yawa suna kin daidaitawa da canjin bukatu da kuma yanayi. Irin wannan ya kashe masana’anta har ma ya kifar da gwamnatoci. (Misalai 16:18) Muna farin ciki cewa Jehovah da kungiyarsa ba haka suke ba!

Yadda Jehovah Ya Nuna Yin La’akari

16. Ta yaya Jehovah ya nuna la’akari a yadda ya yi sha’ani da Lutu kafin a halaka Saduma da Gwamarata?

16 Ka sake yin la’akari da halakar Saduma da Gwamarata. Mala’ikun Jehovah sun ba Lutu da iyalinsa umurni: “Ka tsira zuwa dutse.” Amma, Lutu bai so wannan ba. Ya yi roko, “Ba haka ba, ya ubangijina.” Domin ya tabbata cewa zai mutu idan zai gudu zuwa duwatsu, Lutu ya yi roko cewa shi da iyalinsa a kyale su su gudu zuwa birni da yake kusa mai suna Zoar. Ka tuna Jehovah ya nufa ya halaka wannan birni. Bugu da kari, Lutu ba shi da dalilin gaske na tsorata. Hakika  Jehovah zai iya kiyaye ran Lutu a kan duwatsun! Duk da haka, Jehovah ya yarda da rokon Lutu ya kyale Zoar. “Ga shi, na amsa maka a kan wannan abu kuma,” in ji mala’ikan ga Lutu. (Farawa 19:17-22) Wannan ba yin la’akari ba ne daga Jehovah?

17, 18. Wajen sha’ani da mutanen Nineveh, ta yaya Jehovah ya nuna cewa yana da la’akari?

17 Jehovah yana amsa tuba ta gaske, kullum yana yin abin da ke jinkai da kuma daidai. Ka lura da abin da ya faru sa’ad da aka aiki annabi Yunana zuwa mugun birni na Nineveh. Sa’ad da Yunana ya bi cikin birnin Nineveh, huraren sako da ya sanar mai sauki ne: A cikin kwanaki 40 za a halaka babban birnin. Amma, yanayi ya canja kwarai. Mutanen Nineveh suka tuba!—Yunana, sura 3.

18 Gwada yadda Jehovah ya ji da yadda Yunana ya ji game da wannan canji zai koyar da mu. A wannan yanayin Jehovah ya daidaita, ya sa kansa ya kasance mai gafarta zunubi maimakon ya zama “mayaki.” * (Fitowa 15:3) Yunana kuma, ba shi da daidaita kuma ba shi da jinkai. Maimakon ya nuna la’akari irin na Jehovah, ya aikata kamar jirgin kasa ko kuma babban jirgin ruwa da aka ambata da farko. Ya riga ya sanar da halaka, saboda haka dole halaka ta kasance! Amma cikin hakuri Jehovah ya koyar da annabinsa marar hakuri darasi da ba zai manta ba na yin la’akari da kuma jinkai.—Yunana, sura 4.

Jehovah yana da la’akari kuma ya fahimci kasawarmu

19. (a) Me ya sa za mu tabbata cewa Jehovah yana la’akari da abin da yake bukata a gare mu? (b) Ta yaya Misalai 19:17 ta nuna cewa Jehovah Shugaba ne na “kirki kuma mai la’akari” kuma da tawali’u mai girma?

19 Na karshe, Jehovah yana la’akari wajen abin da yake bukata a gare mu. Sarki Dauda ya ce: “Ya san tabi’armu; ya kan tuna mu turbaya ne.” (Zabura 103:14) Jehovah yana fahimtar  kasawarmu da kuma ajizancinmu fiye da mu kanmu. Ba ya neman abin da ba za mu iya yi ba a gare mu. Littafi Mai Tsarki ya bambanta wadannan shugabannai mutane “masu-nasiha” da wadanda suke “masu-sherare.” (1 Bitrus 2:18) Jehovah wane irin Shugaba ne? Ka lura da abin da Misalai 19:17 ta ce: “Mai-jin tausayin fakirai yana bada rance ga Ubangiji.” Hakika, sai dai shugaba na kirki ne zai lura da dukan kirki da aka yi wa fakirai. Fiye ma da haka, nassosi sun nuna cewa Mahaliccin dukan halitta, watau, yana ganin mutane da suka yi ayyukan jinkai suna bin sa bashi! A nan ga tawali’u mai girma kwarai.

