Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 BABI NA 29

Dukan Liyafa Ce Take Faranta wa Allah Rai?

Dukan Liyafa Ce Take Faranta wa Allah Rai?

Me ya sa Allah ya yi farin ciki da wannan liyafar?

KANA so ka je wajen liyafa?— Suna da daɗi ƙwarai. Kana tsammanin Babban Malami zai so ya je wajen liyafa?— E, ya je bikin da za a iya kiransa liyafa sa’ad da wani ya yi aure, kuma wasu almajiransa sun bi shi. Jehovah, ‘Allah ne mai farin ciki,’ saboda haka yana farin ciki sa’ad da muka ji daɗi a lokatan liyafa masu kyau.—1 Timothawus 1:11; Yohanna 2:1-11.

Shafi na 29 na wannan littafin ya gaya mana cewa Jehovah ya raba Jar Teku saboda Isra’ilawa su wuce. Ka tuna mun karanta wannan?— Daga baya, mutanen suka rera waƙa kuma suka yi rawa suka yabi Jehovah. Wannan kamar liyafa suka yi. Mutanen sun yi murna ƙwarai, kuma mun tabbata cewa Allah ma ya yi murna.—Fitowa 15:1, 20, 21.

Shekara 40 bayan haka Isra’ilawan sun sake yin wata babbar liyafa. A wannan lokacin mutanen da suka gayyace su ba sa bauta wa Jehovah. In gaya maka, mutanen da suka gayyace su suna yi wa wasu alloli sujjada kuma suna yin jima’i da matan da ba nasu ba. Kana tsammanin daidai ne a halarci irin  wannan liyafa?— Jehovah bai yi farin ciki ba, kuma ya yi wa Isra’ilawan horo.—Litafin Lissafi 25:1-9; 1 Korinthiyawa 10:8.

Littafi Mai Tsarki kuma ya yi magana game da bukukuwa biyu na ranar haihuwa. Bikin ranar haihuwar Babban Malami yana ɗaya daga cikinsu ne?— A’a. Dukan waɗannan bukukuwa na mutane ne waɗanda ba su bauta wa Jehovah ba. Ɗaya cikin bukukuwan haihuwar Sarki Hirudus Antipa ne. Shi ne yake sarautar yankin Galili sa’ad da Yesu yake zama a wurin.

Sarki Hirudus ya yi abubuwa da yawa marasa kyau. Ya ƙwace matar ɗan’uwansa. Sunanta Hirudiya. Bawan Allah Yohanna mai Baftisma ya gaya wa Hirudus cewa ba daidai ba ne ya yi haka. Hirudus bai ji daɗin haka ba. Saboda haka, ya sa aka jefa Yohanna a kurkuku.—Luka 3:19, 20.

Sa’ad da Yohanna yake kurkuku, ranar bikin haihuwar Hirudus ta zagayo. Ya shirya babbar liyafa. Ya gayyaci manyan mutane da yawa. Suka ci suka sha suka wala. Sai ’yar Hirudiya ta shigo ta yi musu rawa. Kowa ya ji daɗin rawarta sai Sarki Hirudus ya so ya ba  ta kyauta ta musamman. Ya ce mata: ‘Ko me ki ka roƙe ni, zan ba ki har da rabin mulkina.’

Menene za ta roƙa? Kuɗi? kaya masu kyau? ko nata fada? Yarinyar ba ta san abin da za ta ce ba. Saboda haka, ta je wurin mamarta, Hirudiya, ta ce: ‘Me zan ce a ba ni?’

Ka tuna cewa Hirudiya ta ƙi jinin Yohanna mai Baftisma. Sai ta gaya wa ’yarta ta ce a ba ta kan Yohanna. Yarinyar ta koma wurin sarkin ta ce: “Ina so ka ba ni yanzu yanzu kan Yohanna mai yin baftisma a cikin akushi.”

Sarki Hirudus ba ya so ya kashe Yohanna domin ya sani cewa Yohanna mutumin kirki ne. Amma Hirudus ya riga ya yi alkawari, kuma yana tsoron abin da wasu da suka taru wajen liyafar za su ce idan ya canja ra’ayinsa. Saboda haka, ya aiki wani mutum ya je kurkuku ya tsaro kan Yohanna. Ba da daɗewa ba mutumin ya dawo. Ya kawo kan Yohanna cikin akushi, ya ba wa yarinyar. Sai yarinyar ta ba wa mamarta.—Markus 6:17-29.

