Menene matsayin Yesu na musamman?

Daga ina ya fito?

Shi wane irin mutum ne?

DA AKWAI mutane da yawa da suka shahara a duniya. Wasu sanannu ne a yankinsu, a birninsu, ko kuma a ƙasarsu. Wasu kuma sanannu ne a dukan duniya. Amma, sanin sunan shahararren mutum ba shi ne saninsa ba da gaske. Ba ya nufin ka san tarihinsa da kuma kamaninsa.

2 Mutane a duniya sun ji wani abu ne game da Yesu Kristi, ko da yake ya rayu a nan duniya kusan shekara 2,000 da ta shige. Duk da haka, mutane da yawa sun ruɗe game da ainihi wanene Yesu. Wasu sun ce shi dai mutumin kirki ne. Wasu sun ce bai shige annabi ba. Har ila wasu sun ce Yesu Allah ne kuma ya kamata a bauta masa. Ya kamata ne?

3 Yana da muhimmanci ka san gaskiya game da Yesu. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.’ (Yohanna 17:3) Hakika, sanin gaskiya game da Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi zai sa mu sami rai madawwami a aljanna a duniya. (Yohanna 14:6) Bugu da ƙari, Yesu ya kafa misali mafi kyau na yadda za mu rayu da kuma yadda za mu bi da mutane. (Yohanna 13:34, 35) A babin farko na wannan littafin, mun tattauna gaskiya game da Allah. Yanzu bari mu tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ainihi ya koyar game da Yesu Kristi.

ALMASIHU DA AKA YI ALKAWARINSA

4 Da daɗewa kafin a haifi Yesu, Littafi Mai Tsarki ya yi annabcin zuwan wanda Allah zai aiko ya zama Almasihu, ko kuma Kristi. Waɗannan sunayen sarauta “Almasihu” (daga Ibrananci) da kuma “Kristi” (daga Helenanci) duka suna nufin “Shafaffe.” Wanda aka yi alkawarinsa zai zama shafaffe, wato, wanda Allah ya naɗa a matsayi na musamman. A babobi masu zuwa na wannan littafin za mu koyi game da matsayi mai muhimmanci na Almasihu wajen cika alkawuran Allah. Kuma za mu koyi game da albarkatai da Yesu zai kawo mana har ma a yanzu. Kafin a haifi Yesu, mutane da yawa suna mamaki, ‘Waye ne zai zama Almasihu?’

5 A ƙarni na farko A.Z., almajiran Yesu Banazare sun tabbata shi ne Almasihu da aka annabta. (Yohanna 1:41) Ɗaya cikin almajiransa, mai suna Saminu Bitrus, ya fito fili ya ce game da Yesu: “Kai Kristi ne.” (Matta 16:16) To, yaya waɗannan almajirai, da mu kanmu, za mu tabbata cewa Yesu shi ne Almasihun da aka yi alkawarinsa da gaske?

6 Annabawan Allah da suka rayu kafin Yesu sun yi annabci dalla-dalla game da Almasihu. Wannan bayani dalla-dalla zai taimaki wasu su gane shi. Za mu iya kwatanta wannan haka: A ce an aike ka tashar mota ko ta jirgin ƙasa ko ta jirgin sama ka ɗauko wani mutumin da ba ka taɓa saduwa da shi ba. Idan aka yi maka ɗan kwatancensa hakan ba zai taimaka maka ba? Hakazalika, ta wajen annabawan Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya ba da cikakken kwatancin abin da Almasihun zai yi da abin da zai fuskanta. Cikan waɗannan annabce-annabce zai taimaki masu aminci su gane shi.

7 Ga misalai biyu rak. Na farko, fiye da shekaru 700, annabi Mika ya annabta cewa Ɗan alkawarin za a haife shi a Baitalami, wani ɗan ƙaramin gari a ƙasar Yahuda. (Miƙah 5:2) A ina aka haifi Yesu? Lalle, a wannan garin ne! (Matta 2:1, 3-9) Na biyu, ƙarnuka da yawa, annabci da aka rubuta a Daniel 9:25 ya nuna har shekarar da Almasihu zai bayyana, wato shekara ta 29 A.Z.* Cikan wannan da kuma wasu annabce-annabce ya tabbatar da cewa lalle Yesu shi ne Almasihun da aka yi alkawarinsa.

