KA SAN ko waye ne wannan jaririn? Hakika, Yesu ne. Ba da daɗewa ba aka haife shi a barga. Barga wuri ne da ake ajiye dabbobi. Maryamu ta kwantar da Yesu cikin sakarkari, wato wurin da ake zuba abincin jakai da kuma wasu dabbobi. Amma me ya sa Maryamu da Yesu suke nan tare da dabbobi? Wannan wuri ne da ya kamata a haihu?

A’a, wannan ba wuri ba ne da ya kamata a haihu. Amma ga dalilin da ya sa suke wannan wurin: Sarkin Roma, Kaisar Agustus, ya kafa doka cewa kowa ya koma garin da aka haife shi domin a rubuta sunansa cikin takarda. A Baitalami ne aka haifi Yusufu. Amma sa’ad da shi da Maryamu suka isa babu sauran ɗaki da ya rage dominsu. Saboda haka dole ne su zauna tare a ɗakin dabbobi. Kuma a wannan ranar ne Maryamu ta haifi Yesu! Amma kamar yadda ka gani lafiyarsa lau.

Yusufu da Maryamu da jariri Yesu

Ka ga makiyaya da suka zo su ga Yesu? Suna daji daddare suna kiwon tumakinsu sai haske ya haskaka su. Mala’ika ne ya bayyana! Makiyaya suka tsorata ƙwarai. Amma mala’ikan ya ce: ‘Kada ku ji tsoro! Na kawo muku albishir ne. Yau, a Baitalami, an haifi Kristi Ubangiji. Zai ceci mutanen! Kuma za ku same shi an naɗe shi yana kwance a cikin sakarkari.’ Farat ɗaya, sai mala’iku da yawa suka bayyana suka fara yabon Allah. Ba tare da ɓata lokaci ba waɗannan makiyaya suka hanzarta suka je neman Yesu, kuma sun same shi.

Ka san abin da ya sa Yesu yake da muhimmanci haka? Ka san ko ainihi shi wanene ne? Ka tuna a labari na farko na wannan littafin mu yi magana game da Ɗan fari na Allah. Wannan ɗan ya yi aiki tare da Jehobah wajen halittar sammai da duniya da kuma dukan wani abu. Wannan ɗan farin shi ne Yesu!

Jehobah ya ɗauki ran Ɗansa daga sama ya saka shi a cikin Maryamu. Ba tare da ɓata lokaci ba yaro ya fara girma a cikinta kamar yadda wasu yara suke girma a cikin mamarsu. Amma wannan yaron Ɗan Allah ne. A ƙarshe aka haifi Yesu a barga a Baitalami. Yanzu ka fahimci abin da ya sa mala’iku suka yi farin ciki ƙwarai har suka gaya wa mutane cewa an haifi Yesu?

Luka 2:1-20.Tambayoyi

 • Wanene jaririn da ke wannan hoto, kuma a ina ne Maryamu take kwantar da shi?
 • Me ya sa aka haifi Yesu a cikin barga na dabbobi?
 • A cikin hoton nan waɗanne mutane ne suke shiga cikin bargar, kuma menene mala’ika ya gaya musu?
 • Me ya sa Yesu ɗa ne na musamman?
 • Me ya sa za a iya kiran Yesu Ɗan Allah?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Luka 2:1-20.

  Menene Kaisar Agustus ya yi wajen cika annabci game da haihuwar Yesu? (Luk 2:1-4; Mi. 5:2)

  Ta yaya mutum zai kasance cikin waɗanda aka kira “mutanen da ya ke murna da su sarai”? (Luk 2:14; Mat. 16:24; Yoh. 17:3; A. M. 3:19; Ibran. 11:6)

  Idan Yahudawa makiyaya suna da dalilin farin ciki domin haihuwar Mai Ceto, wane babban dalili ne bayin Allah a yau suke da shi na farin ciki? (Luka 2:10, 11; Afisawa 3:8, 9; Ru’ya ta Yohanna 11:15; 14:6)