KA SAN addu’ar da Yesu ya koya wa mabiyansa?— Idan ba ka sani ba, za mu karanta tare daga Littafi Mai Tsarki, a Matta 6:9-13. Addu’ar da mutane da yawa suke kira Addu’ar Ubangiji, ta haɗa da kalmomin nan: “Mulkinka shi zo.” Ka san ko menene Mulkin Allah?—

Sarki mutum ne mai iko a kan wata ƙasa ko kuma yanki. Kuma wannan gwamnatin ana kiranta mulki. A wasu ƙasashe, mai iko a gwamnatin ana kiransa shugaban ƙasa. Menene ake kiran Mai Iko a gwamnatin Allah?— Sarkin. Abin da ya sa ke nan ake kiran gwamnatin Allah Mulki.

Ka san ko wanene Jehovah Allah ya zaɓa ya zama Sarki a gwamnatin?— Ɗansa ne, Yesu Kristi. Me ya sa ya fi kowanne mutum da  mutane suka zaɓa?— Domin Yesu yana ƙaunar Ubansa ne, Jehovah. Saboda haka, ko da yaushe yana yin abin da yake da kyau.

Da daɗewa kafin a haifi Yesu a Baitalami, Littafi Mai Tsarki ya faɗi game da haihuwarsa kuma ya ce zai zama Sarki da Allah ya zaɓa. Bari mu karanta wannan a Ishaya 9:6, 7. Ta ce: “Gama an haifa mana yaro, a garemu an bada ɗa: mulkin za ya kasance a kafaɗarsa: za a ce da sunansa . . . Sarkin Salama. Ƙaruwar mulkinsa da salama ba ta da iyaka.”—Tafiyar tsutsa tamu ce.

Ka san abin da ya sa aka kira Sarkin Mulkin Allah a nan ‘ɗan Sarki’?— Ɗan sarki yarima ne. Kuma Yesu ɗan Babban Sarki ne Jehovah. Amma Jehovah kuma ya naɗa Yesu Sarkin gwamnatinsa, wanda zai mallaki duniya na shekara dubu. (Ru’ya ta Yohanna 20:6) Bayan Yesu ya yi baftisma, ya fara “wa’azi, ya ce, Ku tuba; gama mulkin sama ya kusa.”—Matta 4:17.

Me kake tsammani ya sa Yesu ya ce Mulkin ya yi kusa?— Domin Sarkin, wanda daga baya zai yi sarauta a sama, yana tare da su ne! Abin da ya sa ke nan Yesu ya gaya wa mutane: “Mulkin Allah yana cikinku.” (Luka 17:21) Za ka so Sarki na Jehovah ya kasance kusa da kai da za ka iya taɓa shi?—

To, gaya mini, wane aiki ne mai muhimmanci Yesu ya yi a duniya?— Yesu ya amsa wannan tambayar, yana cewa: “Dole sai in yi Bishara ta mulkin Allah . . . gama saboda wannan aka aiko ni.” (Tafiyar tsatsa tamu ce; Luka 4:43.) Yesu ya sani cewa ba zai iya aikin wa’azin shi kaɗai ba. Domin haka, menene kake tsammani ya yi?—

Wane aiki ne Yesu ya zo duniya ya yi?

Yesu ya kwashi mutane ya nuna musu yadda za su yi aikin wa’azi. Mutane na farko da ya koyar  manzanninsa ne 12 da ya zaɓa. (Matta 10:5, 7) Yesu ya koyar da manzanni ne kawai su yi wannan aikin? A’a, Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya koyar da wasu da yawa su yi wa’azi. Daga baya ya tura wasu almajirai 70 su yi gaba, ya raba su bibbiyu. Me suke koya wa mutane?— Yesu ya ce: “Ku ce musu, Mulkin Allah ya zo kusa da ku.” (Luka 10:9) Ta wannan hanyar mutanen suka koyi game da gwamnatin Allah.

Dā dā a Isra’ila, sababbin sarakuna za su hau jaki su shigo gari su nuna kansu ga mutane. Abin da Yesu ya yi ke nan sa’ad da ya yi ziyararsa na ƙarshe a Urushalima. Ka gani, Yesu zai zama Sarki na Mulkin Allah. Mutanen suna so ya zama Sarki kuwa?—

Sa’ad da yake tafiya a kan hanya, yawancin mutane suna shimfiɗa tufafinsu a kan hanya a gabansa. Wasu sun sare rassan itace sun zuba a kan hanya. Ta wurin yin haka, sun nuna cewa suna so Yesu ya zama Sarkinsu. Suna kirari: “Mai-albarka ne Sarki mai-zuwa cikin sunan Ubangiji!” Amma ba dukan mutane ba ne suka yi farin ciki. Wasu ma cikin shugabannan addini suka ce wa Yesu, ‘Ka gaya wa almajiranka su yi shuru.’—Luka 19:28-40.

Me ya sa mutane suka canja ra’ayinsu game da son Yesu ya zama Sarki?

