Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 DARASI NA 33

Ruth da Naomi

Ruth da Naomi

A lokacin da ake yunwa a ƙasar Isra’ila ne Naomi da maigidanta da kuma yaransu biyu suka ƙaura zuwa ƙasar Mowab. Ana nan, sai maigidan Naomi ya mutu. Yaranta sun auri ’yan Mowab masu suna Ruth da Orpah. Abin baƙin cikin shi ne, daga baya, sai yaran Naomi suka mutu.

Da Naomi ta ji cewa an daina yunwa a ƙasar Isra’ila, sai ta ce za ta koma gida. Sai Ruth da Orpah suka soma bin ta, amma Naomi ta gaya musu cewa: ‘Ku matan yarana ne kuma na ji daɗin zama da ku don kuna da hankali. Amma ina son ku koma Mowab don ku sake yin aure.’ Sai matan suka ce: ‘Muna ƙaunarki kuma ba ma son mu bar ki.’ Sai Naomi ta ci gaba da gaya musu su koma. Bayan haka, sai Orpah ta koma amma Ruth ta ƙi komawa. Sai Naomi ta gaya mata cewa: ‘Ga Orpah cān tana komawa gida kuma za ta ci gaba da bauta wa allolinku. Ke ma ki bi ta.’ Amma Ruth ta ce: ‘Ba zan bar ki ba. Mutanenki za su zama mutanena, Allahnki kuma zai zama Allahna.’ Yaya kake ganin Naomi ta ji sa’ad da Ruth ta faɗi hakan?

Ruth da Naomi sun iso Isra’ila a lokacin da ake girbin hatsi. Wata rana, sai Ruth ta je gonar wani mutum mai suna Boaz don ta yi kalar hatsi. Kuma Rahab ce ta haifi wannan mutumin. Ya ji labari cewa Ruth ’yar Mowab ce da ta manne wa Naomi. Sai ya gaya wa masu yi masa aiki su riƙa barin wasu hatsi don Ruth ta samu.

 Da Ruth ta koma gida, sai Naomi ta tambaye ta: ‘A gonar waye ne kika yi kalar hatsi yau?’ Sai Ruth ta ce: ‘A gonar wani mutum mai suna Boaz.’ Naomi ta ce mata: ‘Boaz dangin maigidana ne. Ki riƙa zuwa gonarsa yin kala domin babu abin da zai same ki.’

Sai Ruth ta ci gaba da yin kala a gonar Boaz har lokacin da aka daina girbi. Boaz ya lura cewa Ruth tana aiki sosai kuma ita mace ce mai hankali. A zamanin dā, idan mutum ya mutu kuma bai da yara, danginsa zai iya auran matarsa. Sai Boaz ya auri Ruth kuma sun haifi yaro mai suna Obed. Wannan yaron ne ya zama kakan Sarki Dauda. Abokan Naomi sun yi farin ciki sosai kuma suka ce mata: ‘Da farko, Jehobah ya ba ki Ruth kuma ta taimaka miki sosai. Kuma yanzu ya ba ki jika. Yabo ya tabbata ga Jehobah.’

“Waɗansu abokai sun fi ’yan’uwa aminci.”​—Misalai 18:​24, Littafi Mai Tsarki