Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Ka Koya Daga Wurin Babban Malami

 BABI NA 32

Yadda Aka Kāre Yesu

Yadda Aka Kāre Yesu

JEHOVAH wani lokaci yana yin abubuwa a hanya mai ban mamaki domin ya kāre waɗanda suke ƙanana da kuma waɗanda ba za su iya kāre kansu ba. Idan ka fita yawo cikin gari, za ka ga yadda Jehovah yake yin haka. Amma da farko ba za ka gane abin da yake faruwa ba.

Ka ga tsuntsuwa ta sauka ƙasa kusa da kai. Kamar ta ji ciwo. Tana jan fukafukinta ta gudu idan ka yi kusa da ita. Sa’ad da ka bi tsuntsuwar, za ta yi gaba ba za ka iya kama ta ba. Sai farat ɗaya ta tashi sama ta yi tafiyarta. Babu ciwon da ya sami fukafukinta! Ka san abin da tsuntsuwar take yi?—

Inda tsuntsuwar ta sauka kusa da kai, ’ya’yanta suna ɓoye a cikin daji. Mamar tana tsoro za ka gansu ka kama su. Saboda haka, ta yi kamar ta ji ciwo domin ta janye ka daga wurin. Ka san wanda zai iya kāre mu kamar yadda mamar tsuntsuwa take kāre ’ya’yanta?— A cikin Littafi Mai Tsarki an kwatanta Jehovah da wata tsuntsuwa da ake kira gaggafa, wadda take taimakon ’ya’yanta ƙanana.—Kubawar Shari’a 32:11, 12.

Ta yaya wannan tsuntsuwa take kāre ’ya’yanta?

 Ɗa wanda Jehovah ya fi ƙaunarsa shi ne Yesu. Sa’ad da Yesu yake sama, shi ruhu ne mai iko kamar Ubansa. Yana kula da kansa. Amma sa’ad da aka haifi Yesu jariri a duniya ba shi da ta kansa. Yana bukatar kāriya.

Domin a cika nufin Allah game da shi, Yesu dole ne ya yi girma ya zama cikakken mutum kamili. Amma Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya kashe Yesu kafin hakan ya faru. Ƙoƙarin da aka yi a kashe Yesu sa’ad da yake yaro da kuma yadda Jehovah ya kāre shi labari ne mai daɗi. Kana so ka ji?—

Ba da daɗewa ba bayan an haifi Yesu, Shaiɗan ya saka wani abin da ya yi kama da tauraro ya bayyana a sama, ta Gabas. Mutane da ake kira masana taurari, waɗanda suka yi nazarin taurari, suka bi tauraron ɗarurruwan mil zuwa Urushalima. A nan suka yi tambaya a ina za a haifi wanda zai zama sarkin Yahudawa. Sa’ad da aka tambayi mutanen da suka san abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da wannan suka amsa: “A Baitalami.”—Matta 2:1-6.

Bayan masana taurari sun ziyarci Yesu, wane gargaɗi Allah ya yi musu da ya kāre Yesu?

 Bayan Hirudus mugun sarki a Urushalima ya ji game da wannan sabon sarkin da bai daɗe ba aka haife shi a gari na kusa da Baitalami, ya gaya wa masana taurarin: ‘Ku tafi, ku biɗi labarin ɗan yaron nan a hankali; sa’anda kun same shi kuma, ku kawo mini labari.’ Ka san abin da ya sa Hirudus yake so ya san inda zai sami Yesu?— Dalilin shi ne Hirudus yana kishi yana so ya kashe shi!

Ta yaya Allah ya kāre Ɗansa?— Sa’ad da masana taurarin suka sami Yesu, sun ba shi kyauta. Daga baya Allah ya yi wa masana taurarin gargaɗi a cikin mafarki kada su koma wurin Hirudus. Sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam ba tare da bi ta Urushalima ba. Sa’ad da Hirudus ya ji cewa masana taurarin sun tafi, ya yi fushi sosai. Domin ya kashe Yesu, Hirudus ya sa aka kashe dukan yara ’yan kasa da shekara biyu a Baitalami! Amma kafin nan, Yesu ba ya wajen.

Ka san yadda aka yi Yesu ya tsira?— Bayan da masana taurarin suka koma ƙasarsu, Jehovah ya ba da gargaɗi ga mijin Maryamu, Yusufu, ya gudu zuwa ƙasar Masar. A nan Yesu ya tsira daga hannun Hirudus mugun mutum. Bayan wasu shekaru sa’ad da Yesu da Maryamu suka dawo daga ƙasar Masar da Yesu, Allah ya sake yi wa Yusufu gargaɗi. Ya gaya masa cikin mafarki ya ƙaura zuwa Nazarat, inda Yesu zai samu kwanciyar hankali.—Matta 2:7-23.

