Wata biyu bayan Isra’ilawa sun haye Jar Teku, sai suka zo Dutsen Sinai. A wurin ne Jehobah ya yi alkawari cewa ya ɗauki mutanen Isra’ila a matsayin al’ummarsa na musamman. Ya kāre su kuma ya biya dukan bukatansu. Ya ba su abincin da ake kira manna, tufafinsu ba su yage ba kuma ya ba su masauki mai kyau. Idan kana da yara, ka taimaka musu su fahimci dalilin da ya sa Allah ya ba Isra’ilawa Doka da mazauni da kuma firist. Ka nanata muhimmancin cika alkawarinmu da kasancewa da tawali’u da kuma aminci ga Jehobah.