Me ya sa Jehobah ya yi amfani da ambaliyar ruwa don ya halaka mugayen mutane a zamanin Nuhu? Domin mutane a lokacin ba sa yin abin da ya dace. Wasu mutane kamar Adamu da Hauwa’u da kuma ɗansu Kayinu sun zaɓi su yi mugunta. Wasu kuma kamar Habila da Nuhu sun zaɓi su yi abu mai kyau. Yawancin mutane sun yi abubuwa marasa kyau, shi ya sa Allah ya kawo ƙarshen su. Wannan sashen zai taimaka mana mu san cewa Jehobah yana ganin zaɓin da muke yi kuma ba zai taɓa barin mugunta ta rinjayi nagarta ba.