Dauda ya zama sarki bayan Saul ya mutu. Shekarunsa 30 a lokacin. Bayan da ya yi sarauta na wasu shekaru, sai wata rana daddare ya hango wata kyakkyawar mace daga saman fādarsa. An gaya wa Dauda cewa sunanta Bath-sheba kuma ita matar wani soja mai suna Uriah ne. Dauda ya aika a kira Bath-sheba zuwa fādarsa. Sai ya kwana da ita kuma ta yi ciki. Dauda ya yi ƙoƙarin ya ɓoye abin da ya yi. Ya gaya wa shugaban sojojinsa cewa idan suka je yaƙi, ya ajiye Uriah a gaba. Idan suka soma yaƙi sai su gudu su bar shi. Bayan da aka kashe Uriah a yaƙi, sai Dauda ya auri Bath-sheba.

Amma Jehobah ya ga dukan abubuwan da suka faru. Mene ne zai yi? Jehobah ya aiki annabi Nathan zuwa wurin Dauda. Sai Nathan ya ce: ‘Wani mai arziki yana da tumaki da yawa kuma wani matalauci ma yana da tunkiya ɗaya kawai da yake so sosai. Sai mai arzikin ya ƙwace tunkiyar matalaucin.’ Da Dauda ya ji labarin, sai ya yi fushi sosai, ya ce: ‘Dole a kashe mai arzikin!’ Sai Nathan ya gaya wa Dauda cewa: ‘Kai ne mai arzikin!’ Hakan ya dame Dauda sosai, sai ya ce wa Nathan: ‘Na yi wa Jehobah laifi.’ Laifin ya jawo wa Dauda da kuma iyalinsa matsala sosai. Ko da yake Jehobah ya yi wa Dauda horo, amma bai kashe shi ba domin ya faɗi gaskiya kuma yana da sauƙin kai.

Dauda ya so ya gina wa Jehobah haikali, amma Jehobah ya zaɓi yaron Dauda mai suna Sulemanu ya gina haikalin. Sai Dauda  ya soma shirya wa Sulemanu kayan da zai yi ginin da shi. Ya ce: ‘Dole haikalin Jehobah ya yi kyau sosai. Ko da yake Sulemanu ƙaramin yaro ne, amma zan taya shi tattara kayan da zai yi aikin da shi.’ Dauda ya ba da kyautar kuɗinsa don a yi ginin da shi. Kuma ya nemo mutanen da suka iya aiki sosai. Ya tattara zinariya da azurfa kuma ya sa an yanko itatuwa daga birnin Tyre da Sidon. Sa’ad da Dauda ya kusan mutuwa, ya ba Sulemanu tsarin ginin. Sai ya ce: ‘Jehobah ya ce in rubuta maka waɗannan abubuwan. Kada ka ji tsoro, Jehobah zai taimake ka. Ka yi ƙarfin hali kuma ka soma aiki.’

“Wanda ya rufe laifofinsa ba za ya yi albarka ba: amma dukan wanda ya faɗe su ya kuwa rabu da su za ya sami jinƙai.”​—⁠Misalai 28:⁠13