Wata rana, Yesu da manzanninsa sun wuce ta Kwarin Kidron sa’ad da za su Dutsen Zaitun. Da tsakar dare ne kuma akwai farin wata. Sa’ad da suka isa lambun Jathsaimani, sai Yesu ya ce musu: “Ku zauna a nan ku yi tsaro.” Sai Yesu ya je gaba kaɗan cikin lambun ya durƙusa. Ya damu ƙwarai, kuma ya yi addu’a ga Jehobah cewa: ‘Bari a yi nufinka.’ Jehobah ya turo mala’ika don ya ƙarfafa shi. Sa’ad da Yesu ya koma wurin manzanninsa, sai ya ga cewa suna barci. Ya ce: ‘Ku tashi! Yanzu ba lokacin barci ba ne! Lokaci ya kai da maƙiyana za su kama ni.’

Bayan ɗan lokaci, sai Yahuda ya zo wurin tare da mutanen da suke ɗauke da takobi da kuma sanduna. Ya san wurin da Yesu yake domin sun saba zuwa lambun tare. Yahuda ya gaya wa sojojin cewa zai nuna musu Yesu. Sai ya zo wurin Yesu ya ce masa: ‘Sannu, Malam,’ kuma ya yi masa sumba. Yesu ya tambaye shi: ‘Yahuda, kana cin amanata ta wajen yi mini sumba?’

Yesu ya zo gaban mutanen ya tambaye su: “Wa kuke nema?” Sai suka ce: “Yesu na Nazarat.” Ya ce musu: ‘Ni ne shi.’ Mutanen suka ja da baya suka faɗi a ƙasa. Yesu ya sake ce musu: “Wa kuke nema?” Suka sake cewa: “Yesu na Nazarat.” Yesu ya ce: ‘Na ce muku ni ne shi. Amma ku ƙyale waɗannan mutanen su tafi.’

Sa’ad da Bitrus ya ga abin da ke faruwa, sai ya ciro takobinsa ya yanke kunnen wani bawan babban firist mai suna Malkus. Amma Yesu ya taɓa kunnen mutumin kuma ya warkar da shi. Sai ya ce wa Bitrus: ‘Ka mai da takobinka. Idan ka yi faɗa da takobi, to da takobi za a kashe ka.’ Sai sojojin suka kama Yesu kuma suka ɗaura  hannunsa. Da manzannin suka ga haka, sai suka gudu. ’Yan tawaye suka kai shi wurin babban malami mai suna Hananiya. Sai Hananiya ya yi masa tambayoyi kuma ya tura shi zuwa wurin Babban Firist mai suna Kayafa. Amma me ya faru da manzannin?

“A cikin duniya kuna da wahala; amma ku yi farin ciki, na yi nasara da duniya.”​—Yohanna 16:33