Wannan sashen ya yi magana game da Yusufu da Ayuba da Musa da kuma Isra’ilawa. Dukansu sun jimre da jarraba daga Shaiɗan. An yi wa wasu daga cikinsu rashin adalci, an tura wasu kurkuku, wasu an mai da su bayi, wasu kuma sun yi rashin ʼyan’uwansu babu zato. Amma Jehobah ya cece su a hanyoyi da yawa. Idan kana da yara, ka taimaka musu su fahimci yadda waɗannan bayin Allah suka ci gaba da bauta wa Jehobah duk da wahalar da suka sha.

Jehobah ya yi amfani da Annoba Goma don ya nuna cewa ya fi dukan allolin Masar ƙarfi. Ka nuna yadda Jehobah ya kāre bayinsa a dā da kuma yadda yake yin hakan a yau.