Bayan kwana biyar aka kama Yesu aka kai shi gaban gwamna, Bilatus Babunti. Abokan gaba na Yesu suka ce Yesu yana da’awar cewa shi sarki ne yana hamayya da gwamnatin Roma. Saboda haka, Bilatus ya tambayi Yesu game da wannan. Yesu ya nuna cewa shi ba juyin mulki yake so ya yi ba. Ya gaya wa Bilatus: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne.”—Yohanna 18:36.

Sai Bilatus ya fita ya gaya wa mutanen nan cewa shi bai sami wani laifi ba a wurin Yesu. Amma yanzu mutanen ba sa son Yesu ya zama Sarkinsu. Ba sa son a ƙyale shi. (Yohanna 18:37-40) Bayan ya sake magana da Yesu, Bilatus ya tabbata cewa bai yi laifi ba. A ƙarshe, bayan ya sake fitowa da Yesu waje, Bilatus ya ce: “Ga sarkinku!”  Amma mutanen suka ta da murya suka ce: ‘A tafi da shi, a tafi da shi, a rataye shi’!

Bilatus ya yi tambaya: ‘In rataye sarkinku? Manyan firistoci suka amsa: “Ba mu da wani sarki sai Kaisar.” Ji irin wannan abin! Waɗannan miyagun firistoci sun sa mutane su juya wa Yesu baya!—Yohanna 19:1-16.

A yau yanayin ya yi daidai da na lokacin Yesu. Mutane da yawa ba sa son Yesu ya zama Sarkinsu. Za su ce sun yi imani da Allah, amma ba sa son Allah ko kuma Kristi ya gaya musu abin da za su yi. Suna son gwamnatocinsu ne na nan duniya.

 To, mu kuma fa? Sa’ad da muka koyi game da Mulkin Allah da dukan abubuwa na ban sha’awa da zai yi, yaya muke ji game da Allah?— Muna ƙaunarsa ko ba haka ba?— To, yaya za mu nuna wa Allah cewa muna ƙaunarsa kuma muna son Mulkinsa ta mallake mu?—

Me ya sa Yesu ya yi baftisma, kuma yaya Allah ya nuna cewa ya amince da haka?

Za mu nuna wa Allah yadda muke ji ta wajen bin misalin Yesu. Menene Yesu ya yi ya nuna cewa yana ƙaunar Jehovah?— Yesu ya yi bayani cewa: “Kullum ina aika abin da ya gamshe shi.” (Yohanna 8:29) Hakika, Yesu ya zo duniya ya yi ‘nufin Allah’ kuma ya “cika aikinsa.” (Ibraniyawa 10:7; Yohanna 4:34) Ka yi la’akari da abin da Yesu ya yi kafin ya fara aikinsa na wa’azi.

Yesu ya je wajen Yohanna Mai Yin Baftisma a Kogin Urdun. Bayan da suka shiga cikin ruwa, Yohanna ya soma Yesu cikin ruwa sai kuma ya fito da shi. Ka san abin da ya sa Yohanna ya yi wa Yesu baftisma?—

A ina za mu iya yi wa wasu magana game da Mulkin Allah?

Yesu ya gaya wa Yohanna ya yi masa baftisma. Amma ta yaya muka sani cewa Allah yana so Yesu ya yi baftisma?— Mun san da haka domin sa’ad da Yesu ya fito daga cikin ruwa, ya ji muryar Allah daga sama ta ce: “Kai ne Ɗana ƙaunatacce, da kai raina ya ji daɗi sarai.”  Allah kuma ya aika da ruhu mai tsarki cikin siffar kurciya a kan Yesu. A ta wajen yin baftisma ne, Yesu ya nuna cewa yana so ya bauta wa Jehovah a dukan kwanan ransa, hakika, har abada.—Markus 1:9-11.

Har yanzu kai matashi ne. Menene za ka yi a nan gaba?— Za ka zama kamar Yesu ka yi baftisma?— Ya kamata ka yi koyi da shi, domin Littafi Mai Tsarki ya ce ya ‘bar maka gurbi, domin ka bi sawunsa.’ (1 Bitrus 2:21) Sa’ad da ka yi baftisma, za ka nuna cewa kana son Mulkin Allah ya yi sarautarka da gaske. Amma idan ka yi baftisma ba shi ke nan ba.

Muna bukatar mu yi biyayya ga dukan abin da Yesu ya koyar da mu. Yesu ya ce bai kamata mu kasance “na duniya ba.” Idan muka shagala cikin abubuwa na duniya muna yi masa biyayya ne? Yesu da manzanninsa sun guji irin waɗannan abubuwa. (Yohanna 17:14) Menene suka yi maimakon haka?— Sun gaya wa wasu game da Mulkin Allah. Wannan shi ne babban aiki a rayuwarsu. Za mu iya yin haka ne mu ma?— Hakika, za mu iya idan mun tabbata da abin da muka ce sa’ad da muke addu’a Mulkin Allah ya zo.

Ka ga waɗannan nassosi kuma da suka gaya mana abin da za mu yi mu nuna muna son Mulkin Allah ya zo: Matta 6:24-33; 24:14; 1 Yohanna 2:15-17; da kuma 5:3.