Musa ya ja-goranci Isra’ilawa shekaru da yawa kuma yanzu ya kusan mutuwa. Sai Jehobah ya gaya masa cewa: ‘Ba kai ba ne za ka kai Isra’ilawa Ƙasar Alkawari ba. Amma zan nuna maka ƙasar.’ Sai Musa ya roƙi Jehobah ya zaɓi wani shugaba da zai riƙa yi wa Isra’ilawa ja-goranci. Sai Jehobah ya gaya masa cewa: ‘Ka je ka gaya wa Joshua cewa shi ne zai zama shugabansu.’

Sai Musa ya gaya wa Isra’ilawa cewa ya kusan mutuwa amma Jehobah ya zaɓi Joshua ya ja-gorance su zuwa Ƙasar Alkawari. Bayan haka, sai Musa ya gaya wa Joshua: ‘Kada ka ji tsoro, Jehobah zai taimake ka.’ Sai Musa ya haura kan Dutsen Nebo kuma Jehobah ya nuna masa ƙasar da ya yi wa Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yakubu alkawari. Musa ya mutu yana ɗan shekara 120.

Jehobah ya gaya wa Joshua cewa: ‘Ka tsallake Kogin Urdun kuma ka je Kan’ana. Zan taimake ka kamar yadda na taimaki Musa. Ka tabbata ka karanta littafin Doka kowace rana. Kada ka ji tsoro, ka yi ƙarfin hali. Ka je ka yi abin da na gaya maka.’

 Sai Joshua ya aiki ’yan leƙen asiri guda biyu zuwa birnin Yariko. A labari na gaba, za mu koyi abin da ya faru a wurin. Da suka dawo, sai suka gaya wa Joshua cewa yanzu ne lokacin da ya dace su tafi ƙasar Kan’ana. Washegari, sai Joshua ya gaya wa al’ummar su tattara kayansu. Sai ya ce firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin su wuce gaba zuwa Kogin Urdun. Kogin yana gudu sosai. Amma da firistocin suka shiga kogin, sai kogin ya daina gudu kuma ruwan ya janye! Sai firistocin suka taka zuwa tsakiyar kogin suka tsaya kuma Isra’ilawa suka tsallake zuwa wancan gefen. Wannan abin al’ajabin ya tuna musu da abin da ya faru a Jar Teku, ko ba haka ba?

Isra’ilawa sun iso Ƙasar Alkawari bayan da suka yi shekaru da yawa a jeji. Yanzu za su iya gina gidaje da birane kuma su yi noma. Babu shakka, ƙasa ce mai cike da madara da zuma.

‘Jehobah zai bi da ku kullayaumin, zai biya bukatarku da abubuwa masu kyau.’​—Ishaya 58:​11, Littafi Mai Tsarki