Isra’ilawa sun sake koma bautar wasu alloli. Saboda haka, Jehobah ya bar Filistiyawa su yi mulki a ƙasarsu. Amma akwai wasu a cikinsu da suke son yin biyayya ga Jehobah. Ɗaya daga cikinsu shi ne Manoah. Shi da matarsa ba su da yara. Wata rana, sai Jehobah ya aiki wani mala’ika wurin matar Manoah. Sai mala’ikan ya ce mata: ‘Za ki haifi yaro kuma shi ne zai ceci Isra’ilawa daga hannun Filistiyawa. Zai zama Banaziri.’ Ka san ko waye ne ake kira Banaziri? Bayin Jehobah ne na musamman. Ba a yarda su riƙa yin aski ba.

Bayan wani lokaci, sai matar Manoah ta haifi yaro mai suna Samson. Da yaron ya yi girma, Jehobah ya sa ya zama mai ƙarfi sosai. Samson yana kashe zaki da hannu. Akwai lokacin da Samson ya kashe Filistiyawa 30 shi kaɗai. Don haka, sai Filistiyawa suka tsane shi kuma suna son su kashe shi. Wata rana da Samson yake barci da dare a birnin Gaza, sai suka je suka jira shi a babbar ƙofar birnin don su kashe shi da safe. Amma da tsakar dare, sai Samson ya je ya cire ƙofar birnin. Bayan haka, sai ya ɗauki babbar ƙofar a kafaɗarsa kuma ya kama tafiya har zuwa dutsen Hebron!

Bayan haka, sai Filistiyawa suka je suka sami budurwar Samson mai suna Delilah. Suka ce mata: ‘Za mu ba ki kuɗin azurfa 5,500 idan kika lallashi Samson don ya gaya miki dalilin da ya sa yake da ƙarfi. Muna son mu kama shi mu saka shi a fursuna.’ Da yake Delilah tana kwaɗayin kuɗi sosai, sai ta yarda. Da farko, Samson bai yarda ya gaya mata dalilin da ya sa yake da ƙarfi ba. Amma da ta nace, sai ya gaya mata sirrinsa. Ya ce: ‘Ba a taɓa min aski ba tun da aka haife ni. Idan aka aske gashin kaina, ƙarfina zai ƙare.’ Samson ya yi babban kuskure da ya gaya mata wannan maganar, ko ba haka ba?

Sai Delilah ta je wurin Filistiyawa nan da nan ta ce: ‘Ya gaya  mini sirrinsa!’ Sai ta sa Samson ya kwanta a cinyarta kuma ya yi barci sosai. Bayan haka, sai ta sa wani ya yi masa aski. Da aka gama aske gashin kansa, sai Delilah ta yi ihu: ‘Samson ka tashi ga Filistiyawa suna zuwa!’ Da Samson ya tashi, sai ya ji bai da ƙarfi kuma. Sai Filistiyawa suka kama shi suka cire ƙwayar idanunsa kuma suka saka shi a fursuna.

Wata rana, dubban Filistiyawa sun taru a wani ɗakin allahnsu mai suna Dagon kuma suka yi ihu: ‘Allahnmu ya ba mu Samson! Ku fito da shi nan! Muna son ya zo ya yi mana wasa.’ Kuma sun sa ya tsaya a tsakanin ginshiƙai guda biyu kuma suna ta masa zolaya. Sai Samson ya ce: ‘Ya Jehobah, ka taimaka mini ka ba ni ƙarfi sau ɗaya kawai.’ A wannan lokacin, gashin kan Samson ya riga ya soma girma. Sai ya ture ginshiƙan ɗakin da dukan ƙarfinsa. Sai ɗakin gabaki ɗaya ya rushe kuma ya kashe shi da kuma dukan mutanen da ke ciki.

“Ubangiji Yahweh ƙarfina ne.”​—Ishaya 12:2