Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 95: Yadda Yesu Yake Koyarwa

Labari na 95: Yadda Yesu Yake Koyarwa

WATA rana Yesu ya gaya wa wani mutum cewa ya ƙaunaci maƙwabcinsa. Sai mutumin ya tambayi Yesu: ‘Waye ne maƙwabcina?’ Yesu ya san abin da mutumin yake tunani. Mutumin yana tunani ne cewa mutane irinsa ne kawai ko kuma waɗanda suke addininsa su ne maƙwabtansa. Bari mu ga abin da Yesu ya gaya masa.

Wani lokaci Yesu yana koyarwa ta wajen ba da labari. Abin da ya yi ke nan yanzu. Ya ba da labarin wani Bayahude da Basamariye. Mun riga mun koyi cewa yawancin Yahudawa ba sa son Samariyawa. Saurari labarin Yesu:

Wata rana wani Bayahude yana bin wata hanya cikin duwatsu zuwa Jericho. ’Yan fashi suka faɗa masa. Suka ƙwace kuɗinsa kuma suka yi masa dūka har ya kusa mutuwa.

Jim kaɗan sai wani Bayahude firist ya bi hanyar. Ya ga mutumin da aka yi masa dūka. Me kake tsammani ya yi? Sai ya koma waccan gefen hanya ya ci gaba da tafiyarsa. Sai wani mai bin addini ya zo. Balawi ne. Ya tsaye ne? A’a, bai tsaya ya taimaki mutumin da aka yi wa dūka ba. Ga firist da Balawi can suna tafiyarsu.

Amma ga wani mutum yana tare da mutumin da aka yi wa dūka. Mutumin Basamariye ne. Kuma yana taimakon Bayahuden. Yana saka masa magani a ciwonsa. Daga baya ya ɗauki Bayahuden zuwa wurin da zai huta ya sami sauƙi.

Basamariye mai halin maƙwabta

Bayan ya gama ba da labarin, Yesu ya tambayi mutumin da ya tambaye shi: ‘Wanene a tsakanin mutanen uku kake tsammanin ya kasance maƙwabci ga mutumin da aka yi wa dūka? Firist ɗin, ko Balawi ko kuma Basamariyen?’

Mutumin ya amsa: ‘Basamariyen ne. Ya yi wa mutumin da aka yi wa duka kirki.’

Yesu ya ce: ‘Gaskiyarka. Je ka ka yi wa mutane kirki.’

Ba ka son yadda Yesu yake koyarwa? Za mu koyi abubuwa da yawa idan muka saurari abin da Yesu ya ce a cikin Littafi Mai Tsarki.

Luka 10:25-37.Tambayoyi

 • Wace tambaya ce wani mutum ya yi wa Yesu, kuma me ya sa?
 • Da me Yesu wani lokaci yake amfani da shi wajen koyarwa, kuma menene muka koya game da Yahudawa da Samariyawa?
 • A labarin da Yesu ya gaya mana, menene ya faru da Bayahude da yake tafiya a kan hanyar zuwa Jericho?
 • Menene ya faru sa’ad da firist Bayahude da Balawi suke wuce wa a hanya?
 • A cikin hoton, wanene yake taimakon Bayahude da aka ji masa rauni?
 • Bayan da Yesu ya gama labarin, wace tambaya ce ya yi, kuma yaya mutumin ya amsa?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Luka10:25-37.

  Maimako ya ba da amsa kai tsaye, ta yaya Yesu ya taimaki masanin Attaurat ya yi tunani game da batun? (Luk 10:26; Mat. 16:13-16)

  Ta yaya Yesu ya yi amfani da kwatanci ya sa masu sauraronsa su sha kan wariya? (Luk 10:36, 37; 18:9-14; Tit. 1:9)