A kwana a tashi, sai mutane suka soma yawa a duniya. Amma yawancinsu ba sa yin abu mai kyau. Har da wasu mala’iku ma da ke sama. Sun sauko daga sama zuwa duniya. Ka san dalilin da ya sa suka yi hakan? Domin su sami jiki irin na mutane kuma su auri mata.

Matan da mala’ikun suka aura sun haifi yara. Waɗannan yaran sun yi girma sosai kuma suka zama mugaye. Jehobah bai bari su ci gaba da yin mugunta ba. Ya ce zai halaka su da ambaliyar ruwa.

Amma akwai wani mutum da ba ya mugunta. Yana ƙaunar Jehobah sosai. Sunansa Nuhu. Shi da matarsa suna da yara uku. Sunayensu Shem da Ham da Japheth kuma dukansu sun yi aure. Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa ya gina babban jirgin ruwa da ke kama da akwati da za su zauna a ciki don kada su mutu. Jehobah ya kuma gaya wa Nuhu cewa ya shigar da dabbobi da yawa cikin jirgin don kada su mutu.

Nan da nan sai Nuhu ya soma gina jirgin. Sun yi shekara hamsin kafin su gama aikin. Sun gina jirgin yadda Jehobah ya gaya musu. A lokacin, Nuhu ya gaya wa mutanen cewa Jehobah zai halaka su da ruwa idan ba su daina yin mugunta ba. Amma ba su ji ba.

Sa’ad da lokaci ya kai, sai Nuhu da iyalinsa suka shiga cikin jirgin. Bari mu ji abin da ya faru bayan haka.

“Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama.”​—Matta 24:​37, Littafi Mai Tsarki