Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Darussa daga Littafi Mai Tsarki

 DARASI NA 41

Dauda da Saul

Dauda da Saul

Sarki Saul ya sa Dauda ya zama shugaban sojojinsa bayan da ya kashe Goliath. Dauda ya ci yaƙi da yawa kuma ya yi suna. A duk lokacin da Dauda ya dawo daga yaƙi, sai mata su fito suna rawa da kuma waƙa. Suna cewa: ‘Saul ya kashe dubbai, amma Dauda ya kashe dubun dubbai!’ Sai Saul ya soma kishin Dauda kuma ya so ya kashe shi.

Dauda ya iya kaɗa molo sosai. Wata rana da Dauda yake kaɗa wa Saul molo, sai ya jefa mashi don ya kashe Dauda. Amma Dauda ya kauce, kuma mashin ya shiga bango. Bayan haka, Saul ya yi ƙoƙari ya kashe Dauda sau da yawa. Daga baya, sai Dauda ya gudu zuwa cikin daji.

Saul ya zaɓi sojoji 3,000 kuma suka fita neman Dauda. Amma bai san cewa ya shiga cikin kogon dutsen da Dauda da  abokansa suka ɓoye ba. Sai abokan Dauda suka ce: ‘Ka sami damar kashe Saul.’ Dauda ya je wurin Saul a hankali kuma ya yanke rigarsa. Amma Saul bai sani ba. Bayan haka, Dauda ya yi da-na-sani domin abin da ya yi reni ne ga sarkin da Jehobah ya naɗa. Bai yarda abokansa su kashe Saul ba. Sai Dauda ya gaya wa Saul cewa da ya kashe shi sa’ad da ya sami damar yin haka. Shin hakan ya sa Saul ya daina neman Dauda?

A’a. Saul ya ci gaba da neman Dauda. Wata rana, sai Dauda da ɗan yayarsa mai suna Abishai suka shiga inda Saul yake barci. Har Abner wanda shi ne sojan da ke tsaron Saul ya yi barci. Sai Abishai ya ce: ‘Mun sami dama! Bari in kashe shi.’ Dauda ya ce: ‘Jehobah da kansa zai hukunta Saul. Mu ɗauki mashinsa da kuma gorar ruwansa.’

Sai Dauda ya hau wata dutse da ke kusa. Ya yi ihu ya ce: ‘Abner, me ya sa ba ka kāre sarki ba? Ina mashin Saul da gorar ruwansa?’ Da Saul ya ji muryar Dauda, sai ya ce: ‘Ka sami zarafin kashe ni, amma ba ka yi hakan ba. Na san cewa kai ne za ka zama sarkin Isra’ila bayan ni.’ Bayan haka, sai Saul ya koma fādarsa. Amma akwai wani a cikin iyalin Saul da yake ƙaunar Dauda.

‘Idan ya yiwu, ku zauna lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku. Kada ku ɗauka wa kanku fansa, ƙaunatattu, amma ku kauce wa fushi.’​—Romawa 12:​18, 19