Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 BABI NA 42

Abin da Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Aiki

Abin da Ya Sa Ya Kamata Mu Yi Aiki

MENENE kake so sosai, wasa ko kuma aiki?— Babu laifi a yi wasa. Littafi Mai Tsarki ya ce Urushalima tana cike da ‘yara maza da ’yan mata suna wasa’ a dandalinta.—Zechariah 8:5.

Babban Malami ya yi farin ciki sa’ad da ya ga yara suna wasa. Kafin ya zo duniya, ya ce: “Ina nan wurinsa, gwanin mai-aiki ne: . . . kullum ina farinciki a gabansa.” Ka lura cewa Yesu yana aiki tare da Jehovah a sama. Kuma sa’ad da yake can, ya ce: “Daulata tana wurin ’yan adam.” Hakika, kamar yadda muka koya da farko, Babban Malami yana ƙaunar kowa, har da yara ƙanana.—Misalai 8:30, 31.

Menene Babban Malami ya more kafin ya zo duniya?

 Kana tsammanin Yesu ya yi wasa sa’ad da yake yaro?— Ƙila ya yi wasa. Tun da shi ‘gwanin aiki’ ne a sama, ya yi aiki ne a duniya?— E, an kira Yesu ‘ɗan masassaƙi.’ Amma kuma an kira shi, shi kansa “masassaƙi.” Menene wannan ya nuna?— Wannan ya nuna cewa Yusufu wanda ya yi renon Yesu ɗansa, lallai ya koya masa. Saboda haka, Yesu kansa ya zama masassaƙi.—Matta 13:55; Markus 6:3.

Yesu wane irin masassaƙi ne?— Tun da gwanin aiki ne a sama, kana tsammanin ya zama gwanin sassaƙa a duniya?— Ka yi la’akari da wuyar aikin sassaƙa a wancan lokacin. Wataƙila dole ne Yesu ya je ya sare itace, ya rarraba shi, ya kwaso su ya kawo gida,  kuma ya sifanta katakon ya mai da shi teburi, benci, ko kuma wasu abubuwa.

Kana tsammanin wannan aikin ya faranta wa Yesu rai?— Za ka yi farin ciki idan za ka iya yi wa mutane tebura, kujeru ko kuma wasu abubuwa domin su yi amfani da su?— Littafi Mai Tsarki ya ce yana da kyau mutum ya yi “murna cikin aikinsa.” Aiki yana ba da farin ciki da ba za ka iya samu ba daga wasa.—Mai-Wa’azi 3:22.

Aiki yana yi mana amfani a jiki da kuma a tunaninmu. Yara da yawa suna zama su kalli telibijin ko kuma su kalli wasan bidiyo. Sai su yi ƙiba su zama marasa ƙarfi, kuma ba sa farin ciki. Ba sa faranta wa wasu rai ma. Menene muke bukatar mu yi domin mu yi farin ciki?—

A Babi na 17 na wannan littafin mun koyi cewa yin wani abu domin mu taimaki wasu yana kawo farin ciki. (Ayukan Manzanni 20:35) Littafi Mai Tsarki ya kira Jehovah ‘Allah mai farin ciki.’ (1 Timothawus 1:11) Kuma kamar yadda muka karanta a Misalai, kullum Yesu yana “farinciki a gabansa.” Me ya sa Yesu yake farin ciki?— Ya ba da dalili guda sa’ad da ya ce: “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.”—Yohanna 5:17.

Sa’ad da Yesu yake duniya, ba aikin sassaƙa ya yi ba a dukan kwanan rayuwarsa. Jehovah Allah yana da aiki na musamman da zai yi a duniya. Ka san kowane irin aiki ne wannan?— Yesu ya ce: “Dole sai in yi Bishara ta mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luka 4:43) A wasu lokatai, idan Yesu ya yi wa mutane wa’azi suna gaskata abin da ya ce kuma su gaya wa wasu abin da ya ce, kamar yadda wannan Basamariyar da kake gani a nan ta yi.—Luka 4:43; Yohanna 4:7-15, 27-30.

Waɗanne irin ayyuka biyu ne Yesu ya yi sa’ad da yake duniya?

