Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 90: Da Mace a Bakin Rijiya

Labari na 90: Da Mace a Bakin Rijiya

YESU ya tsaya ya huta a bakin rijiya a Samariya. Almajiransa sun shiga cikin gari su sayi abinci. Matar da Yesu yake magana da ita ta zo ta ɗebi ruwa. Ya ce mata: ‘Ki ba ni ruwa in sha.’

Yesu yana magana da mace Basamariya

Hakan ya ba matar mamaki ƙwarai. Ka san abin da ya sa? Domin Yesu Bayahude ne, ita kuma Basamariye ce. Kuma yawancin Yahudawa ba sa son Samariyawa. Ba sa ma yi musu magana! Amma Yesu yana ƙaunar dukan mutane. Saboda haka ya ce: ‘Da kin san wanda ya ce ki ba shi ruwa, da kin tambaye shi ya ba ki ruwa mai ba da rai.’

Matar ta ce: ‘Malam ba ka ma da abin ɗiba ruwa kuma ga shi rijiya tana da zurfi. A ina za ka sami ruwa mai ba da rai?’

‘In kin sha ruwan wannan rijiya za ki sake jin kishin ruwa,’ Yesu ya yi mata bayani. ‘Amma ruwan da zan ba ki yana iya sa mutum ya rayu har abada.’

Matar ta ce: ‘Malam don Allah ka ba ni wannan ruwa! Ba zan sake jin kishi ba. Kuma ba zan sake zuwa nan ba domin in ɗebi ruwa.’

Matar tana tsammani Yesu yana magana ne game da ruwa na ainihi. Amma yana magana ne game da gaskiya ta Allah da kuma mulkinsa. Wannan gaskiyar tana kama da ruwa mai ba da rai. Tana iya ba mutum rai madawwami .

Yesu ya gaya wa matar: ‘Ki tafi ki kira mijinki ku dawo tare.’

‘Ba ni da miji,’ ta amsa.

‘Kin faɗi gaskiya,’ Yesu ya ce mata. ‘Amma kin yi maza har biyar, kuma mutumin da kike tare da shi yanzu ba mijinki ba ne.’

Matar ta yi mamaki, domin duka abin da ya ce mata gaskiya ne. Ta yaya Yesu ya san waɗannan abubuwa? Hakika, domin Yesu ne Wanda aka yi Alkawarinsa wanda Allah ya aiko, kuma Allah ya sanar da shi wannan bayani. A wannan lokaci almajiran Yesu suka iso, kuma suka yi mamaki yana magana da Basamariya.

Menene muka koya daga duka waɗannan abubuwa? Ya nuna cewa Yesu yana yi wa duka ƙabilu kirki. Kuma ya kamata mu ma mu yi haka. Kada mu yi tunanin cewa wasu mutane mugaye ne domin kawai sun fito daga wata ƙabila. Yesu yana son duka mutane su san gaskiya da zai kai su ga rai madawwami. Mu ma ya kamata mu yi ƙoƙari mu taimaki mutane su koyi gaskiya.

Yohanna 4:5-43; 17:3.Tambayoyi

 • Me ya sa Yesu ya tsaya a rijiya da ke Samariya, menene yake gaya wa matar da ke wurin?
 • Me ya sa matar take mamaki, menene Yesu ya gaya mata, kuma me ya sa?
 • Wane irin ruwa ne matar take tunani Yesu yake magana, amma wane ruwa ne ainihi yake nufi?
 • Me ya sa matar take mamaki don abin da Yesu ya sani game da ita, kuma ta yaya ya samu wannan bayani?
 • Waɗanne darussa za mu iya koya daga labarin matar da ke rijiya?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Yohanna 4:5-43.

  Ta wurin bin misalin Yesu, wane hali ne ya kamata mu nuna wa mutane daga wata ƙasa ko yanayin zama? (Yoh. 4:9; 1 Kor. 9:22; 1 Tim. 2:3, 4; Tit. 2:11)

  Wane amfani na ruhaniya ne mutumin da ya zama almajirin Yesu yake samu? (Yoh. 4:14; Isha. 58:11; 2 Kor. 4:16)

  Ta yaya za mu nuna godiya kamar na mata Basamariya, wadda ta yi dokin gaya wa mutane abin da ta koya? (Yoh. 4:7, 28; Mat. 6:33; Luk 10:40-42)