Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Darussa daga Littafi Mai Tsarki

 DARASI NA 36

Alkawarin da Jephthah Ya Yi

Alkawarin da Jephthah Ya Yi

Isra’ilawa sun sake barin Jehobah kuma suka soma bauta wa allolin ƙarya. Waɗannan allolin ƙaryan ba su taimaki Isra’ilawa ba a lokacin da Ammoniyawa suka yaƙe su. Isra’ilawan sun yi shekaru da yawa suna shan wahala. Daga baya, sai suka ce wa Jehobah: ‘Mun yi zunubi. Muna roƙonka ka ceci mu daga abokan gabanmu.’ Sai Isra’ilawan suka halaka dukan gumakansu kuma suka dawo suna bauta wa Jehobah. Jehobah bai yi farin ciki don wahalar da suke sha ba.

Sai Jehobah ya zaɓi Jephthah ya ja-goranci Isra’ilawa don su yaƙi Ammoniyawa. Ya ce wa Jehobah: ‘Idan ka taimake mu muka ci yaƙin nan, na yi maka alkawari cewa idan na koma gida, zan ba ka duk mutumin da ya fara fitowa daga gidana don ya yi  mini maraba.’ Jehobah ya amsa addu’ar Jephthah kuma ya ci yaƙin.

Sa’ad da Jephthah ya dawo gida, sai ’ya guda ɗaya kawai da yake da ita ta fito don ta yi masa maraba. Ta fito tana kiɗi kuma tana rawa. To me Jephthah zai yi? Ya tuna da alkawarinsa kuma ya ce: ‘Kash ’yata! Kin sa ni baƙin ciki. Na yi wa Jehobah alkawari kuma don in cika alkawarin, za ki je ki yi hidima a mazauninsa a Shiloh.’ Sai ta ce masa: ‘Baba, tun da ka riga ka yi wa Jehobah alkawari, dole ka cika alkawarin. Abin da nake so shi ne ka ba ni wata biyu in ɗan kasance tare da ƙawayena a kan dutse. Bayan haka, zan tafi.’ ’Yar Jephthah ta yi hidima a mazauni har ƙarshen rayuwarta. Abokanta sukan kai mata ziyara kowace shekara a Shiloh.

“Duk wanda ya fi son mamarsa ko babansa fiye da ni, bai isa ya zama nawa ba.”​—Matta 10:​37, Juyi Mai Fitar da Ma’ana