Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labarin na 87: Saurayi Yesu a Haikali

Labarin na 87: Saurayi Yesu a Haikali

DUBI wannan yaron yana magana da tsofaffin mutane. Malamai ne na haikalin Allah a Urushalima. Yaron kuma Yesu ne. Ya ɗan girma a nan. Yanzu yana da shekara 12.

Malaman suna mamaki cewa Yesu yana da sanin Allah da kuma abubuwa da suke rubuce cikin Littafi Mai Tsarki. Amma me ya sa Yusufu da Maryamu ba sa nan? Ina suke? Bari mu gani.

Saurayi Yesu yana magana da malamai

Kowace shekara Yusufu yana kawo iyalinsa zuwa Urushalima domin biki na musamman da ake kira bikin ƙetarewa. Doguwar tafiya ce daga Nazare zuwa Urushalima. Babu wanda yake da mota, kuma babu jirgin ƙasa. Ba su da waɗannan abubuwa a zamani dā. Yawancin mutane suna tafiya ne da ƙafafunsu, kuma yana ɗaukansu kwana uku su isa Urushalima.

A yanzu Yusufu yana da babban iyali. Suna da ƙannen Yesu maza da mata da suke kula da su. A wannan shekarar Yusufu da Maryamu sun yi doguwar tafiyar da ’ya’yansu zuwa Nazare. Suna tsammani Yesu yana tare da waɗansu da suke tafiya tare. Amma da suka tsaya, bayan sun yi yini suna tafiya, ba su ga Yesu ba. Suka neme shi tsakanin ’yan’uwa da abokai ba su gan shi ba! Saboda haka suka koma Urushalima su neme shi.

A ƙarshe suka sami Yesu a nan tare da malamai. Yana sauraronsu kuma yana yi musu tambayoyi. Kuma dukan mutanen suka yi mamakin hikimarsa. Amma Maryamu ta ce: ‘Ɗana me ya sa ka yi mana haka? Ni da babanka mun damu ƙwarai muna nemanka.’

‘Me ya sa kuke nema na?’ Yesu ya yi tambaya. ‘Ba ku sani ba ne cewa zan kasance a gidan Ubana?’

Hakika, Yesu yana ƙaunar ya kasance a inda zai koyi game da Allah. Ba haka ya kamata mu ji ba mu ma? A garinsu Nazare Yesu yana zuwa taro domin bauta a kowace mako. Domin yana sauraron abin da ake faɗa, ya koyi abubuwa da yawa daga Littafi Mai Tsarki. Ya kamata mu zama kamar Yesu mu yi koyi da misalinsa

Luka 2:41-52; Matta 13:53-56.Tambayoyi

 • Shekarar Yesu nawa ne a wannan hoton, kuma a ina yake?
 • Menene Yusufu da iyalinsa suka yi kowace shekara?
 • Bayan sun yi yini suna tafiyar komawa gida, me ya sa Yusufu da Maryamu suka koma Urushalima?
 • A ina ne Yusufu da Maryamu suka samu Yesu, kuma me ya sa mutane da suke wajen suka yi mamaki?
 • Menene Yesu ya gaya wa mamarsa, Maryamu?
 • Ta yaya za mu zama kamar Yesu sa’ad da muke koyo game da Allah?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Luka 2:41-52.

  Ko da Dokar tana bukatar maza kaɗai su halarci idodi kowace shekara, wane misali ne mai kyau Yusufu da Maryamu suka nuna wa iyaye a yau? (Luk 2:41; K. Sha 16:16; 31:12; Mis. 22:6)

  Ta yaya Yesu ya kafa misali mai kyau ga matasa a yau wajen yi wa iyayensu biyayya? (Luk 2:51; K. Sha 5:16; Mis. 23:22; Kol. 3:20)

 • Ka karanta Matta 13:53-56.

  Waɗanne ’yan’uwan Yesu huɗu ne aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, ta yaya aka yi amfani da biyu cikinsu a cikin ikilisiyar Kirista daga baya? (Mat. 13:55; A. M. 12:17; 15:6, 13; 21:18; Gal. 1:19; Yaƙ. 1:1; Yahu. 1)