Jehobah ya ba Isra’ilawa alƙalai don su yi musu ja-goranci amma sun ce suna so a naɗa musu sarki. Sun gaya wa Sama’ila cewa: ‘Duka ƙasar da ke kewaye da mu suna da sarki. Don haka, muna so a naɗa mana sarki.’ A ganin Sama’ila, hakan bai dace ba, sai ya yi addu’a ga Jehobah. Jehobah ya ce masa: ‘Ba kai mutanen suka ƙi ba amma ni suka ƙi. Ka gaya musu cewa za a naɗa musu sarki amma sarkin zai bukaci abubuwa da yawa daga gare su.’ Duk da haka, mutanen suka ce: ‘Ba mu damu ba. Mu dai sarki kawai muke so!’

Jehobah ya gaya wa Sama’ila cewa sunan wanda zai zama sarkin shi ne Saul. Sa’ad da Saul ya ziyarci Sama’ila a birnin Ramah, sai Sama’ila ya naɗa shi sarki ta wajen zuba masa māi a kai.

Bayan haka, sai Sama’ila ya kira Isra’ilawa don ya nuna musu sarkinsu. Amma an nemi Saul an rasa. Ka san me ya sa? Domin ya je ya ɓoye a cikin kayayyaki. Da suka gan shi, sai suka kawo shi gaban jama’a. Saul ya fi duka mutanen tsayi kuma yana da kyau sosai. Sai Sama’ila ya ce: ‘Ga wanda Jehobah ya zaɓa.’ Sai mutanen suka yi ihu kuma suka ce: ‘Ran sarki shi daɗe!’

Da farko, Sarki Saul ya saurari abin da Sama’ila ya gaya masa kuma ya bi umurnin Jehobah. Amma daga baya, sai ya canja. Alal misali, bai kamata sarki ya miƙa hadaya da kansa ba. A wani lokaci, Sama’ila ya gaya wa Saul cewa ya jira shi amma Sama’ila bai zo da sauri ba. Don haka, Saul ya miƙa hadayar da kansa. Mene ne Sama’ila ya yi? Ya gaya masa: ‘Me ya sa ka yi wa Jehobah rashin biyayya?’ Shin Saul ya koyi darasi daga kuskurensa?

Bayan haka, sai Saul ya je ya yi yaƙi da Amalakawa kuma Sama’ila ya gaya masa cewa ya kashe kowa a ƙasar. Amma Saul bai kashe Sarki Agag ba. Jehobah ya gaya wa Sama’ila cewa: ‘Saul ya ƙi ni kuma ba ya mini biyayya.’ Hakan ya sa Sama’ila baƙin  ciki sosai, kuma ya gaya wa Saul cewa: ‘Tun da ba ka bin umurnin Jehobah, zai zaɓi wani sarki.’ Da Sama’ila ya juya zai tafi, sai Saul ya ja rigarsa kuma ta yage. Sai Sama’ila ya gaya wa Saul cewa: ‘Jehobah ya riga ya ƙwace mulki daga hannunka.’ Jehobah zai ɗauki mulkin ya ba wani da ke ƙaunarsa kuma yake bin umurninsa.

“Biyayya ta fi hadaya.”​—1 Sama’ila 15:22