KA CI abinci yau?— Ka san wadda ta dafa shi?— Wataƙila mamarka ko kuma wata, amma me ya sa za ka gode wa Allah domin abincin?— Domin Allah shi ne ya sa abincin ya yi girma. Duk da haka, ya kamata mu gode wa wadda ta dafa abincin ko kuma wadda ta kawo mana abincin.

Wani lokaci muna manta mu ce mun gode sa’ad da wasu suka yi mana abin kirki, ko ba haka ba? Sa’ad da Babban Malami yake duniya, da akwai wasu kutare da suka manta su ce sun gode.

Ka san ko wanene ne kuturu?— Kuturu mutum ne wanda yake da cutar da ake kira kuturta. Wannan cutar za ta iya cinye wasu tsokar mutum. Sa’ad da Yesu yake duniya, kutare suna zama nesa da mutane masu lafiya. Kuma idan kuturu ya ga wani mutum yana zuwa, dole ne ya sanar da mutumin cewa ya gafara daga wurinsa. Ana yin wannan ne domin wasu mutane kada su zo kusa su ma su kamu da cutar kuturta.

Yesu ya yi wa kutare kirki. Wata rana, yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, Yesu ya bi ta cikin wani ƙaramin gari. Sa’ad da ya zo kusa da garin, kutare goma suka zo su gan shi. Sun ji cewa Yesu yana da iko daga wurin Allah da zai iya magance kowacce irin cuta.

Kutaren ba su zo kusa da Yesu ba. Sun tsaya can daga nesa. Amma sun gaskata cewa Yesu zai warkar da kuturtarsu. Saboda haka, da kutaren suka ga Babban Malami, suka ce masa: ‘Yesu, Malam, ka taimake mu!’

 Kana jin tausayin mutane da ba su da lafiya?— Yesu ya ji tausayinsu. Ya sani cewa abin baƙin ciki ne mutum ya zama kuturu. Saboda haka, ya amsa musu ya ce: “Ku tafi, ku gwada kanku ga malamai.”—Luka 17:11-14.

Menene Yesu yake gaya wa waɗannan kutare su yi?

Me ya sa Yesu ya gaya musu su yi haka? Domin doka ce da Jehovah ya ba wa mutanensa game da kutare. Wannan dokar ta ce firist na Allah zai dubi fatar kuturun. Firist ɗin zai gaya wa kuturun sa’ad da cutar ta ƙyale shi. Sa’ad da ya sami lafiya, zai zauna tare da mutane masu lafiya kuma.—Leviticus 13:16, 17.

Amma waɗannan kutaren har ila suna da cutarsu. Saboda haka, sun je wurin malamin ne kamar yadda Yesu ya gaya musu?— Hakika  sun je ba tare da ɓata lokaci ba. Waɗannan mutane sun gaskata cewa Yesu zai magance cutarsu. Menene ya faru?

Sa’ad da suke kan hanyarsu zuwa wurin firist, cutarsu ta warke. Suka sami lafiya! Gaskata ikon Yesu ya kawo musu albarka. Kai, sun yi murna sosai! Amma yanzu menene za su yi su nuna godiyarsu? Da menene za ka yi?—

Menene wannan kuturun ya tuna ya yi?

Mutum ɗaya cikin mutanen da aka warkar ya zo wurin Yesu. Ya fara daraja Jehovah, yana faɗin abubuwa masu kyau game da Allah. Wannan shi ne abin da ya dace ya yi domin ikon da ya warkar da shi ya zo ne daga wurin Allah. Mutumin kuma ya durƙusa a gaban Babban Malami ya yi masa godiya. Ya yi godiya kuma game da abin da Yesu ya yi.

To, sauran mutane tara ɗin fa? Yesu ya yi tambaya: ‘Kutare goma ne aka warkar, ko ba haka ba ne? Ina sauran tara ɗin? Mutum ɗaya ne kawai ya komo ya yabi Allah?’

E, gaskiya ne. Ɗaya ne kawai cikin goma ya yabi Allah kuma ya koma ya gode wa Yesu. Kuma wannan mutumin Basamariye ne, mutumin wata ƙasa dabam.  Sauran mutane taran ba su gode wa Allah ba, kuma ba su gode wa Yesu ba.—Luka 17:15-19.

Wanene cikin waɗannan mutane ya yi daidai da kai? Muna so mu zama kamar Basamariyen nan ko ba haka ba?— Saboda haka, idan wani ya yi mana abin kirki, me ya kamata mu tuna mu yi?— Ya kamata mu nuna godiyarmu. Sau da yawa mutane suna mantuwa su ce sun gode. Yana da kyau mu ce mun gode. Sa’ad da muka yi haka, Jehovah Allah da kuma Ɗansa, Yesu za su yi farin ciki.

Ta yaya za ka yi koyi da kuturun da ya komo wurin Yesu?

Idan ka yi tunani game da shi, za ka ga cewa mutane da yawa sun yi maka abubuwa da yawa. Alal misali, ka taɓa rashin lafiya?— Wataƙila ba ka taɓa rashin lafiya ba kamar waɗannan kutare goma, amma wataƙila ka taɓa yin mura ko kuma ciwon ciki. Akwai waɗanda suka kula da kai?— Wataƙila sun ba ka magani kuma sun yi maka wasu abubuwa. Ka yi farin ciki cewa sun taimake ka ka samu sauƙi?—

Basamariyen ya yi wa Yesu godiya domin ya taimake shi ya samu lafiya, kuma wannan ya sa Yesu farin ciki. Kana tsammanin mamarka da babanka za su yi farin ciki idan ka yi musu godiya sa’ad da suka yi maka wani abu?— Hakika, za su yi farin ciki.

Me ya sa yake da muhimmanci mu tuna mu yi godiya?

Wasu mutane suna yi maka abubuwa kowacce rana ko kuma kowanne mako. Wataƙila aikinsu ne su yi maka waɗannan. Kuma  wataƙila za su yi farin cikin yin waɗannan. Amma wataƙila za ka manta ka yi musu godiya. Malamar makarantarku za ta yi ƙoƙari sosai wajen koyar da ku. Wannan aikinta ne. Amma za ta yi farin ciki idan ka yi mata godiya domin ta koyar da kai.

Wani lokaci mutane suna yi mana abu kaɗan ne kawai. Akwai wanda ya taɓa buɗe maka ƙofa? Ko kuma wani ya taɓa ba ka abinci a lokacin cin abinci? Yana da kyau ka yi godiya ko ga irin waɗannan ƙananan abubuwa ma.

Idan mun tuna mun yi godiya ga mutane da suke duniya, to za mu iya tunawa mu yi godiya ga Ubanmu wanda yake samaniya. Kuma da akwai abubuwa da za mu yi wa Jehovah godiya a kai! Ya ba mu rai da dukan abubuwa masu kyau da suke daɗaɗa rayuwa. Saboda haka, muna da dalilai da yawa na yabon Allah ta wajen faɗan abubuwa masu kyau game da shi kowacce rana.

Game da yin godiya, mu karanta Zabura 92:1; Afisawa 5:20; Kolossiyawa 3:17; da kuma 1 Tassalunikawa 5:18.