Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu

 BABI NA GOMA SHA TARA

Ya Kāre, Ya Tanadar Kuma Ya Jimre

Ya Kāre, Ya Tanadar Kuma Ya Jimre

1, 2. (a) Waɗanne canje-canje ne Yusufu da iyalinsa suke bukatar su yi? (b) Mene ne Yusufu ya gaya wa matarsa?

YUSUFU ya daɗa wa jakin kaya. Ka yi tunanin yadda yake waiwaya yana kallon ƙauyen Bai’talami kuma ya daddaɓa jakin su soma tafiya. Babu shakka, yana tunanin doguwar tafiya da ke gabansu. Za su ƙasar Masar inda ake wani yare da kuma al’ada dabam. Hakika, ya damu da yadda iyalinsa za su saba da sabon yanayin.

2 Mala’ikan Jehobah ya gaya wa Yusufu a mafarki cewa suna bukatar su bar Bai’talami nan da nan domin Sarki Hirudus yana so ya kashe ɗansu. Ko da yake Yusufu ya ji nauyin gaya wa matarsa ƙaunatacciya wannan labarin, amma ya yi hakan da gaba gaɗi. (Karanta Matta 2:13, 14.) Maganar ta dami Maryamu ƙwarai, kuma tana mamakin dalilin da zai sa wani zai so ya kashe yaron da bai san hawa ko sauka ba. Sun dogara ga Jehobah kuma sun shirya su tafi Masar ko da yake ba su san ainihin dalilin ba.

3. Ka bayyana yadda Yusufu da iyalinsa suka bar Bai’talami. (Ka kuma duba hoton.)

3 Sa’ad da Yusufu da Maryamu da Yesu suka bar Urushalima daddare, mutane suna barci tun da yake ba su san ƙullin da Sarki Hirudus ya yi ba. Sa’ad da gari ya soma wayewa, wataƙila Yusufu yana tunanin yadda rayuwa za ta kasance musu a inda za su. Yaya kafinta da kuma talaka kamarsa zai iya kāre iyalinsa daga magabta masu ƙarfi sosai? Shin zai iya ci gaba da kula da su? Shin zai iya gama wannan aiki na rainon wannan ɗa na musamman da Jehobah Allah ya ce ya yi? Yusufu ya fuskanci ƙalubale masu wuya. Yayin da muke yin la’akari da yadda ya shawo kan kowannensu, za mu ga abin da ya sa ubanni da kuma dukanmu muke bukatar mu yi koyi da bangaskiyar Yusufu.

Yusufu Ya Kāre Iyalinsa

4, 5. (a) Ta yaya rayuwar Yusufu ta canja dindindin? (b) Ta yaya wani mala’ika ya ƙarfafa Yusufu ya yi aikin da aka ba shi?

4 Rayuwar Yusufu ta canja gabaki ɗaya sa’ad shi da ’yar Heli  suka yi alkawarin aure fiye da shekara ɗaya da ta shige. Yusufu ya san cewa Maryamu tana ƙaunar Jehobah kuma tana bin mizanansa, amma sai ya ji cewa ta yi juna biyu. Ya so ya sake ta a ɓoye don kada ta sha kunya da kuma wulaƙanci. * Amma, wani mala’ika ya bayyana masa a mafarki cewa ruhu mai tsarki ne ya sa Maryamu ta yi juna biyu. Mala’ikan ya kuma ce ɗan da za ta haifa zai “ceci mutanensa daga zunubansu.” Ya tabbatar wa Yusufu cewa: “Kada ka ji tsoro ka auro Maryamu matarka.”—Mat. 1:18-21.

5 Da yake Yusufu mutumi ne mai adalci da biyayya, sai ya yi abin da mala’ikan ya gaya masa. Ya karɓi wannan aiki mai muhimmanci sosai, wato raino da kuma kula da ɗan da ba nasa ba, amma wanda ya fi tamani ga Allah. Bayan haka, Yusufu da matarsa mai juna biyu sun je Bai’talami don su yi rajista, domin sarki ya dokaci dukan mazauna wurin su yi hakan, kuma a wurin ne aka haifi ɗan.

6-8. (a) Mene ne ya sake canja rayuwar Yusufu da iyalinsa? (b) Yaya muka sani cewa Shaiɗan ne ya aika da abin da masanan suke ganin tauraro ne? (Ka kuma duba hasiya.)

