Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Darussa daga Littafi Mai Tsarki

 DARASI NA 72

Sa’ad da Yesu Yake Karami

Sa’ad da Yesu Yake Karami

Yusufu da Maryamu suna zama a birnin Nazarat tare da Yesu da sauran ’yan’uwansa. Yusufu kafinta ne kuma yana aiki sosai don ya biya bukatun iyalinsa da kuma koya masu Dokar Jehobah. Suna zuwa majami’a a kai a kai don yin ibada kuma suna zuwa Urushalima kowace shekara don su yi Idin Ƙetarewa.

Sa’ad da Yesu yake ɗan shekara 12, iyalinsa ta yi wata tafiya mai nisa zuwa Urushalima kamar yadda suka saba yi. Birnin yana cike da mutanen da suka zo Idin Ƙetarewa. Sa’ad da Yusufu da Maryamu suke komawa gida, sun ɗauka cewa Yesu yana cikin jama’ar da suke tafiyar tare. Amma sai suka neme shi suka rasa.

Sai suka sake komawa Urushalima, kuma sun yi kwana uku suna neman sa. A ƙarshe, suka je haikalin. Yesu yana zaune tare da malamai kuma yana sauraran su da kuma yi musu  tambayoyi. Hakan ya burge malaman da har suka soma yi wa Yesu tambayoyi. Sun yi mamakin abubuwan da Yesu yake faɗa, kuma sun ga cewa ya san Dokar Jehobah sosai.

Yusufu da Maryamu sun damu sosai. Sai Maryamu ta ce: ‘Ɗana, ina ka je? Mun yi ta neman ka a ko’ina!’ Sai Yesu ya ce: ‘Ba ki san cewa dole ne in kasance a gidan Ubana ba?’

Yesu ya koma Nazarat tare da iyayensa. Yusufu ya koya wa Yesu aikin kafinta. A ganin ka, Yesu wane irin mutum ne sa’ad da yake ƙarami? Yayin da Yesu yake girma, hikimarsa ta ci gaba da ƙaruwa kuma Allah da mutane suna son shi sosai.

“Murna nake yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.”​—Zabura 40:8