Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki

Labari na 74: Mutumin da Baya Tsoro

Labari na 74: Mutumin da Baya Tsoro

DUBI waɗannan mutane suna yi wa wannan saurayin ba’a. Ka san ko wanene shi? Wannan Irmiya ne. Annabin Allah ne na musamman.

Mutane suna ba’ar Irmiya

Ba da daɗewa ba bayan Sarki Josiah ya fara halaka gumaka a ƙasar, Jehobah ya gaya wa Irmiya ya zama annabinsa. Amma Irmiya yana ganin cewa shi yaro ne ba zai iya zama annabi ba. Amma Jehobah ya gaya masa cewa zai taimake shi.

Irmiya ya gaya wa Isra’ila su daina yin miyagun abubuwa. Ya ce: ‘Allolin da mutanen al’ummai suka bauta wa allolin ƙarya ne.’ Amma Isra’ilawa da yawa sun gwammace su bauta wa gumaka maimakon Jehobah. Sa’ad da Irmiya ya gaya wa mutane cewa Allah zai yi musu hukunci domin muguntarsu, sai suka yi masa dariya.

Shekaru da yawa suka shige. Josiah ya mutu, kuma bayan watanni uku ɗansa Jehoiakim ya zama sarki. Irmiya ya ci gaba da gaya wa mutanen cewa: ‘Za a halaka Urushalima idan ba su daina miyagun halayensu ba.’ Firist ya kama Irmiya ya yi ihu: ‘Ya kamata a kashe ka domin ka faɗi wannan abin.’ Sai suka faɗa wa shugabanni Isra’ila: ‘Ya kamata a kashe Irmiya domin yana mugun magana game da birninmu.’

Menene Irmiya zai yi yanzu? Bai ji tsoro ba! Ya gaya musu duka: ‘Jehobah ya aiko ni in faɗa muku waɗannan abubuwa. Idan ba ku daina miyagun halayenku ba, Jehobah zai halaka Urushalima. Amma ku tabbata: Idan kuka kashe ni za ku kashe mutum ne da bai yi laifi ba.’

Shugabannin ba su kashe Irmiya ba, amma Isra’ilawan ba su sake miyagun halayensu ba. Daga baya Nebuchadnezzar sarkin Babila ya zo ya yaƙi Urushalima. A ƙarshe, Nebuchadnezzar ya mai da Isra’ilawa suka zama bayinsa. Ya kwashi dubbai zuwa Babila. Ka yi tunanin yadda zai kasance mutanen da ba ka sani ba su ɗauke ka zuwa wata ƙasar da ba ka sani ba!

Irmiya 1:1-8; 10:1-5; 26:1-16; 2 Sarakuna 24:1-17.Tambayoyi

 • Wanene wannan saurayi da ke wannan hoto?
 • Wane tunani ne Irmiya ya yi game da zama annabi, amma menene Jehobah ya gaya masa?
 • Wane saƙo ne Irmiya ya ci gaba da gaya wa mutane?
 • Ta yaya firistoci suka yi ƙoƙarin hana Irmiya, amma ta yaya ya nuna cewa baya tsoro?
 • Wanene wannan saurayi da ke wannan hoto?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Irmiya 1:1-8.

  Kamar yadda misalin Irmiya ya nuna, menene yake sa mutum ya cancanci bauta wa Jehobah? (2 Kor. 3:5, 6)

  Wane ƙarfafa ne misalin Irmiya ya yi wa matasa a ikilisiyar Kirista a yau? (M. Wa. 12:1; 1 Tim. 4:12)

 • Ka karanta Irmiya 10:1-5.

  Wane kwananci ne mai muhimmanci Irmiya ya yi amfani da shi ya nuna wautar dogara ga gumaka? (Irm. 10:5; Isha. 46:7; Hab. 2:19)

 • Ka karanta Irmiya 26:1-16.

  Sa’ad da suke sanar da saƙon gargaɗi a yau, ta yaya raguwar shafaffu suke tuna umurnin Jehobah ta bakin Irmiya ‘kada ka rage kome magana ɗaya’? (Irm. 26:2; K. Sha 4:2; A. M. 20:27)

  Wane misali ne mai kyau Irmiya ya yi tanadi ga Shaidun Jehobah a yau wajen sanar da gargaɗin Jehobah ga al’ummai? (Irm. 26:8, 12, 14, 15; 2 Tim. 4:1-5)

 • Ka karanta 2 Sarakuna 24:1-17.

  Wane mugun sakamako ne Yahuda ta samu domin rashin amincinta ga Jehobah? (2 Sar. 24:2-4, 14)