Sa’ad da Yusufu yake cikin kurkuku, sai Fir’auna sarkin ƙasar Masar ya yi mafarki. Babu mutumin da ya san ma’anar mafarkin. Sai wani bawan Fir’auna ya gaya masa cewa Yusufu yana faɗin ma’anar mafarki. Fir’auna ya ce a kira Yusufu da sauri.

Fir’auna ya tambaye shi: ‘Za ka iya faɗin ma’anar mafarkina?’ Sai Yusufu ya ce: ‘Abinci zai yi yawa a ƙasar Masar shekara bakwai. Amma bayan haka, za a yi yunwa shekara bakwai. Ka zaɓi wani mai hikima ya tattara abinci.’ Sai Fir’auna ya ce: ‘Kai na zaɓa! Za ka zama mataimakina a ƙasar Masar.’ Ta yaya Yusufu ya san ma’anar mafarkin Fir’auna? Jehobah ne ya taimake shi.

Yusufu ya yi shekaru bakwai yana tattara abinci. Bayan haka, sai aka soma yunwa a dukan duniya kamar yadda Yusufu ya faɗa. Sai mutane suka soma zuwa daga wurare dabam-dabam don su sayi abinci a wurin Yusufu. Yakubu, baban Yusufu ya sami labari cewa akwai abinci a ƙasar Masar, sai ya ce yaransa su je su sayo abinci.

Da yaran Yakubu suka je wajen Yusufu, nan da nan ya gane su. Amma ʼyan’uwansa ba gane shi ba. Sai suka rusuna masa, kamar yadda ya gani a mafarkinsa sa’ad da yake yaro. Yusufu yana so ya san ko har yanzu, ʼyan’uwansa mugaye ne. Sai ya ce musu: ‘Ku ʼyan leƙen asiri ne. Kuna so ku san asirin ƙasarmu.’ Suka ce: ‘A’a! Mun zo ne daga ƙasar Kan’ana kuma mu goma sha biyu ne. Amma ɗan’uwanmu guda ɗaya ya mutu, autanmu kuma yana tare da babanmu.’ Yusufu ya ce musu: ‘Sai kun kawo autanku kafin in  yarda da abin da kuka ce.’ Bayan haka, sai suka koma gida.

Sa’ad da Yakubu da iyalinsa suka cinye abincin da suka sayo, sai ya sake cewa su koma ƙasar Masar. Amma a wannan lokacin, sun tafi tare da autansu Banyamin. Don ya gwada ʼyan’uwansa, Yusufu ya ɓoye kofinsa na azurfa a cikin jakar da Banyamin ya zuba hatsi kuma ya ce su suka sace kofin. ʼYan’uwan Banyamin sun yi mamaki sosai sa’ad da bayin Yusufu suka ga kofin a jakar Banyamin. Sai suka soma roƙon Yusufu cewa ya hukunta su maimakon Banyamin.

Hakan ya sa Yusufu ya san cewa ʼyan’uwansa sun canja halinsu. Yusufu ya kasa riƙe abin a zuciyarsa, sai ya fashe da kuka ya ce musu: ‘Ni ne ɗan’uwanku, Yusufu. Babanmu yana nan da rai?’ ʼYan’uwansa sun yi mamaki sosai. Sai ya ce musu: ‘Kada ku yi baƙin ciki saboda abin da kuka yi. Allah ne ya aiko ni nan domin in ceci ran mutane. Yanzu, ku koma gida da sauri ku kawo mini babana.’

Sai suka koma gida suka gaya wa babansu abin da ya faru a ƙasar Masar. Yusufu da babansa sun sake haɗuwa bayan sun yi shekaru da yawa ba su ga juna ba.

“Idan ba ku gafarta wa mutane laifofinsu ba, Ubanku kuma ba za shi gafarta naku laifofin ba.”​—Matta 6:15