Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Ka Kusaci Jehovah

Allah yana gayyatar ka ka kusace shi. Wannan littafin zai nuna maka yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka ka yi hakan.

Gabatarwa

Za ka iya kulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah Allah har abada.

BABI NA 1

“Ga Shi, Wannan Allahnmu Ne”

Tun da Musa ya riga ya san sunan Allah, me ya sa ya tambayi sunan?

BABI NA 2

Za Ka Iya ‘Kusantar Allah’ da Gaske Kuwa?

Jehobah Allah, Mahalaccin sama da kasa, yana gayyatarmu kuma yana ba mu tabbaci.

BABI NA 3

“Mai-Tsarki, Mai-Tsarki, Mai-Tsarki ne, Ubangiji”

Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya kamanta tsarki da kyau?

BABI NA 4

“Ubangiji . . . Mai-Girma ne Cikin Iko”

Ya kamata mu ji tsoron Allah saboda ikonsa ne? Amsar E ne da a’a.

BABI NA 5

Ikon Halitta—‘Mahaliccin Sama da Kasa’

Yin la’akari da dukan halittu, daga rana mai matukar girma, har zuwa karamar tsunstu, wato hummingbird, za mu koyi abubuwa masu muhimmanci game da Allah.

BABI NA 6

Ikon Halaka—Jehovah, “Mayaki Ne”

Me ya sa “Allah na salama” yake yaki?

BABI NA 7

Ikon Kāriya—“Allah Mafaka ne a Gare Mu”

Allah yana kāre bayinsa a hanyoyi biyu, amma hanya daya ta fi muhimmanci.

BABI NA 8

Ikon Maidowa—Jehovah Yana “Sabonta Dukan Abu”

Jehobah ya riga ya maido da bauta ta gaskiya. Mene ne zai maido a nan gaba?

BABI NA 9

“Kristi Ikon Allah”

Mene ne mu’ujizan Yesu Kristi da kuma koyarwarsa suke nuna mana game da Jehobah?

BABI NA 10

“Ku Zama fa Masu-Koyi da Allah” Wajen Amfani da Iko

Walkila kana da ikon fiye da yadda kake tsammani—ta yaya za ka yi amfani da shi a hanyar da ta dace?

BABI NA 11

“Dukan Tafarkunsa Shari’a Ne”

Ta yaya adalcin Allah yake sa mu kusace shi?

BABI NA 12

“Da Rashin Adalci ne Tare da Allah?”

Idan Jehobah ya tsani rashin adalci, me ya sa ake rashin adalci a ko’ina a duniya?

BABI NA 13

‘Dokar Jehovah Cikakkiya Ce’

Ta yaya tsarin doka yake daukaka kauna?

BABI NA 14

Jehovah Ya Yi Tanadin “Fansar Mutane Dayawa”

Koyarwa mai sauki amma mai ma’ana zai taimaka maka ka kusaci Allah.

BABI NA 15

Yesu “Ya Kafa Shari’a ta Gaskiya Cikin Duniya”

Ta yaya Yesu ya daukaka shari’a ta gaskiya a dā? Yaya yake yin hakan a yanzu? Ta yaya zai kafa shari’a ta gaskiya a nan gaba?

BABI NA 16

Yi “Aikin Gaskiya” Wajen Tafiya da Allah

Me ya sa Yesu ya ba da gargadi: “Kada ku zartar, domin kada a zartar muku”?

BABI NA 17

“Ya Zurfin . . . Hikimar Allah!”

Me ya sa hikimar Allah ta fi saninsa da fahimi da basira?

BABI NA 18

Hikima Cikin “Maganar Allah”

Me ya sa Allah ya yi amfani da ’yan Adam don ya rubuta Littafi Mai Tsarki maimakon ya yi amfani da mala’iku ko kuma ya rubuta da kansa?

BABI NA 19

“Hikima ta Allah Cikin Asiri

Wane asiri ne Allah ya boye a dā amma ya bayyana yanzu?

BABI NA 20

“Da Hikima a Zuciya”—Amma Kuma Mai Tawali’u

Ta yaya Sarki Madaukaki ya zama mai tawali’u?

BABI NA 21

Yesu Ya Bayyana ‘Hikima Daga Allah’

Ta yaya koyarwar Yesu ya sa sojoji da aka tura su kama Yesu su koma hannu wofi?

BABI NA 22

Hikima Mai-Fitowa Daga Bisa” Tana Aiki Kuwa a Rayuwarka?

Littafi Mai Tsarki ya kwatanta abubuwa hudu da za su taimaka maka ka sami hikima ta allah.

BABI NA 23

“Ya Fara Kaunace Mu”

Mene ne furunin nan “Allah kauna ne” yake nufi?

BABI NA 24

Babu Abin da Zai Iya “Raba Mu da Ƙaunar Allah”

Kada ku yarda cewa Allah ba ya kaunarku.

BABI NA 25

“Jinƙai Mai-Taushi na Allahnmu”

Ta yaya irin jinkai ta Allah yake nuna maka yana kama da irin jinkai da uwa take nuna wa jaririnta?

BABI NA 26

Allah Wanda Yake da “Hanzarin Gafartawa”

Idan Allah yana tunawa da kome, ta yaya zai iya gafartawa kuma ya mance?

BABI NA 27

‘Ina Misalin Girman Nagartarsa!’

Mene ne ainihi nagartar Allah?

BABI NA 28

‘Kai Kaɗai ne Mai Aminci’

Me ya sa amincin Allah ya yana da girma?

BABI NA 29

“Ku Sani Kuma Ƙaunar Kristi”

Hanyoyi uku da Yesu ya nuna kauna sun nuna irin kaunar da Jehovah yake nunawa.

BABI NA 30

“Ku Yi Tafiya Cikin Kauna”

Korintiyawa ta fari ta nuna hanyoyi 14 da za mu iya nuna kauna.

BABI NA 31

‘Ka Kusaci Allah, Shi ma Zai Kusace Ka’

Wace tambaya mai muhimmanci ne za ka iya yi wa kanka? Yaya za ka amsa?