6 Yusufu da iyalinsa ba su koma Nazarat ba. Maimakon haka, sun koma zama a Bai’talami da ke da nisan mil 10 daga Urushalima. Su talakawa ne, amma Yusufu ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kāre da kuma kula da Maryamu da Yesu. Da shigewar lokaci, suka soma zama a ƙaramin gida, amma yanayinsu ya kuma canja farat ɗaya sa’ad da wataƙila Yesu ya wuce shekara guda.

7 Wani rukunin masanan taurari daga Gabas, wataƙila ƙasar Babila sun kai musu ziyara. Sun bi bayan abin da suke ganin tauraro ne zuwa gidan Yusufu da Maryamu suna neman yaron da zai zama sarkin Yahudawa. Mutanen sun daraja shi sosai.

8 Waɗannan masanan sun sa rayuwar yaron cikin haɗari, ko da saninsu ko babu. Tauraron da suka gani ya yi musu ja-gora zuwa Urushalima maimakon Bai’talami. * A wajen sun gaya wa mugun Sarki Hirudus cewa suna neman yaron da zai zama sarkin Yahudawa. Abin da suka faɗa ya ta da hankalin sarkin sosai.

9-11. (a) Mene ne ya nuna cewa akwai wanda ya fi Hirudus da kuma Shaiɗan iko? (b) Me ya sa yadda aka kwatanta tafiyar su Yusufu a littafin Afokirifa ya yi dabam da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki?

9 Amma, akwai wanda ya fi Hirudus da kuma Shaiɗan iko. Yaya muka sani? Sa’ad da baƙin suka iso gidansu Yesu kuma suka  gan shi tare da mahaifiyarsa, sai suka ba shi kyauta kuma ba su karɓi kome ba. Babu shakka, Yusufu da Maryamu sun yi mamaki cewa sun sami “zinariya da lubban da jawul” domin kaya ne masu tamani. Masanan sun yi niyya su koma wurin Sarki Hirudus don su gaya masa inda suka ga ɗan yaron. Amma, Jehobah ya hana su kuma ya gaya musu a mafarki cewa su koma gida ta wata hanya dabam.—Karanta Matta 2:1-12.

10 Ba da daɗewa ba da masanan suka tafi, sai mala’ikan Jehobah ya gaya wa Yusufu a mafarki cewa: “Tashi, ka ɗauki ɗan yaron da uwarsa, ka gudu zuwa cikin Masar, ka zauna can har sai ka ji daga gare ni: gama Hirudus za ya nemi ɗan yaron domin shi halaka shi.” (Mat. 2:13) Saboda haka, kamar yadda aka faɗa ɗazu, Yusufu ya yi biyayya nan da nan. Da yake ya fi so ya kāre ɗansa, sai ya ƙaura zuwa Masar tare da iyalinsa. Yusufu zai yi amfani da kyautar da waɗannan masanan suka kawo wajen kula da iyalinsa a hanya da kuma sa’ad da suke ƙasar Masar.

Yusufu ya sadaukar da kai kuma ya yi saurin ɗaukan mataki don ya kāre ɗansa

11 A littafin ƙage da almara na afokirifa, an ƙara gishiri a labarin don a nuna cewa tafiyar ta yi sumul, an ce Yesu ya yi mu’ujiza a hanya kamar su, gajartar da tafiyar da hana ’yan fashi su kama su da kuma sa itatuwan dabino su yi ƙasa don mahaifiyarsa ta tsinka. * Amma, da gaske, tafiya ce mai nisa sosai zuwa ƙasar da ba su taɓa zuwa ba.

Yusufu ya canja salon rayuwarsa don ya kāre iyalinsa daga haɗari

12. Ta yaya iyaye da suke rainon yaransu a wannan duniya da ke cike da mummunan tasiri za su iya yin koyi da Yusufu?

12 Iyaye za su iya koyon darussa da yawa daga Yusufu. Ya bar aikinsa kuma ya canja salon rayuwarsa don ya kāre iyalinsa daga haɗari. Hakika, ya san cewa iyali amana ce daga Jehobah. Iyaye suna rainon yaransu a duniya da ke cike da mummunan tasirin da zai iya sa yara su yi abubuwan da ba su dace ba, kuma hakan zai sa su sha wahala da kuma ɓata rayuwarsu. Saboda haka, ya kamata iyaye su yi koyi da Yusufu ta wajen ɗaukan mataki nan da nan don su kāre yaransu daga irin wannan mummunan tasiri.

Yusufu Ya Biya Bukatun Iyalinsa

13, 14. Me ya sa Yusufu da matarsa suka koma zama a garin Nazarat?

