“Waɗannan zantattuka fa, da ni ke umurce ka yau, za su zauna cikin zuciyarka: kuma za ka koya wa ’ya’yanka su da anniya.”—Kubawar Shari’a 6:6, 7

A lokacin da Jehobah ya tsara yadda iyali za ta kasance, ya ba iyaye hakkin kula da ’ya’yansu. (Kolosiyawa 3:20) A matsayinku na iyaye, hakkinku ne ku yi rainon ’ya’yanku don su ƙaunaci Jehobah kuma su zama mutanen kirki. (2 Timotawus 1:5; 3:15) Wajibi ne ku yi ƙoƙari ku san abin da ke cikin zuciyar ’ya’yanku. A gaskiya, yana da muhimmanci ku kafa musu misali mai kyau. Dole Kalmar Jehobah ta kasance a zuciyarku kafin ku koya wa ’ya’yanku ita sosai.Zabura 40:8.

 1 KADA KU SA YARANKU SU JI TSORON TATTAUNAWA DA KU

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: ‘Ku yi hanzarin ji, ku yi jinkirin yin magana.’ (Yaƙub 1:19) Kuna so yaranku su riƙa tattaunawa da ku. Saboda haka, ku nuna musu cewa za ku saurare su a duk lokacin da suke so su tattauna da ku. Idan kuna so su gaya muku abin da ke zuciyarsu, kada ku hau su da faɗa. (Yaƙub 3:18) Idan suna ganin ku masu zafin hali ko kuma masu kushe mutane, ba za su so su gaya muku abin da ke zuciyarsu ba. Ku bi da ’ya’yanku cikin haƙuri kuma ku riƙa nuna musu cewa kuna ƙaunarsu.Matta 3:17; 1 Korintiyawa 8:1.

SHAWARA:

  • Ku saurara idan yaranku suna so su tattauna da ku

  • Ku riƙa tattaunawa da ’ya’yanku a kai a kai, ba sai suna da damuwa ba

2 KU YI ƘOƘARI KU FAHIMCI ABIN DA SUKE NUFI

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Kowane mutum mai-hankali ya kan yi aikinsa bisa ga ilimi.” (Misalai 13:16) A wasu lokatai, kuna bukatar ku yi nazarin kalmomin da yaranku suka gaya muku don ku fahimci ainihin abin da ke damunsu. Matasa suna yawan ƙara gishiri ko kuma su faɗi abin da ba ya zuciyarsu. Kalmar Allah ta ce: “Wanda ya mayar da magana tun ba ya ji ba, wauta ce gare shi da kunya.” (Misalai 18:13) Saboda haka, kada ku yi saurin fushi da su.Misalai 19:11.

SHAWARA:

  • Ku ƙudura cewa ba za ku katse wa yaranku magana ba ko kuma ku yi saurin ɗaukan mataki, ko da mene ne suka faɗa

  • Ku tuna da yadda ku ma kuka ji sa’ad da kuke yara da kuma abin da ya fi muku muhimmanci a lokacin

 3 KU KASANCE DA HAƊIN KAI

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ɗana, ka ji koyarwar ubanka, dokar uwarka kuma kada ka yar da ita.” (Misalai 1:8) Jehobah ya ba iyaye iko bisa yaransu. Wajibi ne ku koya wa yaranku yadda za su girmama ku kuma su yi muku biyayya. (Afisawa 6:1-3) A duk lokacin da iyaye ba su kasance da “nufi ɗaya” ko kuma haɗin kai ba, yaransu za su gano hakan. (1 Korintiyawa 1:10, Littafi Mai Tsarki) Idan ya faru cewa ra’ayinku ya saɓa a batun raino, kada ku nuna musu hakan domin za su rena ku.

SHAWARA:

  • Ku tsai da shawara a kan yadda za ku riƙa yi wa yaranku horo

  • Idan ra’ayinku a kan yadda za ku hori yaranku bai zo ɗaya ba, ku yi ƙoƙari ku fahimci juna

 4 KU KASANCE DA TSARI

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ka goyi [‘yi rainon,’ NW] yaro cikin hanya da za shi bi.” (Misalai 22:6) Yaranku ba za su kasance da tarbiyya mai kyau haka kwatsam ba. Wajibi ne ku tsara yadda za ku koyar da su, kuma wannan tsarin ya haɗa da yin horo. (Zabura 127:4; Misalai 29:17) Ba yi wa yaro duka ne kawai horo ba, amma horo ya ƙunshi taimaka masa ya fahimci muhimmancin umurnin da aka ba shi. (Misalai 1:5) Ƙari ga haka, ku taimaka wa yaranku su so Kalmar Allah kuma su fahimci ƙa’idodin da ke cikinta. (Zabura 1:2) Hakan zai taimaka musu su kasance da lamiri mai kyau.Ibraniyawa 5:14.

SHAWARA:

  • Ka taimaki yaranka su ɗauki Jehobah a matsayin Wanda ya wanzu da gaske kuma za su iya dogara da shi

  • Ka taimaka musu su guji abubuwan da za su iya ɓata ɗabi’arsu, kamar waɗanda ke Intane da kuma dandalin sada zumunta. Ku koya musu yadda za su guji masu yin lalata da yara

‘Ka yi rainon yaro cikin hanya da za shi bi’