ABOKAI mutane ne da muke son mu riƙa taɗi da su kuma muna shaƙatawa. Amma yana da kyau mu sami abokai na kirki. Waye kake tsammani zai kasance abokin kirki da za mu samu?— Hakika, Jehovah Allah.

Amma da gaske za mu iya zama abokan Allah?— E, Littafi Mai Tsarki ya ce, Ibrahim, mutumin da ya rayu a lokacin dā, “abokin Allah” ne. (Yaƙub 2:23) Ka san abin da ya sa ya zama abokinsa?— Littafi Mai Tsarki ya amsa cewa Ibrahim ya yi wa Allah biyayya. Ya yi biyayya har a lokacin da abin da aka ce ya yi yana da wuya. Saboda haka, domin mu zama abokan Jehovah, dole ne mu yi abin da zai faranta masa rai, kamar yadda Ibrahim ya yi da kuma yadda Babban Malami yake yi kullum.—Farawa 22:1-14; Yohanna 8:28, 29; Ibraniyawa 11:8, 17-19.

Me ya sa Ibrahim ya zama “abokin Allah”?

 Yesu ya gaya wa manzanninsa: “Ku ne abokaina idan kun yi abin da na umurce ku.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Yohanna 15:14) Tun da dukan abin da Yesu ya gaya wa mutane ya fito ne daga wurin Jehovah, Yesu yana cewa abokansa mutane ne da suka yi abin da Allah ya ce su yi. Hakika, dukan abokansa sun ƙaunaci Allah.

Wasu abokai na kusa na Babban Malami manzanninsa ne, waɗanda ka ga hotunansu a shafi na 75 na wannan littafin. Sun yi tafiye-tafiye tare da shi kuma sun taimake shi wajen aikin wa’azi. Yawancin lokaci Yesu yana tare da waɗannan mutane. Sun ci abinci tare. Sun yi taɗi game da Allah tare. Kuma sun yi wasu abubuwa tare. Amma Yesu yana da wasu abokai da yawa. Yakan zauna tare da su, kuma suna shaƙatawa tare.

Wata iyali da Yesu yake son zama tare da su tana da zama a Bait’anya wani ƙaramin gari ne, a bayan babban birnin Urushalima. Ka tuna da su?— Su ne Maryamu da Martha da kuma Li’azaru ƙanen Martha. Yesu ya kira Li’azaru abokinsa. (Yohanna 11:1,  5, 11) Dalilin da ya sa Yesu ya ƙaunaci wannan iyali kuma yana son zama tare da su shi ne domin sun ƙaunaci Jehovah kuma suna bauta masa.

Me ya sa Yesu sau da yawa yake zama da wannan iyalin sa’ad da ya ziyarci Urushalima? Ka san sunayensu?

Wannan ba ya nufin cewa Yesu bai yi wa waɗanda ba sa bauta wa Allah kirki ba. Ya yi musu kirki. Har ma ya je gidajensu ya ci abinci tare da su. Wannan ya sa wasu suka ce da Yesu “masoyin masu-karɓan haraji da masu-zunubi!” (Matta 11:19) Yesu bai je gidajen waɗannan mutanen ba domin yana son yadda suke rayuwa. Ya ziyarce su ne domin ya yi taɗi da su game da Jehovah. Ya yi ƙoƙari ya sa su canja tafarkunsu da ba su da kyau kuma su bauta wa Allah.

Me ya sa Zakka ya hau wannan bishiyar?

Wannan ya faru wata rana a birnin Jericho. Yesu yana shigewa ta cikinsa sa’ad da yake kan hanyarsa zuwa Urushalima. Ga taron jama’a, kuma a tsakanin jama’ar da akwai wani mutum sunansa Zakka. Yana so ya ga Yesu. Amma Zakka gajeren mutum ne, kuma bai iya ganinsa ba domin yawan jama’a. Saboda haka, ya je gaba ya hau bishiya domin ya ga Yesu da kyau sa’ad da ya zo wucewa.

Sa’ad da Yesu ya isa wurin bishiyar, ya ɗaga ido ya ce: ‘Ka yi hanzari ka sauko, yau lallai a gidanka zan zauna.’ Amma Zakka mutum  ne mai arziki da ya yi abin da ba shi da kyau. Me ya sa Yesu yake so ya je gidan wannan mutumin?—

Ba domin Yesu yana son yadda mutumin yake rayuwa ba ne. Ya je gidan ne ya gaya wa Zakka game da Allah. Ya ga yadda mutumin ya yi ƙoƙari ƙwarai domin ya gan shi. Saboda haka, ya sani cewa wataƙila zai saurare shi. Wannan lokaci ne mai kyau na yi masa magana game da yadda Allah ya ce mutane su yi rayuwarsu.

Me ya sa Yesu yake ziyartar Zakka kuma menene Zakka yake yin alkawarin zai yi?

Me muke gani yake faruwa a nan?— Zakka yana son koyarwar Yesu. Yana baƙin ciki domin ya cuci mutane, kuma yana alkawari zai mai da kuɗin da ya ƙwace. Sa’an nan ya zama mabiyin Yesu. A wannan lokacin ne Yesu da Zakka suka zama abokai.—Luka 19:1-10.

Idan muka koya daga wurin Babban Malami, za mu ziyarci mutane da ba abokanmu ba?— E. Amma ba za mu je gidajensu ba domin muna son yadda suke rayuwa. Kuma ba za mu bi su yin abin da ba daidai ba. Za mu ziyarce su domin mu gaya musu game da Allah.

 Amma abokanmu na kusa su ne waɗanda muke son shaƙatawa da su. Domin su kasance abokan kirki dole su kasance irin waɗanda Allah yake so. Wasu ba su ma san wanene Jehovah ba. Amma idan suna so su koya game da shi, za mu iya taimakonsu. Kuma sa’ad da lokaci ya kai da suka ƙaunaci Jehovah kamar yadda muke yi, sa’an nan za mu iya zama abokai na kusa.

Da akwai wata hanya kuma na gano ko mutum zai kasance abokin kirki. Ka lura da abin da yake yi. Yana yin rashin kirki ne ga mutane kuma ya yi dariya? Hakan ba daidai ba ne, ko ba haka ba?— Yana yawan shiga masifa ne? Ba za mu so mu shiga masifa tare da shi ba, ko ba haka ba?— Ko kuma yana yin mugayen abubuwa da gangan kuma ya yi tunanin yana da wayo domin ba a kama shi ba? Ko ba a kama shi ba, Allah ya ga abin da ya yi, ko bai gani ba ne? Kana tsammanin mutane da suke irin waɗannan za su kasance abokan kirki?—

Ka ɗauki Littafi Mai Tsarki naka. Bari mu ga abin da ya ce game da yadda abokai suke shafar rayuwarmu. Nassin tana 1 Korinthiyawa sura 15, aya ta 33. Ka sami wurin?— Ta ce: “Kada ku yaudaru: zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.” Wannan yana nufi ne cewa idan muka yi tafiya da miyagun mutane, wataƙila mu ma za mu zama miyagu. Kuma gaskiya ne cewa abokan kirki suna taimakon mu mu yi halayen kirki.

Kada mu manta cewa wanda ya fi daraja a rayuwarmu shi ne Jehovah. Ba ma so mu ɓata abokantakarmu da shi, ko ba haka ba?— Domin haka, mu mai da hankali mu ƙulla abota da waɗanda suke ƙaunar Allah kawai.

An nuna muhimmancin abokan kirki a Zabura 119:115 (118:115, “Dy”); Misalai 13:20; 2 Timothawus 2:22 da kuma 1 Yohanna 2:15.