13 Kamar dai Yusufu da iyalinsa ba su daɗe a Masar ba domin jim kaɗan mala’ikan ya gaya masa cewa Hirudus ya mutu. Yusufu  ya dawo ƙasarsu tare da iyalinsa. Wani annabci a cikin Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah zai kira Ɗansa “daga cikin Masar.” (Mat. 2:15) Yusufu ya cika wannan annabcin, amma a ina ne za su koma da zama yanzu?

14 Yusufu ya mai da hankali sosai domin Archelaus wanda ya ɗauki matsayin Hirudus ma mugu ne kuma yana kisan kai. Allah ya gaya wa Yusufu su koma garinsu Nazarat a Galili a can arewa da ke da nisa daga Urushalima don su rabu da ƙullinsu. A wajen ne shi da Maryamu suka yi rainon yaransu.—Karanta Matta 2:19-23.

15, 16. Mene ne aikin Yusufu ya ƙunsa, kuma wataƙila waɗanne ire-iren kayan aiki ne ya yi amfani da su?

15 Ko da yake Yusufu da matarsa ba su so tara dukiya ba, amma rayuwa ba ta kasance musu da sauƙi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce Yusufu kafinta ne, kuma wannan aikin ya ƙunshi yankan itace da kwashewa da busarwa don a yi amfani da shi wajen gina jinka da yin kwalekwale da gadaje da amalanke da karkiya da kayan noma iri-iri. (Mat. 13:55) Aiki ne mai wuya sosai. Kafinta a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki yakan yi aiki a gaban gidansa ko kuma a shago kusa da gidan.

16 Yusufu ya yi amfani da kayan aiki dabam-dabam, wataƙila mahaifinsa ne ya ba shi wasu. Mai yiwuwa ya yi amfani da ɗan gatari da zarto da gizago da guduma da ɗan bugu da makankari da kuma mahuji da danƙo iri-iri da kuma wasu ƙusoshi, ko da yake suna da tsada.

17, 18. (a) Mene ne Yesu ya koya daga wurin babansa? (b) Me ya sa Yusufu ya yi sana’arsa da ƙwazo sosai?

17 Ka yi tunanin yadda Yesu ƙaramin yaro yake kallon mahaifinsa sa’ad da yake aiki. Yesu yana kallon yadda babansa yake yin aikin da ƙarfi da basira da kuma dabara. Wataƙila Yusufu ya soma nuna wa ɗansa yadda ake wasu ayyuka masu sauƙi kamar yin amfani da busashen fatar kifi don ya goge jikin katako. Mai yiwuwa ya koya wa Yesu ire-iren itatuwa da ya yi amfani da su kamar su ɓaure da ceɗiya da kuma zaitun.

Yusufu ya koya wa ɗansa aikin kafinta

 18 Yesu ya kuma koya cewa babansa yana da ƙarfin yanka itatuwa da kuma kula da shi da mahaifiyarsa da kuma ƙannensa. Ban da Yesu, Yusufu da Maryamu sun haifi aƙalla yara shida. (Mat. 13:55, 56) Yusufu ya yi aiki tuƙuru don ya kula da kuma ciyar da su duka.

Yusufu ya san cewa taimaka wa iyalinsa su bauta wa Allah kuma su ƙulla dangantaka da shi ya fi muhimmanci

19. Ta yaya Yusufu ya taimaki iyalinsa su ƙulla dangantaka da Jehobah kuma su bauta masa?

19 Ko da yake Yusufu ya biya bukatun iyalinsa, amma ya san cewa taimaka wa iyalinsa su bauta wa Jehobah kuma su ƙulla dangantaka da shi ya fi muhimmanci. Saboda haka, ya keɓe lokaci don ya koya wa yaransa game da Jehobah Allah da kuma dokokinsa. Shi da matarsa sukan kai yaran majami’a a kai a kai, inda ake bayyana da kuma tattauna dokokin Allah. Wataƙila Yesu ya yi wa babansa tambayoyi game da Jehobah da dokokinsa kuma baban ya yi iya ƙoƙarinsa don ya amsa tambayoyin. Yusufu yakan kai iyalinsa idodin da ake yi a Urushalima. Wataƙila tafiyar mil 75 da Yusufu yake yi zuwa wurin Idin Ƙetarewan da yin idin da kuma dawowa gida yana ɗaukansa wajen mako biyu.

