Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 91: Yesu Yana Koyarwa a Kan Dutse

Labari na 91: Yesu Yana Koyarwa a Kan Dutse

GA YESU yana zaune a nan. Yana koyar da duka waɗannan mutanen a kan dutse a Galili. Waɗanda suke zaune kusa da shi almajiransa ne. Ya zaɓi 12 su zama manzanninsa. Manzannin almajiran Yesu ne na musamman. Ka san sunayensu?

Yesu yana koyarwa

Da Siman Bitrus da kuma ɗan’uwansa Andarawus. Sai kuma Yaƙub da Yohanna, waɗanda su ma ’yan’uwan juna ne. Da wani manzo kuma da ake kira Yaƙub, da wani kuma da ake kira Siman. Manzanni biyu sunayensu Yahuda. Ɗaya Yahuda Iskariyoti, ɗayan kuma ana kiransa Taddawus. Sai kuma Filibbus da Natanayilu (wanda ake kuma kiransa Barthalamawus), sai kuma Matta da Toma.

Bayan ya dawo daga Samariya Yesu ya fara wa’azinsa na farko yana cewa: ‘Mulkin sama ya kusa.’ Ka san abin da mulkin yake nufi? Gwamnati ce ta ainihi daga Allah. Yesu shi ne sarkinta. Zai yi sarauta daga sama kuma ya kawo salama ga duniya. Mulkin Allah zai mai da dukan duniya ta zama kyakkyawar aljanna.

Yesu yana koya wa mutanen ne game da mulkin. ‘Ku yi addu’a haka,’ ya yi musu bayani. ‘Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Bari a yi nufin ka a duniya kamar yadda ake yinsa a sama.’ Mutane da yawa suna kiransa ‘Addu’ar Ubangiji.’ Wasu kuma suna kiransa ‘Ubanmu.’ Za ka iya faɗan dukan addu’ar?

Yesu kuma yana koya wa mutanen yadda za su bi da juna. ‘Ku yi wa wasu yadda kuke so su yi muku,’ in ji sa. Ba ka so ne idan waɗansu mutane suka yi maka kirki? Saboda haka Yesu ya ce, mu yi wa wasu kirki. Ba abin farin ciki ba ne cewa a aljanna a duniya kowa zai riƙa yi wa wasu kirki?

Matta sura 5 zuwa 7; 10:1-4.Tambayoyi

 • A wannan hoton, a ina ne Yesu yake koyarwa, kuma su waye suka zauna kusa da shi?
 • Menene sunayen manzanni 12?
 • Menene Mulkin da Yesu yake wa’azi game da shi?
 • Menene Yesu ya koya wa mutanen su yi addu’a a kai?
 • Menene Yesu ya ce game da yadda ya kamata mutane su bi da juna?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Matta 5:1-12.

  A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna cewa mun san bukatarmu ta ruhaniya? (Mat. 5:3; Rom. 10:13-15; 1 Tim. 4:13, 15, 16)

 • Ka karanta Matta 5:21-26.

  Ta yaya Matta 5:23, 24 ta nuna cewa dangantakarmu da ’yan’uwanmu yana shafan dangantakarmu da Jehobah? (Mat. 6:14, 15; Zab. 133:1; Kol. 3:13; 1 Yoh. 4:20)

 • Ka karanta Matta 6:1-8.

  Waɗanne irin adalcin kai ne Kiristoci za su guje wa? (Luk 18:11, 12; 1 Kor. 4:6, 7; 2 Kor. 9:7)

 • Ka karanta Matta 6:25-34.

  Menene Yesu ya koyar game da dogara ga Jehobah don biyan bukata? (Fit. 16:4; Zab. 37:25; Filib. 4:6)

 • Ka karanta Matta 7:1-11.

  Menene kwatanci da ke Matta 7:5 ya koya mana? (Mis. 26:12; Rom. 2:1; 14:10; Yaƙ. 4:11, 12)