A lokacin da Isra’ilawa suke yawo a jeji, sai Korah da Dathan da Abiram da kuma wasu mutane 250 suka yi wa Musa taurin kai. Suka ce masa: ‘Ya ishe ka! Me ya sa za ka zama shugabanmu sa’an nan Haruna ya zama babban firist? Jehobah yana tare da dukanmu, ba kai da Haruna kaɗai ba.’ Jehobah bai ji daɗin wannan maganar ba sam domin hakan raini ne a gare shi!

Sai Musa ya gaya wa Korah da mutanen da suka goyi bayansa cewa: ‘Ku zo mazauni gobe kuma ku kawo kaskon turare cike da turare. Jehobah zai nuna mana wanda ya zaɓa.’

Washegari, sai Korah da mutane 250 da suke goyon bayansa suka je suka sami Musa a mazaunin. Suka ƙona turare kamar yadda firistoci suke yi. Sai Jehobah ya gaya wa Musa da Haruna cewa: ‘Ku janye kanku daga Korah da masu goyon bayansa.’

Ko da yake Korah ya je wurin Musa a mazaunin amma Dathan da Abiram da kuma iyalansu sun ƙi zuwa. Sai Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa su matsa daga tantin Korah da Dathan da kuma Abiram. Da sauri sai Isra’ilawa suka matsa daga wurin. Amma  Dathan da Abiram da kuma iyalansu sun tsaya a wajen tantinsu. Sai ƙasa ta buɗe ta haɗiye su duka! Wuta kuma ta fito daga sama ta ƙone Korah da maza 250 da suka goyi bayansa.

Bayan haka, Jehobah ya gaya wa Musa cewa: ‘Ka karɓi sandar kowane shugaban ƙabilun kuma ka rubuta sunayensu a kan sandunan. Amma a kan sandar ƙabilar Lawi, ka rubuta sunan Haruna a kai. Ka ajiye sandunan a mazauni kuma sandar mutumin da ta fitar da fulawa shi ne wanda na zaɓa.’

Washegari, sai Musa ya kawo sandunan kuma ya nuna wa shugabannin. Sandar Haruna ta fito da fulawa da ’ya’yan itacen almond nunannu. Ta haka ne Jehobah ya nuna musu cewa Haruna ne ya zaɓa ya zama babban firist.

“Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku bi umurnansu.”​—Ibraniyawa 13:​17, Littafi Mai Tsarki