Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 89: Yesu ya Tsabtace Haikali

Labari na 89: Yesu ya Tsabtace Haikali

YESU ya yi fushi a nan, ko ba haka ba ne? Ka san abin da ya sa ya yi fushi haka sosai? Domin waɗannan mutane na haikalin Allah a Urushalima masu haɗama ne. Suna ƙoƙarin samun kuɗi mai yawa daga mutane da suka zo su bauta wa Allah a nan.

Yesu yana tutture teburan kuɗi

Ka ga dukan waɗannan ’yan maraƙai da tumaki da kurciyoyi? Mutanen suna sayar da waɗannan abubuwa har a cikin haikali. Ka san abin da ya sa? Domin Isra’ilawa suna bukatar dabbobi da kuma tsuntsaye domin su yi wa Allah hadaya.

Dokar Allah ta ce sa’ad da Ba’isra’ile ya yi laifi, ya ba da kyauta ga Allah. Da kuma wasu lokatai da Isra’ilawa suke ba da kyauta. A ina Ba’isra’ile zai sami tsuntsu ko kuma dabba da zai yi wa Allah hadaya?

Wasu Isra’ilawa suna da tsuntsaye da dabbobi. Saboda haka suna iya ba da wannan. Amma Isra’ilawa da yawa ba su da dabbobi ko kuma tsuntsaye. Kuma wasu inda suke yana da nisa sosai da Urushalima saboda haka ba za su iya kawo dabbobi zuwa haikali ba. Saboda haka mutanen suna zuwa nan su sayi dabbobi ko kuma tsuntsaye da suke bukata. Amma waɗannan mutanen suna karɓan kuɗi mai yawa daga wurin mutane. Suna cutar mutanen. Ban da haka ma bai kamata suna sayarwa a cikin haikalin Allah ba.

Abin da ya sa Yesu ya yi fushi ke nan. Saboda haka ya tutture teburansu na canjin kuɗi ya watsar da kuɗinsu. Ya kuma ɗauki igiya ya yi bulala da shi ya kori dukan dabbobin daga cikin haikali. Ya umurci mutanen da suke sayar da kurciyoyin: ‘Ku kwashe su daga wannan! Ku daina mai da gidan Ubana wajen neman kuɗi.’

Wasu cikin almajiran Yesu suna tare da shi a cikin haikali a Urushalima. Suka yi mamakin abin da Yesu yake yi. Sai suka tuna wani wuri a cikin Littafi Mai Tsarki da ya ce game da Ɗan Allah: ‘Ƙaunar gidan Allah za ta rura a cikinsa kamar wuta.’

Sa’ad da Yesu yake nan a Urushalima yana halartar bikin Ƙetarewa, ya yi mu’ujizai masu yawa. Daga baya Yesu ya bar Yahudiya ya fara tafiyarsa zuwa Galili. Amma da yake tafiya ya bi ta cikin gundumar Samariya. Bari mu ga abin da ya faru a can.

Yohanna 2:13-25; 4:3, 4.Tambayoyi

  • Me ya sa ake sayar da dabbobi a cikin haikali?
  • Menene ya sa Yesu fushi?
  • Yadda ka gani a wannan hoton, menene Yesu ya yi, wane umurni ne ya ba mutanen da suke sayar da kurciyoyi?
  • Sa’ad da mabiyan Yesu suka ga abin da yake yi, menene suka tuna?
  • Wane yanki ne Yesu ya yi tafiya a ciki da yake koma Galili?

Ƙarin tambaya

  • Ka karanta Yohanna 2:13-25.

    Yin la’akari da yadda Yesu ya yi fushi da masu canja kuɗi a haikali, wane ra’ayi ne da ya dace ya kamata mu kasance da shi game da ayyukan kasuwanci a Majami’ar Mulki? (Yoh. 2:15, 16; 1 Kor. 10:24, 31-33)