MUTANE da suka yarda da koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya suka ce Allah ya ƙunshi mutane uku—Uba, Ɗa, da kuma Ruhu Mai Tsarki. Kowane cikin waɗannan uku an ce daidai suke, dukansu masu iko duka ne, kuma ba su da farko. Saboda haka, in ji koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya, Uban Allah ne, Ɗan ma Allah ne, kuma Ruhu Mai Tsarki ma Allah ne, kuma waɗannan Allah Ɗaya ne.

Da yawa da suka gaskata da Allah-Uku-Cikin-Ɗaya sun yarda cewa ba za su iya yin bayani ba a kan wannan koyarwa. Duk da haka, wataƙila suna jin cewa Littafi Mai Tsarki ne ya koyar da shi. Amma ya kamata a lura cewa kalmomin nan “Allah-Uku-Cikin-Ɗaya” ba su bayyana ba a cikin Littafi Mai Tsarki. Amma da ra’ayin ne cikin Littafi Mai Tsarki? Domin mu sami wannan tabbaci bari mu bincika nassi da waɗanda suka gaskata da shi suke amfani da shi su tabbatar da Allah-Uku-Cikin-Ɗaya.

“KALMAN KUWA ALLAH NE”

Yohanna 1:1 ta ce: “A cikin farko akwai Kalma, Kalman kuwa tare da Allah ne, Kalman kuwa Allah ne.” (Yohanna 1:1) Daga baya a wannan sura, manzo Yohanna ya nuna babu shakka cewa “Kalman” Yesu ne. (Yohanna 1:14) Tun da an kira Kalmar Allah, wasu sun kammala da cewa, ‘Ɗan da Uban dole ne su kasance cikin Allah Ɗaya.’

Ka tuna cewa wannan ɓangaren Littafi Mai Tsarki asali an rubuta shi ne da Hellenanci. Daga baya, masu fassara suka fassara shi zuwa wasu harsuna. Wasu Masu fassara na Littafi Mai Tsarki ba su yi amfani da furcin nan “Kalman kuwa Allah ne” ba. Me ya sa? Bisa ga yadda suka fahimci Hellenanci na Littafi Mai Tsarki, waɗannan masu fassara sun ce wannan furcin “Kalman kuwa Allah ne” ya kamata a fassara shi a wata hanya dabam. Wace hanya? Ga wasu misali: “Kalmar nan Allah ne.” (A New Translation of the Bible) “Kalmar wata allah ce.” (The New Testament in an Improved Version) “Kalmar tana tare da Allah, kuma tana kamaninsa.” (The Translator’s New Testament) In ji waɗannan fassaran, Kalmar ba Allah ba ce kanta.* Maimakon haka, domin matsayinsa a tsakanin halittun Jehobah, aka kira Kalmar wata “allah.” A nan kalmar nan “allah” tana nufin “mai iko.”

KA NEMI ƘARIN BAYANI

Mutane da yawa ba su iya Hellenanci na Littafi Mai Tsarki ba. To, ta yaya za ka tabbata ainihin abin da manzo Yohanna yake nufi? Ka yi tunani a kan wannan misalin: Malamin makaranta ya yi wa ɗalibansa bayani a kan wani darasi. Daga baya, ɗaliban ra’ayinsu ya bambanta game da bayanin. Ta yaya ɗaliban za su warware matsalar? Za su tambayi malamin ya sake ba su bayani. Babu shakka, samun ƙarin bayani zai taimake su su fahimci batun. Hakazalika, domin ka fahimci ma’anar Yohanna 1:1, za ka sake bincika Lingilar Yohanna domin ƙarin bayani game da matsayin Yesu. Samun ƙarin bayani game da wannan batun babu shakka zai taimake ka ka fahimci batun yadda ya kamata.

Alal misali, ka yi la’akari da abin da Yohanna ya rubuta a sura 1, aya 18: “Ba wanda ya taɓa ganin Allah [Makaɗaici] ba daɗai.” Amma, mutane sun ga Yesu, Ɗan, domin Yohanna ya ce: “Kalman [Yesu] ya zama jiki, ya zauna a wurinmu muka duba ɗaukakarsa.” (Yohanna 1:14) To, ta yaya ne Ɗan zai kasance ɓangare na Allah Makaɗaici? Yohanna kuma ya ce Kalmar yana ‘tare da Allah.’ Ta yaya mutum zai kasance yana tare da wani kuma ya kasance cewa shi ne wannan mutumin? (Yohanna 1:34) Duk da haka, kamar yadda aka rubuta a Yohanna 17:3, Yesu ya bambanta kansa da kuma Ubansa da ke sama. Ya kira Ubansa, “Allah makaɗaici mai-gaskiya.” A kusan ƙarshen Lingilarsa, Yohanna ya kammala yana cewa: “An rubuta waɗannan, domin ku bada gaskiya Yesu Kristi ne, Ɗan Allah. (Yohanna 20:31) Ka lura cewa ba a kira Yesu Allah ba, amma Ɗan Allah. Wannan ƙarin bayani daga Lingilar Yohanna ta nuna yadda ya kamata a fahimci Yohanna 1:1. Yesu, Kalmar, wani “Allah” ne domin yana da matsayi mai girma amma ba domin ɗaya yake da Allah Makaɗaici ba.

KA TABBATAR DA BAYANIN

Ka sake tunani game da misalin na malamin makaranta da ɗalibai. A ce har yanzu wasu suna shakka, har bayan sun saurari ƙarin bayani daga wurin malamin. Me ya kamata su yi? Suna iya zuwa wurin wani malami domin ƙarin bayani a kan wannan batun. Idan malamin na biyu ya tabbatar da bayani na malami na farkon, za a warware shakka ta yawancin ɗaliban. Hakazalika, idan ba ka tabbatar da abin da marubucin Littafi Mai Tsarki Yohanna yake faɗa ba game da dangantakar da ke tsakanin Yesu da Allah Makaɗaici, kana iya juyawa ga wani marubucin Littafi Mai Tsarki domin ƙarin bayani. Alal misali ka yi la’akari da abin da Matta ya rubuta. Game da ƙarshen wannan zamani, ya yi ƙaulin Yesu yana cewa: “Amma zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani ba, ko mala’iku na sama, ko Ɗa, sai Uba kaɗai.” (Matta 24:36) Ta yaya waɗannan kalmomi suka nuna cewa Yesu ba Allah Makaɗaici ba ne?

Yesu ya ce Uba yana da sani fiye da Ɗan. Idan Yesu ɓangare ne na Allah Makaɗaici, da ya san abin da Uban ya sani. Saboda haka, Ɗa da Uban ba za su taɓa zama ɗaya ba. Duk da haka wasu za su ce: ‘Yesu yana da yanayi biyu. A nan yana magana ne a mutum.’ Amma idan haka ne ma, ruhu mai tsarki fa? Idan ruhu mai tsarki Allah ne daidai da Uba, me ya sa Yesu bai ce ya san abin da Uba ya sani ba?

Sa’ad da ka ci gaba da nazarinka na Littafi Mai Tsarki, za ka fahimci wurare da yawa na Littafi Mai Tsarki da suka shafi wannan batu. Sun tabbatar da gaskiya game da Uba, da Ɗa, da kuma ruhu mai Tsarki.—Zabura 90:2; Ayukan Manzanni 7:55; Kolossiyawa 1:15.


*  Domin ƙarin bayani game da ka’idodin nahawun Hellenanci da ya shafi Yohanna 1:1, dubi shafuffuka na 26-29 na mujallar nan Ya Kamata Ka Gaskata Da Dunƙulin-Alloli-Uku? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

← Ka duba inda babin yake