Manzannin Yesu sun yi biyayya ga Yesu ta wajen yin wa’azi a dukan faɗin duniya. A shekara ta 47 bayan haihuwar Yesu, ’yan’uwan da ke Antakiya sun tura Bulus da Barnaba yin wa’azi a wurare dabam-dabam. Bulus da Barnaba sun yi wa’azi a dukan yankunan da ke Asiya Ƙarami, wato Darba da Listra da kuma Ikoniya.

Bulus da Barnaba sun yi wa kowa-da-kowa wa’azi. Mutane da yawa sun zama Kiristoci. Sa’ad da Bulus da Barnaba suka so su yi wa gwamnan birnin Ƙubrus mai suna Sarjiyus Bulus wa’azi, wani mai-sihiri ya so ya hana su. Amma manzo Bulus ya gaya wa mai-sihirin: ‘Jehobah yana gāba da kai.’ Nan da nan, sai mai-sihirin ya makance. Da Sarjiyus Bulus ya ga haka, sai ya zama Kirista.

Bulus da Barnaba sun yi wa’azi a gidaje da kasuwa da hanya da kuma haikali. A lokacin da suka warkar da wani gurgu, mutanen da ke wajen sun ɗauka cewa su alloli ne kuma suka so su bauta musu. Amma Bulus da Barnaba sun hana su, suka ce: ‘Allah kaɗai za ku bauta wa! Mu ’yan Adam ne kawai.’ Sai wasu Yahudawa suka zo suka yi ƙarya a kan Bulus. Hakan ya sa mutanen suka jefe shi da duwatsu kuma suka jefar da shi a bayan gari suna zato zai mutu. Amma Bulus bai mutu ba! Nan da nan ’yan’uwa suka zo suka kai shi cikin gari. Bayan haka, sai Bulus ya koma Antakiya.

A shekara ta 49, Bulus ya sake zuwa wurare da yawa don yin wa’azi. Bayan da ya sake ziyarar ’yan’uwan da ke Asiya Ƙarami, sai ya je Turai don ya yi wa’azi. Ya je Atina da Afisus da Filibi da  Tasalonika da kuma wasu wurare. Sila da Luka da kuma wani matashi mai suna Timotawus sun bi Bulus sa’ad da yake waɗannan tafiye-tafiyen. Sun yi aiki tare wajen kafa ikilisiyoyi da yawa kuma sun ƙarfafa ’yan’uwan. Bulus ya zauna a Koranti shekara ɗaya da rabi kuma ya ƙarfafa ’yan’uwan da ke wajen. Ya yi wa’azi, ya koyar da mutane kuma ya rubuta wa ikilisiyoyi wasiƙu. Yana sana’ar yin tanti. Da shigewar lokaci, sai Bulus ya koma Antakiya.

Daga baya, Bulus ya sake yin wata tafiya a shekara ta 52. Wannan ƙaro na uku ke nan kuma ya soma ziyarar a Asiya Ƙarami. Ya je wurare masu nisa kamar Filibi da kuma Koranti. Bulus ya yi shekaru da yawa yana koyarwa da warkarwa da kuma taimaka wa ’yan’uwan da ke Afisus. A kowace rana, yana yin jawabi a filin makaranta. Mutane sun saurare shi sosai kuma suka canja halayensu. Bayan Bulus ya yi wa’azi a ƙasashe da yawa, sai ya koma Urushalima.

“Ku tafi fa, ku almajirtar da dukan al’ummai.”​—Matta 28:19