Yusufu yakan kai iyalinsa bauta a haikalin da ke Urushalima a kowace shekara

20. Ta yaya ubanni za su yi koyi da Yusufu?

20 Shugabannin iyalai a yau suna yin koyi da Yusufu. Ko da yake suna aiki tuƙuru don su biya bukatun iyalinsu, sun fi mai da hankali ga koya wa yaransu game da Jehobah. Suna yin iya ƙoƙarinsu su gudanar da bauta ta iyali kuma su kai yaransu taron ikilisiya da kuma manyan taro. Kamar Yusufu, sun san cewa koya wa yaransu game da Jehobah shi ne abu mafi muhimmanci da za su iya yi musu.

“Da Baƙin Ciki”

21. Waɗanne ayyuka ne Yusufu da iyalinsa suke yi a lokacin Idin Ƙetarewa, kuma yaushe ne shi da matarsa suka gano cewa Yesu bai bi su ba?

21 Kamar yadda Yusufu ya saba yi, ya kai iyalinsa Urushalima sa’ad da Yesu yake ɗan shekara 12. Lokacin Idi ne, kuma iyalai da yawa sun yi tafiya tare ta hanyoyin karkara mai dausayi. Sa’ad da suka kusan isa tuddan Urushalima, sai mutane da yawa suka soma rera waƙoƙin zabura. (Zab. 120–134) Mai yiwuwa mutane sun yi maƙil a birnin. Bayan da aka gama idin, sai iyalai da yawa suka koma gida tare. Yusufu da matarsa sun ɗauka cewa  Yesu ya bi wasu, mai yiwuwa danginsu da suke komawa gida tare. Sai bayan sun yi tafiya na kwana ɗaya ne suka gano cewa Yesu ba ya tare da su.—Luk 2:41-44.

22, 23. Mene ne Yusufu da matarsa suka yi sa’ad da suka gano cewa Yesu ba ya tare da su, kuma mene ne mamarsa ta ce sa’ad da suka same shi?

22 Yusufu da matarsa sun koma Urushalima kuma suka nemi Yesu a ko’ina. Ka yi tunanin yadda birnin ya yi shuru yanzu da kowa ya koma gida, kuma suna ta ƙwala ihu da sunan ɗansu. Suna mamaki inda yaron yake! Bayan kwana uku da suke nemansa, wataƙila Yusufu ya soma tunani cewa bai riƙe amanar da Jehobah ya ba shi da kyau ba. A ƙarshe, sai suka shiga cikin haikalin kuma suka same shi a wani babban ɗaki yana zaune a  tsakanin masanan Doka. Babu shakka, hankalin Yusufu da matarsa ya kwanta yanzu.—Luk 2:45, 46.

23 Yesu yana sauraron masanan kuma yana yi musu tambayoyi. Mutanen sun yi mamaki ƙwarai don fahimin yaron da kuma amsoshin da yake bayarwa. Iyayensa sun yi mamaki cewa ya yi hakan, amma Yusufu bai ce uffan ba. Amma, furucin Maryamu ya nuna yadda suka ji: “Ɗana, don menene ka yi mana haka? ga ubanka da ni da baƙinciki muka neme ka.”—Luk 2:47, 48.

24. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da iyaye suke fuskanta sa’ad da suke rainon yara?

24 Wannan labarin ya bayyana abin da iyaye suke fuskanta  yayin da suke rainon yara. Yusufu da matarsa sun sha wahala, duk da cewa ɗansu kamili ne. Rainon yara a cikin wannan duniya yana kawo “baƙin ciki,” amma sanin cewa Littafi Mai Tsarki ya ambata ƙalubale da iyaye suke fuskanta zai ƙarfafa su.

25, 26. Ta yaya Yesu ya amsa iyayensa, kuma yaya wataƙila Yusufu ya ji game da kalamin ɗansa?

25 Yesu ya zauna a inda zai taimaka masa ya kusaci Jehobah sosai, kuma ya ji daɗin koyon abubuwa da yawa game da shi. Ya amsa iyayensa da ladabi yana cewa: “Me ya sa kuka neme ni? ba ku san wajib ne a gareni in yi aikin sha’anin Ubana ba?”—Luk 2:49.

26 Babu shakka cewa Yusufu ya yi tunani sosai sau da sau a kan abin da Yesu faɗa. Wataƙila hakan ya sa shi alfahari, domin ya ƙoƙarta sosai wajen koya wa ɗansa ya ƙaunaci Jehobah. Yesu ƙaramin yaro ne a lokacin, amma dangantakarsa da Yusufu ta taimaka masa ya san yadda uba mai ƙauna da kuma kula yake ji game da yaransa.

