Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 DARASI NA 80

Yesu Ya Zabi Manzanni Goma Sha Biyu

Yesu Ya Zabi Manzanni Goma Sha Biyu

Yesu yana da wata shawara mai muhimmanci da yake so ya yanke bayan ya yi shekara ɗaya da rabi yana wa’azi. Su wane ne zai zaɓa su yi aiki tare da shi? Su wane ne zai horar da su don su ja-goranci ikilisiyar Kirista? Yana bukatar taimakon Jehobah don ya yanke wannan shawarar. Don haka, ya tafi kan dutse, inda babu kowa kuma ya yi dukan dare yana addu’a. Da safe, sai Yesu ya kira wasu mabiyansa kuma ya zaɓi manzanni guda 12. Shin ka tuna sunayensu? Sunayensu Bitrus da Andarawus da Yaƙub da Yohanna da Filibus da Bartalamawus da Toma da Matta da Yaƙub ɗan Halfa da Taddawus da Siman da kuma Yahuda Iskariyoti.

Andarawus, Bitrus, Filibus, Yakubu

Manzanninsa goma sha biyu za su riƙa tafiya da shi. Bayan ya horar da su, sai ya tura su yin wa’azi. Jehobah ya ba su ikon da za su iya fitar da aljannu da kuma warkar da marasa lafiya.

Yohanna, Matta, Bartalamawus, Toma

Yesu ya amince da manzannin sha biyu kuma ya kira su abokansa. Farisawa suna ganin cewa manzannin ba su da ilimi  kuma su talakawa ne. Amma Yesu ya horar da su don aikin da za su yi. Za su kasance tare da Yesu a lokuta mafi muhimmanci a rayuwarsa, wato kafin ya mutu da kuma bayan an tayar da shi daga matattu. Kamar Yesu, yawancin manzannin sha biyu daga Galili suke. Wasu cikinsu ma’aurata ne.

Yakub dan Halfa, Yahuda Iskariyoti, Taddawus, Siman

Manzannin ajizai ne kuma sukan yi kuskure. A wasu lokuta, sukan yi magana da garaje kuma sukan yanke shawarar da ba ta dace ba. Suna fushi a wasu lokuta. Sun ma yi musu a kan wane ne a cikinsu ya fi girma. Amma su mutanen kirki ne da suke ƙaunar Jehobah. Su ne za su kula da ikilisiyar Kirista bayan Yesu ya koma sama.

“Na ce da ku abokai; gama dukan abin da na ji daga wurin Ubana, na sanar muku da su.”​—Yohanna 15:15