Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 DARASI NA 64

An Saka Daniyel a Cikin Ramin Zakuna

An Saka Daniyel a Cikin Ramin Zakuna

An kuma yi wani sarki a Babila mai suna Darius. Sa’ad da ya ga cewa Daniyel ya fi sauran mutanen hikima, sai ya naɗa shi shugaban dukan mutanen da suke da babban matsayi a ƙasar. Waɗannan mutanen suna jin haushin Daniyel kuma suna so su kashe shi. Sun san cewa Daniyel yana yin addu’a ga Jehobah sau uku a rana. Saboda haka, suka gaya wa Darius cewa: ‘Ya sarki, a kafa doka cewa kowa a ƙasar ya yi addu’a a cikin sunanka. A saka duk wani da ya ƙi bin wannan dokar cikin ramin zakuna.’ Darius ya so wannan shawarar kuma ya amince da dokar.

Da Daniyel ya sami labarin sabuwar dokar, sai ya shiga cikin gidansa. Ya buɗe wundon gidansa kuma ya durƙusa a ƙasa ya soma yin addu’a ga Jehobah. Sai waɗannan mutanen da suke kishinsa suka shiga gidansa kuma suka gan shi yana addu’a. Suka ruga da gudu, suka gaya wa Darius cewa: ‘Daniyel yana yi maka rashin biyayya. Yana yin addu’a ga Allahnsa sau uku a rana.’ Darius yana ƙaunar Daniyel sosai kuma ba ya so a kashe shi. Dukan yinin, yana tunanin yadda zai ceci Daniyel. Amma ya kasa domin idan sarki ya saka hannu a doka, ko shi da kansa ba zai  iya canja dokar ba. Saboda haka, ya umurci sojojinsa su jefa Daniyel cikin ramin zakunan.

A wannan daren, Darius ya damu sosai game da Daniyel har ya kasa barci. Da gari ya waye, sai ya ruga a guje ya je ramin kuma ya kira Daniyel ya ce: ‘Allahnka ya cece ka kuwa?’

Sai Darius ya ji muryar Daniyel! Daniyel ya ce wa Darius: ‘Jehobah ya rufe bakin zakunan. Ba su yi mini kome ba.’ Hakan ya sa Darius farin ciki sosai! Sai ya ce a fito da Daniyel daga cikin ramin. Babu ko ciwo a jikinsa. Sai sarkin ya ce: ‘Ku jefa waɗannan mutanen da suka kawo ƙarar Daniyel cikin ramin.’ Da aka saka su a cikin ramin, sai zakunan suka cinye su.

Sai Darius ya gaya wa mutanensa cewa: ‘Kowa ya ji tsoron Allahn Daniyel domin ya cece shi daga bakin zakuna.’

Kana yin addu’a ga Jehobah kowace rana kamar Daniyel kuwa?

“Ubangiji ya san yadda zai ceci masu-ibada daga cikin jarraba.”​—2 Bitrus 2:9