20. Wane tabbaci ne da akwai cewa Jehovah yana sauraron addu’o’inmu kuma yana amsa su?

20 Jehovah hakanan yana da la’akari kuma ba ya tsanantawa ga bayinsa a yau. Sa’ad da muka yi addu’a cikin bangaskiya yana sauraronmu. Kuma da yake ba ya aika da mala’iku su yi magana da mu, kada mu ce ba ya amsa addu’o’inmu. Ka tuna cewa sa’ad da manzo Bulus ya ce ’yan’uwa mabiya su “yi addu’a” domin a sake shi daga fursuna, ya dada cewa: “Domin a maishe ni gareku da sauri.” (Ibraniyawa 13:18, 19) Saboda haka, watakila addu’o’inmu za su motsa Jehovah ya yi abin da kila ba zai yi ba!—Yakub 5:16.

21. Wace kammala ce kada mu taba yi game da tawali’un Jehovah, maimakon haka, menene ya kamata mu fahimta game da shi?

 21 Hakika, babu daya cikin wadannan nunin tawali’un Jehovah—rashin tsanantawarsa, sauraronsa da son rai, hakurinsa, da kuma yin la’akarinsa—da yake nufin Jehovah yana barin mizanansa na adalci. Limaman Kiristendam watakila suna yin tunanin cewa suna yin la’akari ne sa’ad da suke sosa kunnuwan tumakinsu ta wajen rage muhimmancin mizanan dabi’a na Jehovah. (2 Timothawus 4:3) Halin mutane na son rage muhimmancin dabi’a saboda wata dabara, ba abin da ya hada shi da yin la’akari na Allah. Jehovah yana da tsarki; ba zai taba kazantar da mizanansa masu adalci ba. (Leviticus 11:44) Saboda haka, bari mu kaunace yin la’akari na Jehovah domin yadda yake—tabbacin tawali’unsa. Ba ka farin ciki ka yi tunanin Jehovah Allah, mafi hikima a dukan sararin samaniya, cewa ya bambanta wajen tawali’u? Abin farin ciki ne mu kusaci wannan Allah mai ban tsoro har ila kuma marar tsanantawa, mai hakuri, mai la’akari!

^ sakin layi na 3 Marubuta na dā, ko kuma Soferim, sun canja wannan ayar ta ce Irmiya ne ba Jehovah ne ya sunkuya ba. Babu shakka suna tunanin cewa bai dace ba a ce Allah ya yi irin wannan tawali’u. Domin wannan, yawancin fassara ba su fahimci batun wannan kyakkyawar aya ba. Amma dai, The New English Bible ya fassara shi daidai Irmiya yana cewa Allah: “Ka tuna, ka tuna, ka sunkuya zuwa gare ni.”

^ sakin layi na 7 Wasu fassara suka ce “tawali’u da yake zuwa daga hikima” ne da kuma “saukin kai da alamar hikima ce.”

^ sakin layi na 12 Littafi Mai Tsarki ya bambanta hakuri da fahariya. (Mai-Wa’azi 7:8) Hakurin Jehovah ya ba da karin tabbacin tawali’unsa.—2 Bitrus 3:9.

^ sakin layi na 18 A Zabura 86:5, an ce Jehovah yana da “hanzarin gafartawa.” Sa’ad da aka fassara wannan zaburar zuwa Helenanci, furcin nan “mai-hanzarin gafartawa” aka fassara shi e·pi·ei·kesʹ, ko kuma “mai la’akari.”