27. Wane gata ne kake da shi a matsayin uba, kuma me ya sa ya kamata ka tuna da misalin Yusufu?

27 Idan kai mahaifi ne, shin ka fahimci cewa kana da gatan taimaka wa yaranka su ɗauki Jehobah a matsayin Uba mai ƙauna da kuma kula? Hakazalika, idan kana da yara da ba kai ka haifa ba, ka tuna da misalin Yusufu kuma ka bi da kowane yaro bisa ga halinsa kuma ka daraja shi. Ka taimaka wa yaran su kusaci Jehobah kuma su ɗauke shi a matsayin Ubansu.—Karanta Afisawa 6:4.

Yusufu Ya Jimre

28, 29. (a) Mene ne abin da ke littafin Luka 2:51, 52 suka nuna mana game da Yusufu? (b) Ta yaya Yusufu ya taimaka wa ɗansa ya kasance da hikima?

28 Littafi Mai Tsarki bai gaya mana game da rayuwar Yusufu bayan rainon Yesu ba. Duk da haka, za mu iya amfana daga misalinsa. Mun karanta cewa Yesu ya ci gaba  da yin “biyayya” ga iyayensa da kuma kasancewa da “hikima da girma, da kuma tagomashi wurin Allah da wurin mutane.” (Karanta Luka 2:51, 52.) Mene ne waɗannan kalaman suka koya mana game da Yusufu? Sun nuna mana cewa ya ci gaba da ja-gorar iyalinsa, shi ya sa ɗansa kamili bai daina girmama shi da kuma bin ja-gorancinsa ba.

29 Mun kuma karanta cewa Yesu ya ci gaba da kasancewa da hikima. Tabbas, Yusufu ya taimaka wa ɗansa ya yi hakan. Akwai wani sanannen karin maganan Yahudawa a lokacin kuma har wa yau ana iya samunsa. Karin maganan ya ce masu arziki da kuma matsayi ne kaɗai suke da hikima, amma mutane masu sana’a kamar kafinta da manoma da maƙera “ba za su iya yin hukunci ko shari’a ba, kuma ba za a same su a inda ake faɗin almara ba.” Amma daga baya, yadda Yesu ya kasance da hikima sosai ya nuna cewa hakan ba gaskiya ba ne. Sa’ad da Yesu yake yaro, ya sha jin ubansa wanda kafinta ne kuma talaka yana koyar da abubuwan da Jehobah ya halalta da kuma waɗanda ya haramta. Babu shakka ya yi hakan a lokatai da yawa.

30. Ta yaya Yusufu ya zama abin koyi ga ubanni a yau?

30 A bayyane yake kuma cewa Yusufu ya kula da Yesu a zahiri. Yesu ya yi girma kuma ya kasance da koshin lafiya da kuzari da kuma farin ciki. Yusufu ya kuma koya wa ɗansa sana’arsa, har ya zama gwani. Shi ya sa mutane suka san Yesu a matsayin “masassaƙi.” (Mar. 6:3) Saboda haka, Yusufu ya yi rainon ɗansa da kyau. Ubanni za su iya yin koyi da Yusufu ta wajen kula da yaransu da kyau kuma su koya musu yadda za su kula da kansu sa’ad da suka yi girma.

31. (a) Mene ne bincike da aka yi ya nuna game da lokacin da Yusufu ya mutu? (Ka duba  akwatin.) (b) Wane misali ne Yusufu ya kafa mana?

31 A lokacin da Yesu ya kusan kai shekara 30 kuma ya yi baftisma, ba mu sake jin labarin Yusufu ba. Bincike ya nuna cewa Maryamu gwauruwa ce a lokacin da Yesu ya soma hidimarsa. (Ka duba akwatin nan  “A Wane Lokaci Ne Yusufu Ya Rasu?”) Duk da haka, Yusufu ya kafa misali mai kyau na uba da ya kāre iyalinsa, ya yi musu tanadi kuma ya jimre har ƙarshe. Ya kamata dukan ubanni da kuma Kiristoci su yi koyi da bangaskiyar Yusufu.

^ sakin layi na 4 A zamanin Yusufu, ana ɗaukan alkawarin aure da muhimmanci sosai kamar an riga an yi auren.

^ sakin layi na 8 Tauraron ba irin wanda muka saba gani ba ne kuma ba Allah ba ne ya aika shi. A bayane yake cewa Shaiɗan ya yi amfani da wannan mugun ƙulli don ya kashe Yesu.

^ sakin layi na 11 Littafi Mai Tsarki ya nuna sarai cewa Yesu ya yi “al’ajibinsa na farko” ne bayan ya yi baftisma.—Yoh. 2:1-11.