DAN ka mutu, aka tashe ka yaya mamarka za ta ji? Za ta yi farin ciki matuƙa! Amma mutumin da ya mutu zai sake rayuwa kuwa? Hakan ya taɓa faruwa kuwa?

Ka ga wannan mutumin da wannan matar da kuma ɗan yaron nan. Mutumin annabi Iliya ne. Matar kuma gwauruwa ce ta birnin Zeraphath, yaron kuma ɗanta ne. Wata rana sai yaron ya yi rashin lafiya. Ciwon ya yi tsanani sosai har ya mutu. Sai Iliya ya gaya wa matar: ‘Ki ba ni yaron.’

Iliya tare da wata gwauruwa da kuma ɗanta da aka ta da daga mattatu

Iliya ya ɗauki yaron ya hau gidan bene ya kwantar da shi a kan gado. Sai ya yi addu’a: ‘Ya Jehobah, ka sa yaron ya sake rayuwa.’ Sai yaron ya fara numfashi! Iliya ya ɗauki yaron daga benen ya ce wa matar: ‘Dubi, ɗanki yana da rai!’ Abin da ya sa matar take farin ciki ke nan.

Wani muhimmin annabin Jehobah sunansa Elisha. Elisha mataimakin Iliya ne. Amma da shigewar lokaci Jehobah ya yi amfani da Elisha wajen yin mu’ujizai. Wata rana Elisha ya tafi birnin Shu’nem, a nan wata mata ta yi masa kirki ƙwarai. Daga baya wannan matar ta haifi ɗa.

Wata rana, bayan yaron ya ɗan yi girma, ya tafi ya taimaki babansa aiki a gona. Farat ɗaya sai yaron ya fara kuka yana cewa: “Kai na yana ciwo!’ Bayan an kawo shi gida, sai yaron ya mutu. Mamarsa ta yi baƙin ciki matuƙa! Ba tare da ɓata lokaci ba ta tafi wurin Elisha.

Da Elisha ya isa gidan, sai ya shige ɗakin da gawar yaron take. Ya yi wa Jehobah addu’a, ya kwanta a kan yaron. Ba da daɗewa ba jikin yaron ya yi ɗumi, ya yi atishawa sau bakwai. Mamar ta yi farin ciki ƙwarai sa’ad da ta shiga ɗakin ta sami ɗanta da ransa!

Mutane da yawa sun mutu. Wannan ya sa iyalansu da abokansu baƙin ciki. Ba mu da ikon ta da matattu. Amma Jehobah yana da shi. A gaba za mu koyi yadda zai ta da mutane da yawa da suka mutu daga mattatu.

1 Sarakuna 17:8-24; 2 Sarakuna 4:8-37.


Tambayoyi

 • Su wanene ne mutane uku da suke wannan hoton, kuma menene ya faru da wannan ɗan yaron?
 • Menene Iliya ya yi addu’a game da yaron, kuma menene ya faru?
 • Menene sunan mataimakin Iliya?
 • Me ya sa aka kira Elisha zuwa gidan wata mata a Shunem?
 • Menene Elisha ya yi, kuma menene ya faru da yaron da ya mutu?
 • Wane iko ne Jehobah ya bayar, kamar yadda ya bayyana ta wajen Iliya da Elisha?

Ƙarin tambayoyi

 • Ka karanta 1 Sarakuna 17:8-24.

  Ta yaya aka gwada biyayya Iliya da kuma bangaskiyarsa? (1 Sar. 17:9; 19:1-4, 10)

  Me ya sa bangaskiyar gwauruwa ’yar Zarephath fitacciya ce? (1 Sar. 17:12-16; Luk 4:25, 26)

  Ta yaya abin da gwauruwa ’yar Zarephath ta gani ya tabbatar da gaskiyar kalmomin Yesu da suke rubuce a Matta 10:41, 42? (1 Sarakuna 17:10-12, 17, 23, 24)

 • Ka karanta 2 Sarakuna 4:8-37.

  Menene ’yar Shunem ta koya mana game da karɓan baƙi? (2 Sar. 4:8; Luk 6:38; Rom. 12:13; 1 Yoh. 3:17)

  A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yi wa bayin Allah a yau kirki? (A. M. 20:35; 28:1, 2; Gal. 6:9, 10; Ibran. 6:10)