Ana yi wa Yesu baftisma

Yesu ya zama Almasihu ko kuma Kristi a lokacin baftismarsa

8 Ƙarin tabbaci cewa Yesu shi ne Almasihu ya bayyana a ƙarshen shekara ta 29 A.Z. Wannan shekarar ce Yesu ya je wurin Yohanna mai Baftisma ya yi masa baftisma a Kogin Urdun. Jehobah ya yi wa Yohanna alkawarin alama domin ya gane Almasihun. Yohanna ya ga alamar a lokacin baftismar Yesu. Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ya faru: “Sa’anda aka yi masa [Yesu] baftisma, ya fita nan da nan daga cikin ruwa: ga kuwa sammai suka buɗe masa, ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya yana zuwa bisansa; ga kuwa murya daga cikin sammai, ta ce, Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai.” (Matta 3:16, 17) Bayan ya ji kuma ya ga abin da ya faru, Yohanna ba shi da sauran wata shakka cewa Allah ne ya aiko Yesu. (Yohanna 1:32-34) Sa’ad da aka zubo masa ruhun Allah, ko kuma ƙarfin ikonsa a wannan rana, Yesu ya zama Almasihu, ko kuma Kristi, wanda aka naɗa ya zama Shugaba da kuma Sarki.—Ishaya 55:4.

9 Cikar annabcin Littafi Mai Tsarki da kuma shaidar da Jehobah Allah ya bayar ya nuna a fili cewa Yesu ne Almasihu da aka yi alkawarinsa. Amma kuma Littafi Mai Tsarki ya amsa wasu tambayoyi biyu masu muhimmanci game da Yesu Kristi: Daga ina ya fito? Wane irin mutum ne shi?

DAGA INA NE YESU YA FITO?

10 Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Yesu ya rayu a samaniya kafin ya zo duniya. Mika ya annabta cewa za a haifi Almasihu a Baitalami kuma ya daɗa cewa asalinsa “tun daga zamanin dā.” (Miƙah 5:2) A lokatai da yawa, Yesu kansa ya ce ya rayu a samaniya kafin a haife shi mutum. (Yohanna 3:13; 6:38, 62; 17:4, 5) Sa’ad da yake halittar ruhu a samaniya, Yesu yana da dangantaka ta musamman da Jehobah.

11 Yesu shi ne Ɗan Jehobah da ya fi ƙauna, domin kyawawan dalilai. An kira shi “ɗan fari ne gaban dukan halitta,” domin shi ne halitta ta farko na Allah.# (Kolossiyawa 1:15) Da kuwa wani abin da ya sa ya zama Ɗa na musamman. Shi ne “Ɗansa, haifaffe shi kaɗai.” (Yohanna 3:16) Wannan yana nufin cewa Yesu ne kawai Allah ya halitta da hannunsa. Yesu ne kaɗai Allah ya yi amfani da shi wajen halittar dukan wasu abubuwa. (Kolossiyawa 1:16) Saboda haka, kuma ake kiran Yesu “Kalman.” (Yohanna 1:14) Wannan ya nuna mana cewa ya yi magana game da Allah, babu shakka ya idar da saƙonni da umarnin ga sauran ’ya’yan Uban, ’ya’ya na ruhu da kuma na mutane.

12 Shin Ɗan farin daidai yake da Allah, kamar yadda wasu suka gaskata? Littafi Mai Tsarki bai koyar da haka ba. Kamar yadda muka gani a sakin layi na baya, Ɗan, halittarsa aka yi. Saboda haka, a bayyane yake cewa yana da mafari, sa’an nan kuma Jehobah Allah ba shi da farko ba shi da ƙarshe. (Zabura 90:2) Ɗan makaɗaici bai taɓa ma son ya gwada kansa da Ubansa ba. Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Uban ya fi Ɗan. (Yohanna 14:28; 1 Korinthiyawa 11:3) Jehobah ne kaɗai “Allah Alƙadiru.” (Farawa 17:1) Saboda haka, ba shi da wanda ya yi daidai da shi.%

13 Jehobah da Ɗan farinsa sun yi zaman tare na shekaru biliyoyi, kafin ma a halicci sama mai taurari da duniya. Kuma suna ƙaunar juna gaya! (Yohanna 3:35; 14:31) Wannan Ɗan abin ƙauna kamar Ubansa yake. Abin da ya sa ke nan Littafi Mai Tsarki yake kiran Ɗan “surar Allah marar-ganuwa.” (Kolossiyawa 1:15) Hakika, kamar ma yadda ɗa na mutum zai yi kama da ubansa a hanyoyi masu yawa, wannan Ɗa na samaniya ya nuna halaye na Ubansa da kuma mutuntakarsa.

14 Wannan Ɗan Jehobah makaɗaici da son ransa ya zo duniya domin ya yi rayuwa irin ta mutane. Amma za ka yi mamaki, ‘Ta yaya zai yiwu a haifi halittar ruhu a mutum?’ Domin ya cim ma wannan, Jehobah ya yi mu’ujiza. Ya ƙaurar da ran Ɗan farinsa zuwa mahaifar Bayahudiya budurwa Maryamu. Babu uba ɗan adam da ya shiga tsakani. Saboda haka, Maryamu ta haifi kamiltaccen ɗa kuma ta kira shi Yesu.—Luka 1:30-35.