Bikin haihuwa ɗayan da Littafi Mai Tsarki ya faɗa ya  fi wannan kyau ne?— Bari mu bincika. Wannan liyafar domin sarkin ƙasar Masar ne. A lokacin liyafar, sarkin ya sa aka tsare kan wani. Sai kuma ya rataye mutumin domin tsuntsaye su ci! (Farawa 40:19-22) Kana tsammanin Allah ya yarda da waɗannan liyafa biyu?— Da za ka so ka kasance a wani cikin waɗannan bukukuwan?—

Menene ya faru a liyafar ranar haihuwar Hirudus?

Mun sani cewa dukan abin da yake cikin Littafi Mai Tsarki yana da dalili. Ya gaya mana game da bukukuwan ranar haihuwa biyu ne kawai. Kuma dukansu biyun an yi munanan abubuwa a lokacin bikin. Saboda haka, me za ka ce Allah yake so ya gaya mana game da bikin ranar haihuwa? Allah yana so ne mu yi bikin ranar haihuwa?—

Hakika a irin waɗannan liyafa a yau, mutane ba sa yanke kan wasu. Amma wannan batun bikin ranar haihuwa ya fara ne daga mutane da ba sa bauta wa Allah na gaskiya. Ga abin da The Catholic Encyclopedia ya ce game da bikin ranar haihuwa da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki: “Masu zunubi ne kawai . . . suke yin biki domin ranar da aka haife su.” Kana so mu zama kamarsu?—

To, Babban Malami fa? Ya yi bikin ranar haihuwarsa ne?— A’a, Littafi Mai Tsarki bai faɗi kome game da bikin haihuwar Yesu ba. Hakika, mabiyan Yesu na farko ba su yi bikin ranar haihuwarsa ba. Ka san abin da ya sa mutane daga baya suka zaɓi ranar 25 ga Disamba su yi bikin ranar haihuwar Yesu?—

An zaɓi wannan ranar ne domin, kamar yadda The World Book Encyclopedia ya ce, “mutanen Roma suna yin bikin Saturn, bikin ranar haihuwar rana.” Saboda haka, mutane suka zaɓi su yi bikin ranar haihuwar a ranar da arna suke da ranar hutu!

Ka san abin da ya sa ba zai yiwu a haifi Yesu a Disamba ba?— Domin Littafi Mai Tsarki ya ce sa’ad da aka haifi Yesu, makiyaya  suna fili daddare. (Luka 2:8-12) Kuma ba yadda za su fita cikin watan sanyi da ruwa na Disamba.

Me ya sa haihuwar Yesu ba za ta kasance a ranar 25 ga Disamba ba ne?

Mutane da yawa sun sani cewa Kirsimati ba bikin ranar haihuwar Yesu ba ne. Kuma sun sani cewa arna suna da biki a wannan ranar da ba ta faranta wa Allah rai. Amma mutane da yawa suna bikin Kirsimati duk da haka. Sun fi damuwa da yin liyafa da yadda Allah ya ɗauke shi. Amma muna so mu faranta wa Jehovah rai, ko ba ma so ne?—

Saboda haka, idan muka yi liyafa, ya kamata mu tabbata cewa suna da kyau a idanun Jehovah. Za mu iya yin su a kowane lokaci a shekara. Ba sai mun jira wata rana ta musamman ba. Za mu iya cin abinci na musamman mu yi wasanni. Za ka so ka yi wannan?— Wataƙila za ka iya gaya wa iyayenka kuma ka shirya liyafa da taimakonsu. Hakan zai yi kyau, ko ba haka ba?— Amma kafin ka shirya liyafa, ka tabbata abu ne wanda Allah zai yarda da shi.

Ta yaya za mu tabbata cewa liyafa da muke yi suna faranta wa Allah rai?

Muhimmancin yin dukan abin da Allah ya yarda da shi an nuna ma a cikin Misalai 12:2; Yohanna 8:29; Romawa 12:2 da 1 Yohanna 3:22.