MILIYOYIN mutane suna ƙauna kuma suna ɗaukaka gicciye. The Encyclopædia Britannica ya kira gicciye “ainihin alama ta addinin Kirista.” Duk da haka, Kiristoci na gaskiya ba sa amfani da gicciye wajen bauta. Me ya sa?

Dalili ɗaya mai muhimmanci shi ne cewa Yesu Kristi bai mutu a kan gicciye ba. Kalmar Hellenanci da galibi ake fassara ta “gicciye” stau·ros′ ce. Tana nufin “miƙaƙƙen gungume ko sanda.” Littafi Mai Tsarkin nan Companion Bible ya ce: “[Stau·ros′] bai taɓa nufin gumagumai biyu ba, da aka ɗora a kan juna ko ta wane hali…Babu ma wani abu a Hellenanci na [Sabon Alkawari] da ya yi kusa da gumagumai biyu.”

A wasu wurare da yawa, marubutan Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da wata kalma wajen kwatanta abin da aka kashe Yesu a kai. Kalmar Hellenanci ce xy′lon. (Ayukan Manzanni 5:30; 10:39; 13:29; Galatiyawa 3:13; 1 Bitrus 2:24) Ma’anar wannan kalmar ita ce “katako” ko kuma “sanda ko kulki, ko kuma itace.”

Da yake ba da bayani a kan abin da ya sa sau da yawa ake amfani da sanda domin kisa, littafin nan Das Kreuz und die Kreuzigung (Gicciye da kuma Gicciya), na Hermann Fulda, ya ce: “Babu itatuwa a wurare da aka zaɓa domin kisa. Saboda haka ake kafa gungume a ƙasa. A kan wannan ake kafa ko kuma ɗaure hannu da ƙafafuwansu masu laifi a sama.”

Tabbaci mafi ƙarfi ta fito ne daga Kalmar Allah. Manzo Bulus ya ce: “Kristi ya fanshe mu daga la’anar shari’a, da ya zama la’ana maimakonmu: gama an rubuta, kowane wanda an rataye shi ga itace la’ananne ne.” (Galatiyawa 3:13) A nan Bulus ya yi ƙaulin Kubawar Shari’a 21:22, 23, wadda ta yi maganar itace, ba giciye ba. Tun da irin wannan kisa yana mai da mutum “la’ananne,” ba daidai ba ne Kiristoci su yi wa gidajensu ado da siffan Kristi a rataye.

Babu tabbaci cewa Shekaru 300 bayan mutuwar Kristi, waɗanda suka yi da’awar cewa su Kiristoci ne sun yi amfani da giciye wajen bauta. Amma a ƙarni na huɗu, arnen Daula Constantine ya karɓi Kiristanci na ’yan ridda kuma ya yaɗa gicciye a matsayin alamarta. Ko da menene dalilinsa, babu abin da ya haɗa gicciye da Yesu Kristi. Gicciye, ainihi daga arna aka samo shi. New Catholic Encyclopedia ya ce: “Gicciye ta wanzu a al’adu na zamanin kafin Kiristanci da kuma zamanin da babu Kiristanci.” Wasu masana suna nuna alaƙa tsakanin giciye da bautar yanayi da kuma al’adun jima’i na arna.

Me ya sa aka ɗaukaka wannan alama na arna? Domin ya kasance da sauƙi arna su karɓi “Kiristanci.” Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya la’anta bauta ga dukan wani alama ta arna. (2 Korinthiyawa 6:14-18) Nassosi kuma sun hana dukan wani ire-iren bautar gumaka. (Fitowa 20:4, 5; 1 Korinthiyawa 10:14) Saboda haka, domin kyawawan dalilai Kiristoci na gaskiya ba sa amfani da gicciye wajen bauta.*


*  Domin ƙarin bayani game da gicciye, ka dubi shafuffuna na 89-93 na littafin nan Reasoning From the Scriptures, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

← Ka duba inda babin yake