WANE IRIN MUTUM NE SHI YESU?

15 Abin da Yesu ya ce kuma ya yi sa’ad da yake duniya ya taimake mu mu fahimce shi ƙwarai. Fiye da haka, ta Yesu mun zo ga fahimtar Jehobah da kyau. Me ya sa ya kasance haka? Ka tuna cewa wannan Ɗan cikakken surar Ubansa ne. Abin da ya sa ke nan Yesu ya faɗa wa ɗaya cikin almajiransa: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.” (Yohanna 14:9) Littattafai huɗu na Littafi Mai Tsarki da aka sani da Linjila, wato, Matta, Markus, Luka, da Yohanna, sun yi mana bayani ƙwarai game da rayuwa, ayyuka, da kuma mutuntakar Yesu Kristi.

16 An fi sanin Yesu da “Malami.” (Yohanna 1:38; 13:13) Menene ya koyar? Ainihi, saƙonsa shi ne “bishara ta mulkin” wato, Mulkin Allah, gwamnati ta samaniya da za ta yi sarauta bisa dukan duniya kuma za ta kawo albarka marar iyaka ga mutane masu biyayya. (Matta 4:23) Saƙon waye ne wannan? Yesu da kansa ya ce: “Abin da ni ke koyarwa ba nawa ba ne, amma nasa ne wanda ya aiko ni,” wato Jehobah ke nan. (Yohanna 7:16) Yesu ya sani cewa Ubansa yana so mutane su ji bisharar Mulkin. A Babi na 8, za mu koyi game da Mulkin Allah da kuma abin da zai yi.

Yesu yana koyar da almajiransa

Yesu ya yi wa’azi a dukan inda ya tarar da mutane

17 A ina Yesu ya koyar? A dukan wuraren da ya tarar da mutane, a bayan gari, a cikin birni, a ƙauyuka, a kasuwanni, da kuma gidajen mutane. Yesu bai jira mutane su zo gare shi ba. Shi ya je wurinsu. (Markus 6:56; Luka 19:5, 6) Me ya sa Yesu ya yi haka ya kuma ba da lokaci mai yawa wajen wa’azi da koyarwa? Domin yin haka shi ne nufin Allah a gare shi. Yesu ko da yaushe yana yin nufin Ubansa ne. (Yohanna 8:28, 29) Da kuma wani dalili da ya sa ya yi wa’azi. Ya yi juyayin taron jama’a da ta zo wurin shi. (Matta 9:35, 36) Shugabannin addinai sun yi watsi da su, waɗanda ya kamata su riƙa koyar da su gaskiya game da Allah da kuma nufinsa. Yesu ya fahimci yadda suke bukatar su ji saƙon Mulki.

18 Yesu mutum ne mai ƙauna mai juyayi. Saboda haka mutane suka fahimci cewa suna iya zuwa wurinsa domin mai alheri ne. Har yara ma sukan sake sa’ad da suke tare da shi. (Markus 10:13-16) Yesu ba shi da son kai. Yesu ya ƙi lalaci da rashin adalci. (Matta 21:12, 13) A lokacin da mata ba su da daraja da gata, ya bi da su da daraja. (Yohanna 4:9, 27) Yesu mai ƙasƙantar da kai ne ƙwarai. Ya taɓa ma wanke ƙafafun manzanninsa, abin da bara ne ya saba yi.

1. Yesu yana wa’azi; 2. Yesu yana warkar da mutane

19 Yesu yana kula da bukatun mutane. Wannan ya bayyana musamman sa’ad da ya yi amfani da ikon ruhu mai tsarki na Allah ya warkar da wasu cikin mu’ujiza. (Matta 14:14) Alal misali, wani kuturu ya zo wurin Yesu ya ce: “Idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.” Yesu ya ji wahalar wannan mutumin. Tausayi ya kama shi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin, ya ce: “Na yarda; ka tsarkaka.” Sai kuturun ya warke. (Markus 1:40-42) Kana iya tunanin yadda wannan mutumin ya ji?

MAI AMINCI HAR ƘARSHE

20 Yesu ya ba da misali mafi kyau na yin biyayya cikin aminci ga Allah. Ya kasance da aminci ga Ubansa na samaniya cikin dukan yanayi da hamayya da wahala. Yesu ya yi nasara wajen tsayayya da jarabtar Shaiɗan. (Matta 4:1-11) A wani lokaci ’yan’uwan Yesu kansu ba su ba da gaskiya a gare shi ba, har suka ce “ya ruɗe.” (Markus 3:21) Amma Yesu bai ƙyale sun rinjaye shi ba; ya ci gaba da yin aikin Allah. Yesu ya kasance da kame kai, bai yi ƙoƙarin ya cuci masu hamayya da shi ba, duk da zagi da rashin mutunci da suka nuna masa.—1 Bitrus 2:21-23.