Ta yaya aka sake kāre jariri Yesu?

Ka ga yadda Jehovah ya kāre Ɗansa?— Waye za ka ce ya yi kamar ƙananan tsuntsaye ne da mamarsu ta ɓoye su a cikin daji ko kuma kamar Yesu sa’ad da yake ƙarami? Ba kamarsu kake  ba?— Da akwai waɗanda suke so ka ji rauni. Ka san wanene ne?—

Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan kamar zaki ne mai gurnani wanda yake so ya cinye mu. Kamar yadda zaki sau da yawa yake kama ƙananan dabbobi, haka Shaiɗan da aljanunsa sau da yawa suke neman yara ƙanana. (1 Bitrus 5:8) Amma Jehovah ya fi Shaiɗan ƙarfi. Jehovah zai iya ya kāre yaransa, ko kuma ya gyara dukan muguntan da Shaiɗan ya yi musu.

Ka tuna daga Babi na 10 na wannan littafin abin da Iblis da aljanunsa suke ƙoƙarin su sa mu yi?— E, suna ƙoƙari su sa mu yi irin jima’i da Allah ya ce ba shi da kyau. Amma su waye ya kamata su yi jima’i?— Hakika, manyan mutane mata da miji waɗanda suka yi aure.

Abin baƙin ciki, wasu manyan mutane suna son su yi jima’i da yara. Sa’ad da suka yi haka, yara maza da mata sai su fara abin da ba shi da kyau da suka koya daga wurin waɗannan manyan mutane. Sai kuma su fara yin amfani da al’aurarsu a hanyar da ba ta dace ba. Abin da ya faru ke nan da daɗewa a birnin Saduma. Littafi Mai Tsarki ya ce mutanen wurin, “samari da tsofaffi,” suka yi ƙoƙari su yi jima’i da mutane da suka zo su ziyarci Lutu.—Tafiyar tsutsa tamu ce; Farawa 19:4, 5.

Kamar yadda Yesu ya bukaci kāriya, haka kai ma kana bukatar kāriya daga manya—har ma daga wasu yara—da za su yi ƙoƙarin su yi jima’i da kai. Waɗannan mutane za su nuna su abokananka ne. Wataƙila su ba ka wani abu idan za ka yi musu alkawari ba za ka gaya wa kowa ba game da abin da suke so su yi da kai. Amma waɗannan mutane masu son kai ne, kamar Shaiɗan da aljanunsa, suna so ne kawai su faranta ransu. Kuma suna so su sami wannan farin ciki ta wajen yin jima’i da yara. Wannan yana da muni ƙwarai!

 Ka san abin da za su yi domin su sami farin ciki?— Za su yi ƙoƙarin su shafa al’aurarka. Ko kuma su shafa tasu a kan taka. Amma kada ka ƙyale ko ki ƙyale kowa ya yi wasa da azzakari ko kuma farjinki. Ko ɗan’uwanka ko ’yar’uwarka ko ma mamarka da babanka ne. Wannan gaɓa na jikinka naka ne.

Me za ka ce ko kuma za ka yi idan mutum yana so ya taɓa ka a wurin da bai dace ba?

Ta yaya za ka kāre jikinka daga mutane da suke yin mugun abu irin wannan?— Da farko, kada ka ƙyale kowa ya yi wasa da al’aurarka. Idan wani yana ƙoƙarin ya yi haka, ka faɗa da ƙarfi: “Ba na so! Zan kai ƙararka fa!” Amma idan mutumin ya ce abin da ya faru laifinka ne, kada ka yarda. Ba gaskiya ba ne. Ka je ka kai ƙararsa ko wanene ne shi! Ya kamata ka yi ƙararsa ko ya ce abin da kuke yi asiri ne tsakaninku. Ko ma mutumin ya yi maka alkawarin zai ba ka abu mai kyau ko kuma yana razanarka, ka bar wurinsa ka je ka kai ƙararsa.

Kada ka ji tsoro, amma ka mai da hankali. Idan iyayenka suka yi maka gargaɗi game da mutane ko kuma wuraren da za su iya zama haɗari a gare ka, ya kamata ka saurare su. Idan ka yi haka, mugun mutum ba zai iya ji maka rauni ba.

Ka karanta game da kāre kanka daga jima’i da ba shi da kyau, a Farawa 39:7-12; Misalai 4:14-16; 14:15, 16; 1 Korinthiyawa 6:18; da kuma 2 Bitrus 2:14.