Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 BABI NA 17

Hanyar Yin Farin Ciki

Hanyar Yin Farin Ciki

Me ya sa Jehovah ‘Allah mai farin ciki’ ne?

DUKANMU muna so mu yi farin ciki, ko ba haka ba?— Amma ba mutane da yawa ba ne suke farin ciki da gaske. Ka san abin da ya sa?— Domin ba su fahimci asirin yin farin ciki ba ne. Suna tsammanin tara abubuwa da yawa ita ce hanyar yin farin ciki. Amma sa’ad da suka samu waɗannan abubuwa farin cikinsu ba ya daɗewa.

Ga asirin nan mai muhimmanci. Babban Malami ya ce: ‘Da farin ciki da yawa wajen bayarwa fiye da karɓa.’ (Ayukan Manzanni 20:35) Saboda haka, ta yaya za a yi farin ciki?— Hakika, ta wajen bai wa wasu abubuwa da kuma yin ayyuka ga wasu. Ka san da haka?—

Bari mu yi tunani game da wannan. Yesu ya ce wanda ya karɓi kyauta ba zai yi farin ciki ba ne?— A’a, bai faɗi haka ba. Kana son a ba ka kyauta ko ba haka ba?— Kowaye yana so. Muna farin ciki idan aka ba mu abubuwa masu kyau.

 Yesu ya ce da akwai farin ciki mai yawa sa’ad da muka bayar da abu. To, wa za ka ce ya ba mutane abubuwa da yawa fiye da kowa?— Hakika, Jehovah Allah ne.

Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya ba ‘dukan mutane rai da kuma numfashi da dukan abubuwa.’ Yakan ba mu ruwan sama da hasken rana saboda tsiro su fito mu samu abinci. (Ayukan Manzanni 14:17; 17:25) Babu mamaki da Littafi Mai Tsarki ya kira Jehovah ‘Allah mai farin ciki’! (1 Timothawus 1:11) Bai wa mutane abu shi ne abu ɗaya da yake ba wa Allah farin ciki. Kuma sa’ad da muka ba da abu, zai faranta mana rai.

Menene zai sa ka yi farin ciki fiye da ka cinye dukan cincin naka kai kaɗai?

Yanzu, menene za mu ba wa wasu mutane? Menene za ka ce?— Wani lokaci kyauta da za mu yi za ta ci kuɗi. Idan abin a kanti za ka saya dole ka biya kuɗi. Saboda haka, idan irin wannan kyauta kake so ka bayar to dole ne ka tara kuɗi har sai sun kai su sayi abin da kake so ka yi kyauta da shi.

Amma ba dukan kyauta ba ne da za a bayar za a saya a kanti. Alal misali, a lokacin zafi, moɗa ɗaya na ruwan sanyi yana wartsakarwa. Saboda haka, idan ka ba da wannan kyautar ga mutumin da yake da ƙishirwa, za ka samu farin ciki da ake samu in aka ba da kyauta.

Wata rana wataƙila kai da mamarka za ku soya cincin. Wannan zai kasance abin farin ciki. Amma me za ka yi da wasu cincin ɗin da zai sa ka farin ciki fiye da cinye su kai kaɗai?— Hakika, za ka iya ka yi kyauta da su ga abokananka. Za ka so ka yi haka a wani lokaci?—

 Babban Malami da manzanninsa sun san farin cikin bayarwa. Ka san abin da suka ba wasu mutane?— Abu mafi kyau ne a dukan duniya! Sun san gaskiya game da Allah, kuma sun gaya wa wasu wannan bishara da murna. Sun yi haka ba tare da sun ƙyale wasu sun ba su kuɗi ba.

Wata rana manzo Bulus da abokinsa, almajiri Luka suka sami wata mace da take son ta samu farin cikin bayarwa. Sun same ta a bakin kogi. Bulus da Luka sun je wajen ne domin sun ji cewa wajen addu’a ne. Kuma da gaske da suka isa wurin sai suka sadu da wasu mata suna addu’a.

Bulus ya fara gaya wa waɗannan mata bishara game da Jehovah Allah da kuma Mulkinsa. Wata cikinsu, wadda ake kira Lidiya, ta mai da hankali ga abin da suke faɗa. Daga baya, Lidiya ta so ta yi wani abu ta nuna cewa da gaske tana son bisharar da ta ji. Saboda haka, ta ce wa Bulus da Luka: “Idan kun aza ni amintacciya ce ga Ubangiji, ku zo gidana, ku zauna.” Ta sa suka je gidanta.—Ayukan Manzanni 16:13-15.

Menene Lidiya take gaya wa Bulus da Luka?

Lidiya ta yi farin cikin marabtar waɗannan bayin Allah a gidanta. Tana ƙaunarsu domin sun taimake ta ta koyi game da Jehovah da kuma Yesu da yadda mutane za su iya rayuwa har abada. Ta yi farin ciki da ta ba Bulus da Luka abinci da za su ci da kuma wurin da za su huta. Saboda haka, bayarwa na Lidiya ya sa ta farin ciki domin da gaske tana so ta bayar. Wannan wani abu ne da muke bukatar mu tuna. Wani zai iya gaya mana cewa ba da kyauta ya zama dole. Amma idan da gaske ba ma so mu ba da kyauta ba zai sa mu farin ciki ba.

Me ya sa Lidiya ta yi farin cikin yi wa Bulus da Luka tanadi?

Alal misali, a ce kana da minti da kake so ka sha. Idan na ce maka dole ne ka ba wa wani yaro kaɗan, za ka yi farin cikin bayarwa?— Amma idan kana da minti kuma ka sadu da abokin da kake so sosai  fa? Idan ka yi tunanin raba mintin da abokinka, wannan ba zai sa ka farin ciki ba ne?—

A wasu lokatai za mu ƙaunaci mutumin sosai da za mu so mu ba shi dukan abin da muke da shi ba za mu bar kome ba. Idan mun zurfafa a ƙaunar da muke yi wa Allah, haka ya kamata mu ji game da shi.

Me ya sa macen nan matalauciya ta yi farin cikin bayar da dukan abin da take da shi?

Babban Malami ya san wata mace matalauciya da ta ji haka game da Allah. Ya gan ta a haikali a Urushalima. Tana da kwabo biyu ne kawai marasa amfani; abin da take da shi ke nan. Amma ta zuba duka cikin asusun ba da kyauta na haikali. Babu wanda ya sa ta ta yi haka. Yawancin mutanen ba su san abin da ta yi ba. Ta yi haka ne domin tana so ta yi kuma domin tana ƙaunar Jehovah da gaske. Ta yi farin ciki ƙwarai da ta yi haka.—Luka 21:1-4.

Da akwai hanyoyi da yawa da za mu iya bayarwa. Za mu iya tunanin wasu hanyoyi?— Idan muna bayarwa domin da gaske muna so mu bayar, za mu yi farin ciki. Abin da ya sa ke nan Babban Malami ya gaya mana: “Ku bayar.” (Luka 6:38) Idan muka yi, za su sa wasu mutane su yi farin ciki. Kuma za mu zama mafiya farin ciki!

Bari mu karanta game da yadda bayarwa yake kawo farin ciki, a Matta 6:1-4; Luka 14:12-14 ; da kuma 2 Korinthiyawa 9:7.