Sa’ad da suke bauta a Babila Isra’ilawa sun fuskanci gwajin bangaskiyarsu sau da yawa. An jefa Shadrach, Meshach da Abednego cikin tanderu mai zafi, amma Allah ya fito da su da ransu. Daga baya mutanen Medes da Persia suka ci Babila a yaƙi, aka Jefa Daniel cikin ramin zakuna, amma Jehobah ya cece shi ta wajen rufe bakin zakunan.

A ƙarshe, sarkin Persia Cyrus ya saki Isra’ilawa. Suka koma ƙasarsu shekaru 70 bayan an kwashe su zuwa bauta a Babila. Abu na farko da suka fara yi bayan sun koma Urushalima shi ne gina Haikalin Jehobah. Amma, abokan gaba suka tsayar da aikin. Bayan shekaru 22 da komawarsu suka gama gina haikalin.

Bayan haka, za mu koyi game da tafiyar Ezra zuwa Urushalima don ya kyawanta haikalin. Wannan wajen shakaru 47 ke nan bayan an gama gina haikalin. Sai kuma bayan 13 da tafiyar Ezra, Nehemiah ya taimaka wajen sake gina ganuwar Urushalima da ta rushe. KASHI NA BIYAR ya ba da tarihin shekaru 152 zuwa zamaninmu.

Ezra da mutanen suna yin addu’a