Mutanen Yahuda sun ci gaba da yi wa Jehobah rashin biyayya kuma suna bauta wa allolin ƙarya. Amma Jehobah ya yi shekaru da yawa yana taimaka musu. Ya tura annabawansa su yi musu gargaɗi amma maimakon su saurari annabawan, sai su riƙa yi musu dariya. Wane mataki ne Jehobah ya ɗauka don allolin ƙarya da suke bauta wa?

Nebuchadnezzar, sarkin Babila ya ci ƙasashe da yawa da yaƙi. A lokaci na farko da ya ci Urushalima da yaƙi, ya kama Sarki Jehoiachin da hakimai da sojoji da maƙera kuma ya kawo su Babila. Ya kwashe dukan dukiyoyin da ke haikalin Jehobah. Bayan haka, Nebuchadnezzar ya naɗa Zedekiya sarkin Yahuda.

Da farko, Zedekiya ya yi wa Nebuchadnezzar biyayya. Amma ƙasashen da ke kusa da Urushalima da kuma annabawan ƙarya suka gaya wa Zedekiya cewa ya daina yi wa Nebuchadnezzar biyayya. Irmiya ya gaya masa cewa: ‘Idan ka yi tawaye, hakan zai jawo yunwa da ciwo, kuma mutane za su mutu a Yahuda.’

Bayan Zedekiya ya yi shekara takwas yana sarauta, sai ya daina yi wa sarkin Babila biyayya. Ya nemi taimako daga wurin mutanen Masar don ya yaƙi Nebuchadnezzar. Sai Nebuchadnezzar ya aike sojojinsa don su kai wa Urushalima hari kuma suka kewaye birnin. Irmiya ya gaya wa Zedekiya cewa: ‘Jehobah ya ce idan ba ka yi faɗa da Babila ba, kai da mutanenka za ku tsira. Amma idan ka ƙi, mutanen Babila za su ƙone Urushalima kuma za su saka ka cikin fursuna.’ Sai Zedekiya ya ce: ‘Ba zan bar su su shigo ƙasarmu ba!’

 Bayan shekara ɗaya da rabi, sai mutanen Babila suka rushe ganuwar Urushalima kuma suka ƙone birnin. Sun ƙona haikalin, sun kashe mutane da yawa kuma suka ɗauki dubban mutane zuwa zaman bauta a Babila.

Zedekiya ya gudu daga Urushalima amma mutanen Babila sun bi shi a guje. Sun kama shi a wani gari da ke kusa da Yariko kuma suka kawo shi wurin Nebuchadnezzar, sarkin Babila. Sai sarkin ya sa aka kashe ’ya’yan Zedekiya a gabansa. Bayan haka, sai Nebuchadnezzar ya makantar da Zedekiya kuma ya sa shi a cikin kurkuku. A wurin ne Zedekiya ya mutu. Amma Jehobah ya yi wa mutanen Yahuda alkawari cewa: ‘Za ku koma Urushalima bayan shekara 70.’

Mene ne zai faru da matasan da aka kai zaman bauta a Babila? Za su riƙe amincinsu ga Jehobah kuwa?

“Ubangiji Allah, Mai Iko duka, shari’unka masu gaskiya ne, masu adalci kuma.”​—Ru’ya ta Yohanna 16:7