Yusufu yana da ’yan’uwa da yawa da suka girme shi. Kuma ’yan’uwan Yusufu sun san cewa babansu ya fi ƙaunarsa. Yaya kake gani suka ji sa’ad da suka san hakan? Sun ƙi jinin Yusufu. Sa’ad da Yusufu ya yi wasu mafarkai, sai ya gaya wa ʼyan’uwansa. Sun yi tunani cewa mafarkan na nufin cewa wata rana, za su zama bayin Yusufu. Hakan ya sa ba sa son shi ko kaɗan!

Wata rana ʼyan’uwan Yusufu sun je kiwon tumaki kusa da birnin Shechem. Sai Yakubu ya aiki Yusufu ya je ya duba ko yaya suke. Da suka ga Yusufu yana zuwa daga nesa, sai suka ce: ‘Ga mai-mafarkin nan zuwa. Mu je mu kashe shi.’ Sai suka kama shi suka jefa shi cikin wata rijiya da babu ruwa a cikinta. Amma wani yayansa mai suna Yahuda ya ce: ‘Kada mu kashe shi! Mu sayar da shi ya zama bawa.’ Sai suka sayar da Yusufu wa Midiyanawan da za su ƙasar Masar. Midiyanawan sun biya su kuɗi, wato azurfa guda ashirin.

Sai ʼyan’uwan Yusufu suka saka rigarsa cikin jinin akuya kuma suka aika wa babansu, suka ce: ‘Wannan ba rigar Yusufu ba ne?’ Yakubu ya zata cewa wani naman daji ya kashe Yusufu. Ya yi baƙin ciki sosai kuma ya daɗe yana kuka.

Yusufu ya zama bawan wani babban mutum mai suna Fotifar a ƙasar Masar. Amma Jehobah yana tare da Yusufu. Fotifar ya ga cewa Yusufu ya iya aiki kuma zai iya riƙe amana. Fotifar ya gaya wa Yusufu cewa ya riƙa kula da dukan dukiyarsa.

 Matar Fotifar ta ga cewa Yusufu saurayi ne mai kyau kuma yana da ƙarfi. Sai ta soma matsa masa ya kwana da ita. Mene ne Yusufu ya yi? Ya ƙi kuma ya ce: ‘A’a! Hakan bai da kyau. Mijinki ya yarda da ni kuma ke matarsa ce. Idan na kwana da ke, zan yi wa Allah zunubi!’

Wata rana, sai matar Fotifar ta yi ƙoƙarin sa Yusufu ya kwana da ita dole. Ta kama rigarsa amma ya gudu. Da mijinta ya dawo, sai ta yi masa ƙarya cewa Yusufu ya so ya kwana da ita. Fotifar ya yi fushi sosai, sai ya sa a saka Yusufu a kurkuku. Amma Jehobah bai manta da Yusufu ba.

“Ku ƙasƙantar da kanku ƙarƙashin hannu mai iko na Allah domin ya ɗaukaka ku a lokacin da ya ga ya dace.”​—1 Bitrus 5:​6, Juyi Mai Fitar da Ma’ana