Wannan sashen ya koya mana game da matasa da annabawa da kuma sarakuna da yawa da suka kasance da bangaskiya. A ƙasar Suriya, wata yarinya ’yar Isra’ila ta yi imani cewa annabin Jehobah zai iya warƙar da Na’aman. Annabi Iliya ya kasance da gaba gaɗi cewa Jehobah zai kāre shi daga maƙiyansa. Babban Firist mai suna Jehoiada ya sa ransa cikin hadari don ya kāre Jehoash daga hannun kakarsa Athaliah. Sarki Hezekiya ya dogara ga Jehobah don ya san cewa zai ceci Urushalima kuma bai miƙa wuya ga Assuriyawa ba. Sarki Josiah ya cire gumakan da ke ƙasar, ya gyara haikalin Jehobah kuma ya sa mutanensa su soma bauta wa Jehobah.