Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Labari na 71: Allah Ya Yi Alkawarin Aljanna

Labari na 71: Allah Ya Yi Alkawarin Aljanna

WANNAN hoton Aljanna ne da wataƙila Allah ya nuna wa annabinsa Ishaya. Ishaya ya rayu ba da daɗewa ba bayan Yunana.

Mutane a Aljanna

Aljanna tana nufin “lambu” ko “gona.” Ya tuna maka wani abin da muka riga muka gani a wannan littafin? Ya yi kama da lambu mai kyau da Jehobah ya yi domin Adamu da Hauwa’u, ko ba haka ba ne? Amma duniyar duka za ta iya zama aljanna kuwa?

Jehobah ya gaya wa annabi Ishaya ya rubuta game da sabuwar aljanna mai zuwa domin mutanen Allah. Ya ce: ‘Kerkeci da tunkiya za su kasance tare cikin salama. Ƙananan maruƙa za su ci abinci tare da ’ya’yan zakuna, kuma yara za su yi kiwonsu. Jariri ma zai yi wasa kusa da maciji mai dafi kuma ba zai yi masa kome ba.’

Wasu za su ce: ‘Wannan ba zai taɓa faruwa ba.’ ‘Domin duniya ta cika da masifa, kuma za ta ci gaba.’ Amma ka yi tunani game da wannan: Wane irin gida ne Allah ya ba wa Adamu da Hauwa’u?

Allah ya saka Adamu da Hauwa’u cikin aljanna. Domin sun yi wa Allah rashin biyayya ne ya sa suka yi rashin gidansu mai kyau, suka tsufa suka mutu. Allah ya yi alkawarin cewa zai ba mutanen da suke ƙaunarsa dukan abubuwa da Adamu da Hauwa’u suka yi hasararsu.

A aljanna da take zuwa babu abin da zai yi ɓarna ko ya yi halaka. Za a sami cikakkiyar salama. Dukan mutane za su kasance masu koshin lafiya masu farin ciki. Zai kasance kamar yadda Allah yake so ya kasance da farko. A gaba za mu koyi game da yadda Allah zai sa hakan ya kasance.

Ishaya 11:6-9; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.Tambayoyi

 • Wanene Ishaya kuma a wane lokaci ne ya yi rayuwa, menene Jehobah ya nuna masa?
 • Menene kalmar nan “aljanna” take nufi, kuma menene ta tuna maka?
 • Menene Jehobah ya gaya wa Ishaya ya rubuta game da sabuwar aljanna?
 • Me ya sa Adamu da Hauwa suka yi asarar gidansu mai kyau?
 • Menene Jehobah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Ishaya 11:6-9.

  Ta yaya Kalmar Allah ya kwatanta salama da za ta kasance tsakanin dabbobi da mutane a sabuwar duniya? (Zab. 148:10, 13; Isha. 65:25; Ezek. 34:25)

  Waɗanne kalmomin Ishaya ne suke cika a ruhaniya tsakanin mutanen Jehobah a yau? (Rom. 12:2; Afis. 4:23, 24)

  Wa ya cancanci a yaba masa domin canji a halayen mutane a yanzu da kuma a sabuwar duniya? (Isha. 48:17, 18; Gal. 5:22, 23; Filib. 4:7)

 • Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

  Ta yaya Nassosi suka nuna cewa Allah yana zauna tare da mutane yana nufin a alamance ne ba a zahiri ba a duniya? (Lev. 26:11, 12; 2 Laba. 6:18; Isha. 66:1; R. Yoh. 21:2, 3, 22-24)

  Wane irin ciwo ne da kuma hawaye za a share? (Luk 8:49-52; Rom. 8:21, 22; R. Yoh. 21:4)