21 Yesu ya kasance da aminci har mutuwarsa, mutuwar wulakanci a hannun abokan gaba. (Filibbiyawa 2:8) Ka yi la’akari da abin da ya jimre a ranarsa ta ƙarshe ta rayuwar ɗan adam. Aka kama shi, masu shaidan zur suka ba da shaida aka tuhume shi, malalatan alƙalai suka yanke masa hukunci, mutane suka yi masa dariya, kuma sojoji suka gana masa azaba. Aka buga shi da ƙusa a jikin gungumen azaba, a fitar ransa ya yi kuka: “Ya ƙare.” (Yohanna 19:30) Duk da haka, kwanaki uku bayan mutuwar Yesu, Ubansa na samaniya ya ta da shi zuwa rayuwa ta ruhu. (1 Bitrus 3:18) Bayan ’yan makonni, ya koma samaniya. A can ya “zauna ga hannun dama na Allah” yana jira ya karɓi mulki.—Ibraniyawa 10:12, 13.

22 Menene Yesu ya cim ma ta wajen kasancewa da aminci har mutuwarsa? Hakika mutuwar Yesu ta buɗe mana hanyar samun rai na har abada a aljanna a duniya, cikin jituwa da nufin Jehobah na tun dā. Za a tattauna yadda mutuwar Yesu ta sa haka ya yiwu a babi na gaba.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

  • Cikan annabce-annabce da kuma shaida ta Allah suka tabbatar da cewa Yesu shi ne Almasihu, ko kuma Kristi.—Matta 16:16.
  • Yesu ya yi rayuwar halitta ta ruhu a sama da daɗewa kafin ya zo duniya.—Yohanna 3:13.
  • Yesu malami ne, mutum ne mai ƙauna da juyayi, kuma misali ne mafi kyau na biyayya ga Allah.—Matta 9:35, 36.

*  Domin bayani game da annabcin Daniel da ya cika a kan Yesu, ka dubi Rataye.

#  Ana kiran Jehobah Uba domin shi ne Mahalicci. (Ishaya 64:8) Tun da Allah ne ya halicci Yesu, ana kiransa Ɗan Allah. Domin wannan dalilin wasu halittu na ruhu da ma Adamu an kira su ’ya’yan Allah.—Ayuba 1:6; Luka 3:38.

%  Domin ƙarin tabbaci game da cewa Ɗan farin ba daidai yake da Allah ba, ka dubi Rataye.


Tambayoyin Nazari

1, 2. (a) Me ya sa sanin sunan mutumin da ya shahara ba ya nuna saninsa ne na gaskiya? (b) Wane ruɗani ne ya kasance game da Yesu?

3. Me ya sa yake da muhimmanci a gare ka ka san gaskiya game da Yesu?

4. Menene sunayen sarauta nan “Almasihu” da kuma “Kristi” suke nufi?

5. Menene almajiran Yesu suka tabbata game da shi?

6. Ka kwatanta yadda Jehobah ya taimaki masu aminci su gane Almasihu.

7. Waɗanne annabce-annabce ne biyu da suka shafi Yesu suka cika?

8, 9. Wane tabbaci ne ya bayyana a lokacin baftismar Yesu da ya nuna cewa shi ne Almasihu?

10. Menene Littafi Mai Tsarki ya koyar game da rayuwar Yesu kafin ya zo duniya?

11. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu shi ne Ɗan Jehobah da ya fi ƙauna?

12. Ta yaya muka sani cewa Ɗan farin ba daidai yake da Allah ba?

13. Menene Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ce Ɗan “surar Allah marar-ganuwa” ne?

14. Ta yaya aka haifi Ɗan makaɗaici na Jehobah ɗan adam?

15. Me ya za mu ce ta warin Yesu muka zo ga fahimtar Jehobah da kyau?

16. Menene ainihin saƙon Yesu, kuma daga ina ne koyarwarsa ta fito?

17. A ina Yesu ya yi koyarwarsa, kuma me ya sa ya yi irin wannan ƙoƙari domin ya koyar da wasu?

18. Waɗanne halaye ne na Yesu suka fi ba ka sha’awa?

19. Waɗanne misalai ne suka nuna cewa Yesu ya damu da bukatun wasu?

20, 21. Ta yaya Yesu ya kafa misalin biyayya ga Allah?

22. Menene Yesu ya cim ma ta wajen kasance da aminci har mutuwarsa?