Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Ka Koya Daga Wurin Babban Malami

 BABI NA 39

Allah Ya Tuna da Dansa

Allah Ya Tuna da Dansa

YESU ya yi kuka sa’ad da abokinsa Li’azaru ya mutu. Kana tsammanin Jehovah ya ji zafi sosai sa’ad da Yesu ya wahala kuma ya mutu?— Littafi Mai Tsarki ya ce an “ɓata” wa Allah rai har ma an ‘cakune’ shi da abin da ya faru.—Zabura 78:40, 41; Yohanna 11:35.

Za ka iya tunanin ɓacin ran Jehovah sa’ad da yake ganin Ɗansa wanda yake ƙauna ya mutu?— Yesu ya tabbata cewa Allah ba zai manta da shi ba. Abin da ya sa ke nan ya furta waɗannan kalmominsa kafin ya mutu: “Uba, a cikin hannuwanka ni ke bada ruhuna.”—Luka 23:46.

Yesu ya tabbata cewa za a ta da shi daga matattu, ba za a bar shi cikin “lahira” ko kuma kabari ba. Bayan an tashi Yesu daga matattu, manzo Bitrus ya yi ƙaulin abin da aka rubuta ne a cikin Littafi Mai Tsarki game da Yesu, yana cewa: “Ba a bar shi cikin Lahira ba, Jikinsa kuma ba ya ga ruɓa ba.” (Ayukan  Manzanni 2:31; Zabura 16:10) A’a, gawar Yesu ba a bari ta ruɓe ba a kabari.

Sa’ad da Yesu yake duniya, ya gaya wa almajiransa ma cewa ba zai daɗe ba a mace. Ya yi musu bayani cewa za “a kashe shi, rana ta uku kuma a tashe shi.” (Luka 9:22) Hakika, bai kamata almajiran su yi mamaki ba sa’ad da aka tashi Yesu. Amma sun yi mamaki ne?— Bari mu gani.

Da misalin ƙarfe uku ne na rana a ranar Jumma’a Babban Malami ya mutu a kan gungumen azaba. Yusufu, mutum ne mai arziki a Majalisa, kuma mabiyin Yesu ne a asirce. Da ya fahimci cewa Yesu ya mutu, ya tafi wurin Bilatus, gwamna daga Roma. Ya nemi izini ya sauke gawar Yesu daga kan gungume ya binne. Daga baya, Yusufu ya ɗauki gawar Yesu ya kai ta wani lambu inda akwai kabari, wajen da ake saka gawawwaki.

Bayan an saka gawar a cikin kabari, sai aka rufe bakinsa da babban dutse. Aka kai rana ta uku, wadda ta kasance Lahadi. Wannan da asuba ne, gari na da ɗan duhu tukuna. Mutane suna wajen suna gadin kabarin. Manyan firistoci ne suka tura su su yi gadi. Ka san abin da ya sa?—

Firistocin ma sun ji Yesu ya ce za a tashe shi daga matattu. Domin su hana almajiran Yesu daga sace gawarsa kuma daga cewa Yesu ya tashi daga matattu, firistocin ɗin suka saka masu gadi. Farat ɗaya, ƙasa ta fara girgiza. A cikin duhu aka ga haske. Mala’ikan Jehovah ne! Sojojin suka tsorata ƙwarai suka kasa motsi. Mala’ikan ya je kabarin ya ture dutsen. Kabari babu kowa ciki!

Me ya sa babu kome cikin kabarin? Menene ya faru?

Hakika, kamar yadda Bulus ya faɗa ne daga baya: “Wannan Yesu, Allah ya tashe shi.” (Ayukan Manzanni 2:32) Allah ya ba wa Yesu rai da jiki kamar wanda Yesu yake da shi kafin ya zo duniya. An tashe shi da jiki na ruhu kamar wanda mala’iku suke da shi.  (1 Bitrus 3:18) Amma idan mutane za su ga Yesu, to, dole ne ya mai da kansa da jiki irin na mutane. Abin da ya yi ne ke nan?— Bari mu gani.

A lokacin da rana ta fara fitowa. Sojojin sun yi tafiyarsu. Maryamu Magdaliya da wasu mata almajiran Yesu suna kan tafiya zuwa kabarin. Suna cewa a tsakaninsu: ‘Wa za ya ture mana dutsen?’ (Markus 16:3) Amma sa’ad da suka isa kabarin, an riga an ture dutsen. Amma, kabarin babu kome cikinsa! Gawar Yesu babu, ta ɓata! Babu ɓata lokaci, Maryamu Magdaliya ta ruga ta nemi wasu manzannin Yesu.