Yaya Yesu ya ji game da yin wannan aikin? Kana tsammanin  yana so ya yi aikin?— Yesu ya ce: “Abincina ke nan, in yi nufin wanda ya aiko ni, in cika aikinsa.” (Yohanna 4:34) Sau nawa kake so ka ci abincin da kake so sosai?— Wannan ya nuna maka yadda Yesu yake so ya yi aikin da Allah ya ba shi.

Allah ya yi mu yadda koyon aiki zai sa mu yi farin ciki. Ya ce kyautarsa ga mutum shi ne ya yi “murna cikin aikinsa.” Idan ka koyi ka yi aiki sa’ad da kake yaro, rayuwarka gaba ɗaya za ta zama abin murna.—Mai-Wa’azi 5:19.

Wannan ba ya nufin cewa yaro zai iya yin aikin babban mutum, amma dukanmu za mu iya yin wasu ayyuka. Iyayenka ƙila su riƙa zuwa aiki kowacce rana domin su samu kuɗi saboda iyalinku su samu abinci da kuma gidan da za ku zauna a ciki. Kuma kamar yadda ka sani, da akwai ayyuka da yawa da ake bukatar a yi a gida domin a tsabtace gida.

Wane aiki ne za ka iya yi da zai amfani kowa a iyali?— Za ka iya taimakawa ka shirya tebur, ka wanke kwanuka, ka je ka zubar da shara, ka tsabtace ɗakinka, ka kuma kwashe abin wasanka. Wataƙila kana yin wasu cikin waɗannan. Waɗannan ayyuka hakika suna amfanar iyalin.

Me ya sa yake da muhimmanci ka kwashe abin wasanka bayan ka gama wasa da su?

Bari mu ga yadda irin waɗannan ayyuka suke da amfani. Ya kamata ka kwashe abin wasa bayan ka gama wasa. Me ya sa za ka ce wannan yana da muhimmanci?— Domin zai sa gida ya yi tsabta, kuma zai hana mutane su ji ciwo. Idan ba ka kwashe abin wasanka ba, wata rana mamarka za ta zo hannunta cike da kaya kuma ta taka wani cikinsu. Wataƙila ta yi tuntuɓe ta faɗi ta ji ciwo. Wataƙila har ma a kai ta asibiti. Haka zai yi muni, ko ba haka ba?— Saboda haka, idan ka kwashe abin wasanka bayan ka yi wasa, hakan yana da amfani.

Da akwai wasu ayyuka da yara za su yi. Alal misali, ayyukan makaranta.  A makaranta ake koyon yadda ake karatu. Wasu yara suna ganin karatu abin farin ciki ne, wasu kuma sun ce yana da wuya. Ko kamar yana da wuya da farko, za ka yi farin ciki idan ka koyi ka yi karatu da kyau. Idan ka koyi karatu da akwai abubuwa masu daɗi da yawa da za ka koya. Za ka iya karanta littafin Allah, Littafi Mai Tsarki da kanka. Saboda haka, idan ka yi aikinka na makaranta da kyau, yana da amfani ko ba haka ba?—

Da akwai wasu mutane da suke ƙoƙarin su guje wa aiki. Wataƙila ka san wani da yake yin haka. Amma tun da Allah ya yi mu mu yi aiki, ya kamata mu koyi yadda za mu yi murna wajen aiki. Yaya Babban Malami ya more aikinsa?— Kamar cin abinci ne da yake so sosai. Wane aiki yake maganarsa?— Gaya wa wasu game da Jehovah Allah da kuma yadda za su samu rai madawwami.

Saboda haka, ga wani abin da zai taimake mu mu ji daɗin yin aiki. Ka tambayi kanka, ‘Me ya sa ake bukatar a yi wannan aikin?’ Idan ka san abin da ya sa wani abu yake da muhimmanci, yinsa ba zai yi wuya ba. Ko aikin yana da wuya ko babu, ka yi aiki mai kyau. Idan ka yi za ka yi murna cikin aikinka, kamar yadda Babban Malami ya yi.

Littafi Mai Tsarki zai taimaki mutum ya zama mai aiki da kyau. Ka karanta abin da ya ce a Misalai 10:4; 22:29; Mai-Wa’azi 3:12, 13; da kuma Kolossiyawa 3:23.