Da Fir’auna ya ji cewa Isra’ilawa sun fita daga ƙasar Masar, sai ya soma yin da-na-sani. Ya ce wa sojojinsa: ‘Ku shirya dukan kayan yaƙinmu, domin mu kamo su! Da mun sani, da ba mu bar su sun tafi ba.’ Sai shi da sojojinsa suka soma bin su da gudu.

Da rana, Jehobah ya yi amfani da gajimare don ya nuna wa mutanensa hanya. Daddare kuma ya yi amfani da wuta. Ya ja-gorance su zuwa Jar Teku kuma ya ce musu su kafa tantinsu a wurin.

Sai Isra’ilawa suka ga Fir’auna da sojojinsa suna tahowa da gudu. Isra’ilawan sun kasa guduwa domin akwai teku a gabansu kuma sojojin Masarawa suna bayansu. Sai suka soma kuka, suka ce wa Musa: ‘Za mu mutu! Da ka bar mu a ƙasar Masar kawai.’ Amma Musa ya ce: ‘Kada ku ji tsoro. Ku yi shiru ku ga yadda Jehobah zai cece mu.’ Babu shakka, Musa ya dogara ga Jehobah sosai, ko ba haka ba?

Sai Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa a daren cewa su kwashe kayansu su soma tafiya. Bayan haka, ya yi amfani da gajimare wajen kāre su daga ʼyan ƙasar Masar. Wajen da Masarawa suke yana da duhu, amma na Isra’ilawa yana da haske.

 Jehobah ya ce wa Musa ya miƙa hannunsa bisa tekun. Sai Jehobah ya sa aka yi iska mai ƙarfi sosai a daren. Ruwan tekun ya rabu biyu kuma ya buɗe hanya a tsakiyar tekun. Sai miliyoyin Isra’ilawa suka bi hanyar har suka ƙetare tekun.

Sojojin Fir’auna suka bi Isra’ilawan cikin tekun. Sai Jehobah ya sa ʼyan Masar suka ruɗe. Tayoyin karusarsu suka soma fita. Sojojin suka soma ihu: ‘Mu koma! Jehobah yana taimaka musu.’

Jehobah ya sake gaya wa Musa: ‘Ka miƙa hannunka bisa tekun.’ Sai ruwan tekun ya dawo da ƙarfi ya halaka sojojin Masar gabaki ɗaya. Fir’auna da dukan sojojinsa suka mutu. Babu ko ɗayansu da ya tsira.

Amma Isra’ilawan da suka tsallake tekun suka soma rera waƙa ga Allah, suka ce: ‘Mu yi waƙa ga Jehobah, domin ya zama mai ɗaukaka ƙwarai. Ya jefa doki da masu hawansa cikin teku.’ Yayin da mutanen suke waƙar, matan suna rawa kuma suna buga tambura. Dukansu sun yi farin ciki sosai cewa sun sami ceto.

‘Da gaba gaɗi muna cewa, Ubangiji mai-taimakona ne; ba zan ji tsoro ba: ina abin da mutum zai mini?’​—Ibraniyawa 13:6