Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Labari na 70: Yunana da Babban Kifi

Labari na 70: Yunana da Babban Kifi

KA DUBI mutumin da ke cikin ruwa. Yana cikin babbar matsala, ko ba haka ba ne? Wannan kifin yana so ya haɗiye shi! Ka san ko wanene wannan mutumin? Sunansa Yunana. Bari mu ga yadda ya shiga cikin irin wannan babbar matsala.

Yunana annabi Jehobah ne. Ba da daɗewa ba bayan mutuwar Elisha Jehobah ya gaya wa Yunana: ‘Ka tafi babban birnin Nineveh. Muguntar mutane garin ya yi yawa, ina so ka je ka yi musu magana game da abin da suke yi.’

Yunana da babban kifi

Amma Yunana ba ya so ya je. Saboda haka ya shiga jirgi da zai kai shi wani wuri dabam ba Nineveh ba. Jehobah bai yi farin ciki ba da Yunana ya gudu. Saboda haka, ya sa guguwa ta taso. Tana da ƙarfi sosai har jirgin yana so ya nitse. Matuƙan jirgin sun tsorata sosai, suna roƙon allolinsu su taimake su.

A ƙarshe sai Yunana ya gaya musu: ‘Ni Jehobah nake bauta wa, Allahn da ya halicci sama da ƙasa. Ina gudu ne daga yin abin da Jehobah ya ce in yi.’ Saboda haka matuƙan jirgin suka yi tambaya: ‘Me za mu yi maka domin guguwar ta lafa?’

‘Ku jefa ni cikin teku, guguwar za ta lafa,’ in ji Yunana. Matuƙan jirgin ba sa so su yi haka ba, amma da guguwar ta yi tsanani sai suka jefa Yunana cikin ruwa. Sai guguwar ta lafa.

Da Yunana yake nitsewa cikin ruwa, babban kifi ya haɗiye shi. Amma bai mutu ba. Ya yi dare da yini uku a cikin kifin. Yunana ya tuba domin bai yi wa Jehobah biyayya ba ya je Nineveh. To ka san abin da ya faru?

Jonah ya roƙi taimakon Jehobah. Sai Jehobah ya sa kifin ya yi aman Yunana a waje. Bayan haka Yunana ya je Nineveh. Wannan ya koya mana cewa yana da muhimmanci mu yi dukan abin da Jehobah ya ce.

Littafin Yunana.Tambayoyi

 • Wanene Yunana kuma menene Jehobah ya gaya masa ya yi?
 • Domin baya son ya je wurin da Jehobah ya gaya masa, menene Yunana ya yi?
 • Menene Yunana ya gaya ma matuƙa jirgin ruwa su yi domin guguwa ta lafa?
 • Kamar yadda kake gani a wannan hoton menene ya faru sa’ad da Yunana ya nitse cikin ruwa?
 • Kwana nawa ne Yunana ya yi a cikin babban kifi kuma menene ya yi a cikin kifin?
 • Ina ne Yunana ya je sa’ad da ya fita daga cikin babban kifin, kuma menene wannan ya koya mana?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta Yunana 1:1-17.

  Kamar yadda ya bayyana, yaya Yunana ya ji game da aikin da aka ba shi na yi ma mutanen Nineba wa’azi? (Yun. 1:2, 3; Mis. 3:7; M. Wa. 8:12)

 • Ka karanta Yunana 2:1, 2, 10.

  Ta yaya ne abin da Yunana ya fuskanta ya ba mu tabbaci cewa Jehobah zai amsa addu’o’inmu? (Zab. 22:24; 34:6; 1 Yoh. 5:14)

 • Ka karanta Yunana 3:1-10.

  Wace ƙarfafa ce muka samu daga yadda Jehobah ya ci gaba da amfani da Yunana duk da yadda ya kasa cika aiki da aka ba shi da farko? (Zab. 103:14; 1 Bit. 5:10)

  Menene labarin Yunana da mutanen Nineba ya koya mana game da hukunta mutane a yankinmu? (Yun. 3:6-9; M. Wa. 11:6; A. M. 13:48)