Wasu matan suka jira a wurin kabarin. Suka yi mamaki: ‘A ina aka ajiye gawar Yesu?’ Sai mutane biyu da fararen tufafi masu walƙiya suka bayyana. Mala’iku ne! Suka ce wa matan: ‘Me ya sa kuke neman Yesu a nan? An tashe shi. Ku yi sauri ku je ku gaya wa almajiransa.’ Za ka iya tunani irin gudun da matan suka yi! A kan hanya suka haɗu da wani mutum. Ka san ko wanene ne?—

Yesu ne ya bayyana da jiki irin na mutane! Sai ya gaya wa matan: ‘Ku je ku gaya wa almajiraina.’ Matan suna farin ciki. Suka je suka gaya wa almajiran Yesu: ‘Yesu yana da rai! Mun gan shi!’ Maryamu ta riga ta gaya wa Bitrus da Yohanna game da kabarin da suka tarar babu kome ciki. Sun ziyarce shi, kamar yadda kake gani a nan. Sun ga likkafani da aka naɗe gawar Yesu da shi, amma ba su san abin da ya faru ba. Suna so su ba da gaskiya cewa Yesu yana da rai, amma suna ganin wannan abin mamaki ne ba zai zama gaskiya ba.

Tunanin menene Bitrus da Yohanna suke yi?

Daga baya a wannan ranar Lahadi, Yesu ya bayyana ga almajiransa biyu suna tafiya a kan hanyar zuwa ƙauyen Imwasu. Yesu yana magana da su suna tafiya tare, amma ba su gane shi ba domin ba shi da irin jikin da yake da shi a dā. Har sai da suka zauna cin abinci tare ya yi addu’a tukuna suka gane shi ne. Manzannin sun yi  farin ciki ƙwarai suka sake tafiya miloli da yawa suka koma Urushalima! Wataƙila ba da daɗewa ba bayan wannan ne Yesu ya bayyana ga Bitrus ya nuna masa cewa yana da rai.

Daga baya a ranar Lahadin da yamma, almajirai da yawa sun taru a wani ɗaki. Ƙofofin suna rufe. Farat ɗaya Yesu ya bayyana a cikin ɗakin da suke! Yanzu sun tabbata cewa lallai Babban Malami yana da rai. Ka yi tunanin yadda farin cikinsu take!—Matta 28:1-15; Luka 24:1-49; Yohanna 19:38–20:21.

Cikin kwana 40 Yesu ya bayyana da jiki dabam dabam ya nuna wa almajiransa cewa yana da rai. Sa’an nan ya bar duniya ya koma  sama wurin Ubansa. (Ayukan Manzanni 1:9-11) Ba da daɗewa ba almajiran suka fara gaya wa mutane cewa Allah ya ta da Yesu daga matattu. Har sa’ad da firist ya yi musu bulala kuma ya sa aka kashe wasu, sun ci gaba da wa’azi. Sun san cewa idan suka mutu, Allah zai tuna da su kamar yadda ya tuna da Ɗansa.

A lokacin da aka tashi Yesu cikin shekara, tunanin menene mutane da yawa suke yi? Tunanin menene kake yi?

Almajiran Yesu na farko sun bambanta da mutane da yawa a yau! Waɗannan mutane suna tunanin zomo ne kawai na Ista da kuma ƙwayaye masu launi na Ista a lokacin da aka tashi Yesu daga matattu. Amma Littafi Mai Tsarki bai yi magana ba game da zomo na Ista da kuma ƙwayaye. Ya yi magana ne game da bauta wa Allah.

Za mu iya zama kamar almajiran Yesu ta wajen gaya wa mutane cewa Allah ya yi abin ban mamaki sa’ad da ya tashi Ɗansa daga matattu. Kada mu ji tsoro, ko mutane sun ce za su kashe mu. Idan muka mutu, Jehovah zai tuna da mu ya tashe mu, kamar yadda ya tashi Yesu.

Ba ma farin ciki ne da muka sani cewa Allah yana tunawa da waɗanda suka bauta masa kuma zai tashe su daga matattu?— Sanin waɗannan ya kamata ya sa mu so mu san yadda za mu sa Allah ya yi farin ciki. Ka san cewa za mu iya yin haka?— Bari mu yi magana game da wannan a gaba.

Ba da gaskiya ga tashin Yesu daga matattu ya kamata ya sa begenmu da bangaskiyarmu su yi ƙarfi. Don Allah ka karanta Ayukan Manzanni 2:22-36; 4:18-20; da kuma 1 Korinthiyawa 15:3-8, 20-23.